25/07/2022
'Yar gudun hijira ce Allah ya jarabce ta ta haihu yau kwana 47 kenan, An sace mahaifiyar ta ,ansace kakanta 😭 mahaifinta yarasu 😭 mijinta baidawoba ,gashi abunda zataci babu sannan ga rashin lafiya tinda tahaihu 🙏😭
Anaso akai jaririyar asibiti Katsina ko Kano, Amman abunda za'aje asibitin babu 😭😭
Wallahi abunda zata rinka cin abinci saboda ruwan mama yazo Babu 🙏🙏
Danhaka ta bukaci ayima Yan uwa Al'ummar musulmi magana a taimake ta fisabilillahi 🙏🙏 Domin muje mukaita asibitin dakuma abunda zasuhi darajar Annabi S.A.W .
Yanzu suna zaune cikin Garin kankara Nan jihar KATSINA.
Gawanda Allah yahoremawa mai100,200,500,1000 duk abunda Allah yahore ataimaka 🙏 Akira 070609372166 dominjin Karin bayani .
Masu taimakawa Kuma ta banki ga acct.no:
Acc no: 0528884169
Acc name: Mims Foundation
Bank: GTBank
ALLAH YABADA IKON TAIMAKAWA AMIN .
kada amanata copy ko shared Shima sadaka ce 🤲
MUNGODE .
21/07/2022
Allahou Akbar
Ku saurara kuji bayani daga bakinda baya karya
Manzon Allah sallallahou alaihi wa sallam
Yana cewa duk wanda yayi mini salati 40 aranar juma'a Allah zai gafarta masa dukkan zunubansa kuma duk wanda yayi mini salati 80 aranar juma'a Allah zai gafarta masa zunubansa na shekara 80
Allahou Akbar allahoumma salli wa sallim ala katimul ambiya'i wa imamul mursalina
20/07/2022
Dakai nake Mai Karatu.
Ina Rokon Allah Yayi maka Albarka fiye da kokarinka, Yayi maka Rahama fiye da Tubanka, Ya Jikanka fiye da Tunaninka , Ya kara azurta ka fiye da nemanka , Ya karbi Ibadunka fiye da kwazonka .
Allah Yayi wa mahaifanka rahama batare da binciken ayyukansu ba. Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira.
Allah yasa mu cika da imani da kalmar lailaha illallah Muhammadu rasulillah S A W
18/07/2022
WA ZAI IYA BA ALLAH RANCE?
Yaku al'ummar Musulmi mu sani wallahi Allah zai tambaye mu akan Ni'imar da yai mana.Ba shakka, wani abunda yake samu shi kanshi yasan bashi kadai ke da shi ba, akwai na bayin Allah, masakai, gajiyayyu da sauran mabukata.
Wannan baiwar Allah da kuke gani Sunanta AISHA ( Yar Lele). Tana kwance a cikin daki wanda wallahi ko wane mutun idan ya shiga bazai iya minti biyu aciki ba, wannan baiwar Allah har ila yanzu ba asan me yake damunta ba saboda babu wata asibiti da aka taba kaita don duba lafiyarta!
Kasancewar bata da 'DA ko wani mai halin da zai iya daukar nauyinta domin duba lafiyarta.
Saboda haka muke kira GA daidaikun al'umma da Y'an siyasa da masu kudi kai harma da 'YAN kasuwar mu da su taimaka ma wannan baiwar Allah don ceto lafiyarta. Gidauniyar MIMS FOUNDATION zata hada abinda aka samu wajen bayin Allah da nata gudunmawar domin akaita asibiti a neman mata lafiya kuma a bata jari komai kankantarsa.
Domin bada taimako kana iya turawa ta:
Acc no: 0528884169
Acc name: Mims Multi Synergy Foundation
Bank: GTBank
Ko kana iya kiran wadannan Lambobin 09048912174,
07066282856.
Wallahi, Tallahi wannan baiwar Allah na cikin mawuyacin halinda idan muka taimaka mata to Allah zai yaye mana wata masifa.
Wannan baiwar Allah kofa a bude take GA duk maison ganinta don tabbatarwa domin kuwa ance GANI YA KORI JI.
Tana zaune a Lugun shiyar Ango 'Yar Nasarawa.
Allah ya Bada iKon taimakawa
17/07/2022
Ina masoya manzon Allah
S A W
sallou alaihi wa sallimou t'as lima
17/07/2022
YADDA TABI'AI KE GIRMAMASHI (SAWW)
An tambayi Imamu Maliku game da Shin wanene Ayyubus Sakhtiyani (rahimahullah) sai yace "Ban ta'ba ruwaito hadisi daga wajen wani mutum ba fache sai naga Ayyubus Sakhtiyani ya fishi".
Dalilin da yasa nace haka, shi Ayyubus Sakhtiyani yayi hajji sau biyu ina tare dashi amma ban ta'ba jinsa yayi wata magana ba. (wato mutum ne mai yawan yin shuru). Sai dai naga duk lokacin da aka ambaci sunan Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa sallam) agabansa, yakan rusa kuka sosai har sai naji tausayinsa".
Ni kuma yayin da naga irin girmamawarsa da soyayyarsa ga Manzon Allah (saww) shi yasa na fara karbar hadisi daga gareshi".
Musdahu bn Abdillahi (Allah ya jikansa) yace "Imamu Maliku ya kasance idan an ambaci Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) agabansa, launin fuskarsa yakan chanza, kuma yakan sunkuyar da jikinsa saboda girmamawa gareshi (saww) har abun yayi nauyi sosai ga almajiransa.
Sai watarana wani daga cikin Almajiransa yace masa "Ya kai Baban Abdullahi, irin ladabin nan naka ga Manzon Allah (saww) yana yi mana nauyi".
Sai yace masa "Da ache kunga irin abinda na gani, da baza kuyi min inkari ba".
Hakika ni naga Malamina Muhammad ibnul Munkadir alhali shine shugaban Qurra'u (mahaddatan Alqur'ani) na zamaninsa, bamu ta'ba tambayarsa wani hadisin Annabi (saww) ba fache sai yayi ta kuka kafin ya gaya mana hadisin har sai munji tausayinsa".
Hakika ni naga Imamu Ja'afar 'dan Muhammad Assadiq (Jikan Manzon Allah) ya kasance mutum ne shi mai yawan raha. Amma da zarar an ambaci sunan Manzon Allah (saww) agabansa sai launinsa ya chanza. Kuma bai ta'ba karanta hadisin Manzon Allah (saww) ba fache sai yana da alwala".
Kuma na dade ina karatu awajensa zamani mai tsawo amma ban ta'ba ganinsa ba, fache sai acikin halaye guda uku :
- Kodai ina tarar dashi yana sallah.
- Ko in tarar dashi yana azumi.
- Ko in tarar dashi yana karatun Alqur'ani.
Allah yasa mudace amin
16/07/2022
MANZON ALLAH (S.A.W) KENAN!
Da Sunan Allah Mai Girma, salati da amincinsa su tabbata bisa bawansa mafi girma, Annabinmu Muhammadu tare da Iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa masu girma.
YAKOKIN ANNABI (SAW)
Yakokin da Manzon Allah (saww) yayi azamaninsa, ba wai yana yinsu ne domin daukar fansa ko son zubar da jini ba. A'a yakokin nasa sun kasance ne domin mayar da kaidin abokan gaba da ladabtarwa ga duk wani mai ta'addanci, da kuma kira zuwa ga addinin Allah.
Annabi (saww) yayi yakoki da dama kafin badar da kuma bayanta, domin amintar da garin Madeenah da kuma bayar da kariya gareta daga hare-haren kafirai.
Akwai yakokin da ya samu halarta, sun kai k**ar guda ashirun da bakwai ko da takwas. Akwai kuma wasu da dama wadanda bai je ba amma ya tura da rundunoni karkashin jagorancin amintattu daga cikin Sahabbansa.
YAQIN BADAR :
Manzon Allah (saww) ya samu labarin gabatowar wani ayarin fatauci na Quraishawa mai kunshe da rakuma dubu dauke da kayan fatauci, Kuma Abu Sufyan ne yake jagorantar tafiyar.
Sai Manzon Allah (saww) ya umurci Sahabbansa cewa "KU FITA ZUWA GARESU WATAKIL ALLAH YA KARBA MUKU ITA".
Shi kuwa Abu Sufyan (shugaban ayarin Quraishawa) yayun da labari ya iso gareshi cewa Manzon Allah (saw) ya fito da jama'arsa domin tarar ayarinsu, sai ya aika ya sanar wa mutanen makkah (Quraishawa) cewa su fito domin kare dukiyoyin dake cikin ayarinsu. Sannan kuma ya dauki hayar wani mutum wanda yabi dashi ta wata hanyar wacce ba'a santa sosai ba, har dai ya tseratar da ayarin nasu.
Su kuwa abangaren Quraishawa, yayin da labari ya iskesu sai s**a kira taron gaggawa atsakaninsu. S**a yanke shawarar cewa lallai dole su fita su yaqi Manzon Allah (saww) domin kare ayarinsu. Don haka sai manyan garin s**a fito kwansu da kwarkwatarsu, kowa da shirin yaqi.
Abu Sufyan ya basu shawarar cewa su koma gida tunda an tseratar da ayarin nasu. Amma Abu Jahal (L.A) ya kafe kuma yayi rantse da gumakansa cewa sai yaje filin badar ya zauna tsawon kwanaki uku.
Amma Abu Jahal (L.A) ya kafe kuma yayi rantse da gumakansa cewa sai yaje filin badar ya zauna tsawon kwanaki uku yasha giya, ya saurari kida da wakoki, yadda har sai labarin ya watsu atsakanin sauran Qabilun larabawa domin suji tsoro da kwarjinin Quraishawa.
Shi kuwa Manzon Allah (saww) ya fito tare da Sahabbansa guda dari uku da goma sha uku (313) ko kuma 315 a qata riwayar. Tare da takubba goma sha shida, dawakai uku, da rakuma saba'in.
Su kuwa abangaren Mushrikan Quraishawa, aun fito tare da mutum dari tara da hamsin (950) kowanne da cikakken shirin yaqi da kayan yaqi, tare dasu kuma akwai rakuma dari bakwai (700) da dawakai dari (100).
Yayin da dakarun biyu s**a hadu da juna, an fara gwabza yaqin ne ta hanyar salon fito-na-fito (wato Mubarazah). Mutum uku daga bangaren kafirai s**a fara fitowa s**a bukaci wasu su fito daga bangaren Muminai. Bayan Muminan sun samu nasarar kashesu sai yaqi ya rinchabe.
Allah Madaukakin Sarki ya turo da rundunonin Mala'iku domin taimakon Annabinsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) kuma nasara ta tabbata ga muminai.
Daga bangaren Muminai mutum goma sha hudu ne s**ayi shahada. A bangaren kafirai kuma an kashe mutum saba'in daga cikin manyansu, kuma an k**a wasu saba'in din amatsayin fursunonin yaqi. Kuma daga cikin wadanda aka kashe din har da babban makiyin Allahn nan wato Abu Jahal 'dan Hisham.
Muhimmancin Yaqin badar bashi da iyaka acikin tarihin musulunci. Domin dashi ne musulunci ya fara nuna Qarfinsa, kuma daga kansa ne tutar musulunci ta kafu.
Anan zamu tsaya sai a karatu na gaba kuma zamu dora in shaAllah. Salati da amincin Allah su tabbata bisa Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa da matayensa da dukkan Sahabbansa baki daya.
15/07/2022
THE GREAT POSITION OF MY PROPHET (SAW) IKRIMAH quoted a hadith from Ibn 'Abbas (ra) saying: "Some of the Companions of the Prophet (saww) sat and waited for him, until he came out. Until he came near them he heard Muzakarah among them. He listened to them and heard one of them say: "Amazing !! Allah has taken Bada'di (Khaleel) from among His creatures. Because Prophet Ibraheem is BAD'DIN ALLAH. Then one of them said, "This is not surprising, like the conversation God had with the Prophet Moses (pbuh)." Then one of them said: "So Prophet Eisa (as) is the Word of Allah and the Spirit of Allah". Then another of them said: "Here is Prophet Adam whom Allah has chosen". Then the Messenger of Allah (saww) came out to them and said to them, "ALL I HAVE HEARD OF YOUR SAYING AND THE SURPRISE THAT PROPHET IBRAHIM WAS A BADAN OF ALLAH, EH YES. THIS IS HOW PROPHET MOSES (AS) WAS TALKING TO ALLAH. EH YES". "AND PROPHET EISA (AS) IS HIS SPIRIT AND HIS WORD. EH IT IS ALL THE SAME. AND PROPHET ADAM (AS) WAS SELECTED BY GOD. EH IT IS". "LISTEN !!! I AM HABIBULLAH (LOVER OF ALLAH). AND I DID NOT SAY IT FOR PRIDE". "AND I AM THE BEARER OF LIWA'UL HAMDI (THE FLAG OF THANKSGIVING) ON THE DAY OF JUDGMENT. AND PROPHET ADAM AND EVERYONE UNDER HIM, ALL UNDER IT (THIS FLAG). AND I DID NOT SAY IT FOR PRIDE". "AND I AM THE FIRST ONE TO SEEK CHETO, AND THE FIRST ONE TO BE GIVEN CHETO ON THE DAY OF JUDGMENT. I DIDN'T SAY IT FOR PRIDE." "I'M THE FIRST ONE TO MOVE THE GATE OF PARADISE, I'M NOT PROUD." "GOD WILL OPEN ME, ENTER ME INTO IT WITH THE MOST BELIEVERS. AND I DIDN'T SAY IT FOR PRIDE." "AND I AM THE GREATEST OF ALL THE FIRST PEOPLE AND THE LAST PEOPLE, THE GREATEST POSITION OF GOD. AND I DID NOT SAY IT FOR PRIDE." Refer to TUHFAH, hadith 6,095. And AL-IT'HAF hadith of 8,535. I am sure that this hadith MUST make the hearts of the lovers of the Holy Prophet (sallallahu alaihi wa sallam) happy.
15/07/2022
IKRIMAH ya karbo hadisi daga Ibnu 'Abbas (ra) yana cewa:
"Wasu mutane daga cikin Sahabban Manzon Allah (saww) sun zauna suna jiransa, chan sai ya fito. Har sai da yazo kusa dasu sai yaji suna Muzakarah atsakaninsu.
Sai ya saurari zancensu, yaji wani daga cikinsu yana cewa:
"Abin mamaki!! Allah ya riki bada'di (wato Khaleel) daga cikin halittunsa. Domin Annabi Ibraheem shine BADA'DIN ALLAH.
Sai kuma wani daga cikinsu yace "Ai wannan bai zama abin mamaki ba, k**ar zancen nan da Allah yakeyi da Annabi Musa (as).".
Sai kuma wani daga cikinsu yace: "To ai Annabi Eisa (as) Shi Kalmar Allah ne, kuma Ruhin Allah".
Sai wani kuma daga cikinsu yace: "To ai ga Annabi Aadam nan wanda Allah ya zabeshi".
Daga nan Sai Manzon Allah (saww) ya fito garesu yace musu "DUK NAJI ZANCENKU DA KUMA MAMAKIN DA KUKEYI CEWA ANNABI IBRAHEEM SHINE BADA'DIN ALLAH, EH HAKANE. HAKANAN ANNABI MUSA (AS) YANA ZANCE DA ALLAH. EH HAKANE".
"KUMA ANNABI EISA (AS) RUHINSA NE KUMA KALMARSA NE. EH DUK HAKANE. KUMA ANNABI AADAMU (AS) ALLAH YA ZABESHI. EH HAKANE".
"KU SAURARA!!! HAKIKA NINE HABIBULLAHI (MASOYIN ALLAH). KUMA BAN FADA DON ALFAHARI BA".
"KUMA NINE MAI DAUKAR LIWA'UL HAMDI (TUTAR GODIYA) ARANAR ALKIYAMAH. DA ANNABI AADAMU DA DUK WANDA KE QASANSA, DUK SUNA KARKASHINTA (WANNAN TUTAR). KUMA BAN FADA DON ALFAHARI BA".
"KUMA NINE FARKON WANDA ZAI NEMI CHETO, KUMA FARKON WANDA ZA'A BAMA CHETO ARANAR ALQIYAMAH. BAN FADA DON ALFAHARI BA".
"NINE FARKON WANDA ZAI MOTSA KYAUREN GIDAN ALJANNAH, BA ALFAHARI NAKE YI BA".
"ALLAH ZAI BUDE MIN, YA SHIGAR DANI CIKINTA TARE DA TALAKAWAN MUMINAI. KUMA BAN FADA DON ALFAHARI BA".
"KUMA NINE NAFI DUKKAN MUTANEN FARKO DA MUTANEN QARSHE, GIRMAN MATSAYI AGUN ALLAH. KUMA BAN FADA DON ALFAHARI BA".
Aduba cikin TUHFAH, hadisi na 6,095. Da kuma AL-IT'HAF hadisi na 8,535. Na tabbata cewa wannan hadisin DOLE zai faranta zukatan Masoyan Sayyiduna Rasulullahi (sallallahu alaihi wa aalihi wa sallam).
02/05/2022
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai rahama, Mai jin kai, Ma'abucin ranar sak**ako, Kai ne muke bautawa, kuma Kai muke neman taimako, Ka shiryar da mu zuwa ga tafarki madaidaici, tafarkin
barka da sallah aloumman musulmi duniya
17/10/2021
Happy maulud Mouhammad .S. .A. .W.