15/09/2026
DAGA IRAQ — AN GUDANAR DA BIKIN MAULUD A KARBALA
A daren Juma’a, 11 ga Satumba 2026, ’yan uwa Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), mazauna Funduq Jauharatuz-Zahra (S), s**a gudanar da bikin Mauludin Manzon Allah (S.A.W) a birnin Karbala.
A yayin taron, Malam Ishaq Taraba ya gabatar da jawabi kan rayuwa da koyarwar Manzon Allah (S.A.W), tare da jaddada muhimmancin koyi da tafarkinsa.
Taron ya gudana cikin yanayi na farin ciki da ƙaunar Manzon Allah (S.A.W.W) da Ahlul Baiti (A.S).
MEDIA FORUM-IRAQ TEAM
15/09/2026 | 03 Rabi’ul Aakhir 1448H