14/09/2025
Jama'a barkanmu da warhaka!
Kowa da sana'ar da ta karbeshi. Mu kuma sana'armu kenan, wato kera motocin alatu. Toh amma ba nan ne gizo take saka ba. Wannan harka ne na ilimin zamani mai zurfi. Kusan kashi 80% na injiniyoyi wadanda s**a kera wannan motan da kuke gani, duk matasa ne, daga sassa daban-daban na duniya.
Matasanmu na Najeriya, musamman na Arewa, ina yi muku nasiha, addu'a da fatan alheri. Allah Ya yi muku albarka. Don Allah ku dage ku nemi ilimin zamani da na addini. Tabbas, ba zaku tabe ba. Insha Allahu, zaku ga haske a rayuwarku.
Nan bada jimawa ba zamu sake bude dandalin CUPS Computer and ICT training domin daukan sabbin dalibai. Muna son mu fara horaswa da dalibai 50,000. Ku tabbar da cewa kunyi ragista. A yanzu haka muna da dalibai kimanin 15,000 wadanda s**ayi ragista. Idan Allah Ya yarda, muna da kudurin horarsa da yan Najeriya miliyan daya. Ya Ubangiji Allah Ka daatanmana. Amin Ya Rabbi.
Jama'a na barku lafiya.
Dr. Idris Ahmed.
Shugaban CUPS.
14/9/2025.
13/09/2025
Jama'a barkanmu da warhaka. Zuwa yanzu kwararru 90 sun rattaba hannu. Ku ci gaba da yi mana addu'a. Allah Ka bamu gagarumar nasara
08/09/2025
Free CUPS Computer and ICT Training - Latest Update
UPDATE IN ENGLISH:
Fellow compatriots, I write to update you with our progress as follows:
1. We are now fully engaged with the new 160 Computer and ICT experts that we hope to recruit to teach and mentor you Computer and ICT. We have sent them emails and most of them have responded favourably. By Sunday, 14th September 2025, all the experts interested in working with us would have signed a legally binding MoU contract with the CUPS Organisation. The MoU details the job specification, duration of the training, monthly salary, how payment is made and finally rules of disengagement, should the need arise (We hope and pray this doesn't happen).
2. We are also fully engaged with the CUPS syllabus translators into Hausa language. The latest comprehensive syllabus is 41 pages. It is being translated into Hausa language. We expect to get at least 5 fully completed accurate translations by Sunday, 14th September 2025. The best 3 translations will be shared free in all the CUPS Tutor groups.
3. Following a successful engagement with the new Computer and ICT experts, 18 of them will be immediately recruited to expand the classes to 20. Network stability is a significant deciding factor. Starting with 20 classes means we will have a cohort of 50,000 students (there are 2,500 students in each class). However, if the network proves stable, we may decide to increase the number of classes and recruit more tutors.
4. Just before we commence training, all students will be rearranged into 10 classes where the language of instruction will be purely English, and the other 10 classes will be bi-lingual (English and Hausa). It is entirely up to a student to chose which language class to belong to. We created this arrangement to overcome the language issues/challenges encountered by the 3MTT program, which led it its failure in some Northern states.
Thank God, we have made significant progress over the last 3 weeks. This explains my absence from Facebook. Please, keep praying for the success of this program. Fellow compatriots, I leave you in peace.
Dr. Idris Ahmed.
President CUPS.
07/09/2025.
BAYANI DA HAUSA:
Jama'a Barkanmu da warhaka. Ga sabon karin bayani kamar haka:
1. A yanzu haka, muna cikin cikakken hulɗa tare da sabbin ƙwararrun kwamfuta da na ICT, su 160, waɗanda muke fatan za mu ɗauke su don su koya muku ilimin kwamfuta da ICT. Mun aika musu da imel kuma yawancinsu sun ba da amsa mai kyau. Nan da ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025, duk ƙwararrun masu son aiki da CUPS, za su sanya hannu kan kwangilar yarjejeniya (MoU) tare da Ƙungiyar CUPS. Yarjejeniyar MoU ta ƙunshi cikakkun bayanai game da yanayin aikin, tsawon lokacin karantarwan, albashi a kowane wata, yadda zamu biyasu albashi, da kuma ƙa'idodin rabuwa, idan har an samu akasi (Allah Ubangiji Ya kiyaye. Amin).
2. Hakanan kua muna cikin cikakken hulɗa tare da masu fassara manhajar karatun kwanfuta. Muna sa ran samun aƙalla cikakkun fassarori guda 5 daidai nan da ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025. Zamu raba mafi kyawun fassarorin kyauta a cikin duk azuzuwa 20 na kwamfuta.
3. Bayan nasarar hulɗa tare da sababbin ƙwararrun kwamfuta da ICT, zamu dauki 18 daga cikinsu nan take don faɗaɗa azuzuwan zuwa 20. Zamu ƙara ɗaukar wasu sabbin malamai yayin da muke samun ci gaba. Fara horaswa da azuzuwa 20 yana nufin zamu fara da ɗalibai 50,000 (akwai dalibai 2,500 a kowani aji). Duk da haka, idan hanyar sadarwa ta tabbata (Network), toh muna iya yanke shawarar ƙara azuzuwan da ɗaukar ƙarin malamai.
4. Kafin mu fara horarswa, za a sake tsara duk ɗalibai zuwa azuzuwa 10 inda harshen koyarwa zai zama Turanci kawai, sauran azuzuwa 10 kuma za su kasance masu amfani da harsuna biyu (Turanci da Hausa). Ya rage wa ɗalibi ya zaɓi ko wane irin ajin harshe zai shiga. Mun ƙirƙiri wannan tsari ne don magance matsalolin harshe da shirin 3MTT ya fuskanta, wanda ya haifar da gazawar program din a wasu jihohin Arewa.
Tabbas, munyi gagarumar nasara a sati uku da s**a gabata. Wannan shine dalilin da yasa baku ganni a wannan dandalin ba. Toh Allah Ubangiji Ya datanmana. Amin Ya Rabbi. Jama'a kuci gaba da yi mana addu'an samun nasara akan wannan tafiya. Jama'a na barku lafiya.
Dr. Idris Ahmed.
President CUPS.
08/09/2025.
05/08/2025
Congratulations,
to Nafisa Abdullahi Aminu, Overall best in English Language Skills
and
Ruqayya Muhammad Aminu, Overall best in Debate Showcase, globally. The same competition. The same school. The same state. Thank you for making Nigeria and Yobe state proud of you.
It's our pleasure and proud 👏 from all of us at CUPS Organisation
Congratulations,
to Nafisa Abdullahi Aminu
Khadija, Overall best in English Language
Overall best in Debate Showcase, globally. The same competition. The same school. The same state. Thank you for making Nigeria and Yobe state proud of you.
It's our pleasure and proud 👏 from all of us at CUPS Organisation
19/07/2025
Karin Bayani Akan ICT Training Email ✉️
Jama'a barkanmu da warhaka. Kamar yadda yawancinku kuka sani, mun tara emails 📨 fiyes da 14,000. Toh amma har yanzu wasu sunce basu samu ba. Ga dabara nan da zata taimakeku.
Kamfanin Tecomex Forensics Ltd itace ta sayi email marketing din a madadin CUPS. Itace take da alhakin tura emails din. Saboda haka idan kun lalubi "Promotion" folder 📂 baku ga email ba, toh kuyi search na sunan"Tecomex Forensics Ltd", insha'Allah zaku sami wannan email din.
Toh Jama'a na barku lafiya. Allah Ubangiji Ya bamu gagarumar nasara akan wannan tafiyan ceton Arewa da al'ummanta. Amin Ya Rabbi.
Dr Idris Ahmed.
Shugaban CUPS.
19/7/2025.
12/07/2025
What is CUPS?
CUPS stands for Citizens United for Peace and Stability. CUPS is a UK and Nigeria based human rights NGO. We are fully registered in both countries.
We are currently focussing on human capacity development of our people. We have just embarked on a humongous project of providing free Computer and ICT Training for 1 million Nigerians. We are starting with 16,000 students.
We have a long way to go to accomplish this unprecedented task. There are so many challenges. Notwithstanding, we are confident that we shall overcome!
Pray for our success and stay blessed.
Dr Idris Ahmed.
CUPS President.
12/7/2025.
12/07/2025
Sabon Albishir - CUPS Computer Training!
Jama'a barkanmu da warhaka. Ina murnan sanar daku cewa sabon email marketing da muka saya yana aiki, kuma har mun fara tura muku email wurjanjan.
Alhamdulillah, yanzu haka mun tura email zuwa ga daliban Class 1, su fiye da 1,800. Saboda haka don Allah ku dubi emails naku. Idan baku samu a inbox ba, ku duba a sashen spam.
Duk wadda ya sami email yau, to shi dalibin Class 1 ne. Ku danna orange button, wannan shi ne zai kaiku WhatsApp group na Class 1. A wannan group ne zaku sami technical support.
Jama'a ina yi mana murna da fatan Alheri. Allah Ubangiji Ya bamu gagarumar nasara akan wannan tafiyan ceton Arewa da al'ummanta. Amin Ya Rabbi.
Jama'a na barku lafiya.
Dr Idris Ahmed.
President CUPS.
12/7/2025.
10/07/2025
Sabon Bayanai Akan CUPS Computer Training!
Jama'a barkanmu da warhaka. Ga sabon bayani akan CUPS Computer and ICT Training. Yanzu dai munyi watsi da azzalumar kamfanin GoDaddy, wadda s**a ci amananmu, kuma s**a ci kudinmu £84 (N177,640).
Alhamdulillah, mun sami wata sabuwar kamfanin Email marketing, wadda manhajanta ke da abubuwa daban daban, har ma da SMS marketing. Munyi gwajin tura emails zuwa ga daliban Class 2. Daga cikin dalibai 1,800 na wannan ajin, mun turawa dalibai 600.
Yanzu haka mun biya kamfanin Brevo £67.00 (N142,000), wato kudin tura emails na wata daya kenan. Zamu dinga biyan wannan kudin a kowani wata muddin muna bukatan turawa dalibanmu 16,000 emails da SMS. Jama'a tsarin tura emails da SMS yana da tasiri, domin ba kowa bane yake hawan Facebook, Telegram da WhatsApp a kullum.
Muna jiran kamfanin Brevo su gama tantance email addresses 16,000 na dalibanmu. Suna son su tabbatar da cewa bamu samesu ta hanyar zamba ko yaudara irin spamming ba. Da zaran sun gama tantancewa, insha'Allah zamu tsaida ranan fara training!
Jama'a ku taimakemu da addu'a. Allah Ubangiji Ya bamu gagarumar nasara akan wannan tafiya na ceton Arewa da al'ummanta. Amin.
Jama'a na barku lafiya.
Dr. Idris Ahmed.
President CUPS.
10/7/2025.
04/07/2025
The more you read, the more you will know. The more you learn, the more places you will go.
Crying is a form of cleansing; there is a reason for tears, whether from happiness or sadness. Don't go broke trying to get rich. The worst times can turn out to be the best if you focus on positive energy. There is always a reason to smile. Take care of your body, and it will take care of you. Be brave enough to make the necessary changes in your life. The Lord honors those who seek growth.
Thank you🙏
01/07/2025
Sanarwa Daga CUPS!
Assalamu alaikum Jama'a barkanmu da warhaka. Na shigo wannan dandalin mai tarin Albarka domin tabbatar muku da cewa ni da iyalaina muna nan lafiya kalau sai tarin Alheri.
Hakazalika Jama'a ina jaddada muku cewa bamu dakatar da alkawarinmu na CUPS Computer and ICT Training ba. Wato bayan cin amana wadda kamfanin GoDaddy s**ayi mana, mun sake samun wata sabuwar kalubale amma wajen harkan tsaro. Azzaluman sunyi mana kutse, toh amma Alhamdulillah, bai shafi database na dalibanmu 16,000 ba.
Yanzu dai muna kan rinjayen lamarin. Da zaran mun kammala aikin, zamu sanar da ku ta email da SMS ranan da zamu fara training.
Jama'a don Allah ku kwantar da hankalinku. Muddin ina raye, toh insha'Allah ba zamu fasa wannan yunkurin na ceton Arewa da akummanta ba.
Allah Ubangiji Ka daafa mana. Amin Ya Rabbi.
Jama'a na barku lafiya.
Dr Idris Ahmed.
CUPS.
1/7/2025.