17/10/2024
MA GAGARIN MASU SADAKA DA NAMAN DAMO DA BAKIN BUNSURU DON TSAFI...🐘👑🙏✊
SUN LABE SUNA BATARAI SUNA TURA BAKI...TOH AHIR INKU GARBA SAI MAHDI
Allah Ya Kara Daura Sarki Akan Maqiyansa, Allah Yasa Sarki Ya Gama Da Duniya Lafiya Cikin Nasarori Masu Tarun Yawa, Ya Kara Tsare Gaban Sarki Da Bayansa.🐘🤲🙏👑🔥
17/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
TUNATARWA:
Abubuwa guda hudu suna zuwa kaitsaye ba tare da sanarwa ba:
1. Arziki
2. Rabo
3. Rashin lafiya
4. Mutuwa
Ya Allah ka sanya arzikin mu ya zama na halal. Rabon mu ya zamo mai sauki. Rashin lafiyarmu ta zama kaffarar zunubammu. Mutuwar ta zamo hutu da samun rahamar Allah Bijahi Rasulillahi (S.A.W).
Ina muku fatan alheri da kuma barka da safiya. 🙏🙏🙏
13/10/2024
ZAKI SARKIN BANKEWA JIKAN TUKUR:🦁🔥👑
Allah Ya Kara Lalata Shirin Makiyan Sarki Da Yan Kankanba Tunda Sanyin Safiya, Allah Ya Karawa Sarki Lafiya, Tausayi, Imani Da Nisan Kwana.🙏✊🤲👍👑🔥🦁
13/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM 🤲🤲🤲
Ya Jabbaru Kadauka kamu
Ya Rahimu kaji kan mu
Ya Fatahu kayi mana budi
Ya Razzaku ka azurta mu
Ya Mutakabbiru ka kare mu
Ya Alimu ka kara mana sani
Ya Shafi'u kace cemu
Ya Muminu ka tausaya mana.
Dan Alfarmar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.
Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Safiya.🤲🤲🤲
10/10/2024
TANKWARA MAI BORE JIKAN TUKUR CI FANSA:🏹🔥👑
Allah Ya Kara Nunawa Maqiyan Sarki Abunda Basaso, Allah Duk Wanda Yadamu Sarki Allah Yadameshi, Allah Ya Karawa Sarki Lafiya Da Kwanciyan Hankali, Allah Yasa Sarki Ya Gama Da Duniya Lafiya.🙏👍✊🤲👑🔥🏹
10/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
NASIHA CE:
IDAN ZAKU YI ZANCE KUYI ADALCI !!!
Acikin Alƙur'ani Maigirma ALLAH (ﷻ) Ya ce:
وَإِذَا قُلْتُمْ فَاعْدِلُوا
Maʼana: “idan za ku yi magana, Toh ku yi adalci.” [An-am: 152]
Sheikh Saleh Al-fauzan (Hafizahullah) Ya ce: “Ko da ya kasance abokin adawa ne, ko bayahude, ko banasare. ba'a zalunci akansu.” [Atta'alïq ala Risalah: wujúbul amri bil ma'aruf. Shafi na 103]
Wajibi ne ga Mutum ya rinƙa yin magana ta gaskiya a wajen yabo ko s**a ko bayar da shaida, ba tare da la'akari da kusanci ko soyayya ko ƙiyayya ba.
Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W)
Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Safiya.
08/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM 🙏🙏🙏
HATTARA DA CIN ZALI:
Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ruwaito Hadisi daga Annabi sallallahu alaihi wasallam ya ce: "Kun san wane ne matsiyaci? Matsiyaci daga cikin al'ummata shi ne wanda zaizo ranar alkiyama da Sallah da Azumi da Zakka, amma kuma yazo ya zagi wannan, yayi kazafi ma wannan, yaci kudin wannan, ya zubar da jinin wannan, ya daki wannan...sai a debo daga cikin ladarsa a ba wannan..a ba wannan..har sai ladarsa ta kare bai gama biyan hakkinsu ba, sai a debo zunubansu a jefa masa, sannan a wurga shi cikin wuta". Sahihul Jami' (87).
Allah ya karemu baki daya. Allah yasa mudace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W)
Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Safiya.🙏🙏🙏
06/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
NASIHA CE:
Manzon ALLAH (S.A.W) Ya ce';
Lallai akan haramta wa bawa arziki saboda zunubi da ya aikata.
صححه ابن باز حاشية بلوغ المرام 778
Ibnul Qayyim (RH) Ya ce; Kamar yadda tsoron ALLAH yake janyo arziki, to barin tsoron ALLAH ma haka yake janyo talauci, babu wani abu da yake janyo wa mutum arzikin ALLAH tamkar misalin barin saɓon ALLAH الجواب الكافي ص52m
Allah Yasa Mucika Da Imani Bijahi Rasulillahi (S.A.W).
Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Safiya.
05/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
HATSARIN MUTUWA DA BASHI AKAN KA
Manzon Allah (S.A.W) Yace: “Na Rantse Da Wanda Raina Yake Hannunsa, Da Za'a Kashe Mutum Ta Hanyar Ɗaukaka Addinin Allah (ﷻ), Sai A Rayar Dashi, Sannan A Sake Kashe Shi, Sannan a Ƙara Rayashi, Sannan a Sake Kashe Shi, Sannan a Kuma Kashe Shi Da BÃSHI Akansa, Bazai Taɓa Shiga Aljannah ba Har Sai An Biya Masa Wannan Bashin”.
{Nisã'i Ya Ruwaitoshi}
Allah ya tsare mu. Allah yasa mudace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W)
03/10/2024
RARAKA SARAKAI, FATATTAKA SARAKAI, MAI MALFA MAI BINDIGA:🦁🔥👑
KA DAKESU KA DAKI IYAYEN GIDAN SU...
Allah Ya Kara Lalata Makiyan Sarki Na Fili Dana Boye Na Kusa Dana Nesa Na Gida Dana Waje, Allah Yasa Sarki Ya Gama Da Duniya Lafiya.🙏🤲👍✊🔥👑🦁
03/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
SON MA'AIKI ALLAH ANNABI MUHAMMADU (S.A.W)
Lokacin da MA'AIKI (S.A.W) ya sauka a garin Madina, "Banun Najjar" sun yi murna sosai saboda ANNABI yana maƙwabtaka da su. ANNABI (S.A.W) ya ce musu:
"Kuna ƙaunata"? Sai s**a amsa "na'am".
MA'AIKI (S.A.W) yace, ALLAH ya sa ni tabbas zuciyata tana ƙaunarku".
Duk wanda yake son ANNABI (S.A.W) da gasken gaske, kuma yake biyayya ga umarninsa sa'annan yake yawaita yi masa SALATI tabbas ANNABI (S.A.W) ya san da shi, kuma haƙiƙa MA'AIKI (S.A.W) yana ƙaunarsa.
Babu wani ɗaya da zai yiwa ANNABI (S.A.W) SALATI fa ce an gaya masa wane ɗan gidan wane masoyinka ne kuma yana yi maka SALATI.
ALLAH ya sanya sunayenmu cikin jerin masu ƙaunar MA'AIKI (S.A.W) kuma masu yawaita yi masa SALATI.🤲🤲🤲
02/10/2024
SHAKAKIN MAZA DAN SHEHU KUNUN GABARUWA CIKA CIKI KAS MAKOGWARO:🐘👑🔥
Allah Ya Kara Shiga Tsakanin Nagari Da Mugu, Allah Ya Kara Shiga Cikin Dukkan Lamuran Sarki, Allah Ya Karawa Sarki Kwazo Da Himma Cikin Aikin Mulkinsa..🙏👍✊🤲🔥👑🐘
02/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
KARANTA DOMIN GYARA YAU DA GOBEN MU AZABAR KABARI DA SABUBBANSA:
KABARI Shine Masauki Na Farko Na Lahira, Shine Wurin da Ake Turgude Mutum Cikinsa Bayan Ajalinsa Yazo Karshe a Rayuwar Duniya. Mutum Yana Kasancewa ne da Aikinsa Kawai a Cikin Kabarinsa. Amma Dukiyarsa da Iyalansa Zasu Rabu Dashi a Ranar da Yafi Bukatarsu.
Duk Wanda Ya tsira Daga Azabar Kabari Abinda Zai Biyo Baya Yafishi Sauki, Duk Wanda Kuma Bai tsira daga Gareshi ba, Bala'in da Zai Biyo Baya Yafi Wanda Zai Tarar a Cikin Kabarin. Kamar Yanda Manzon Allah (S.A.W) Yake Cewa:
عن ﻋُﺜْﻤَﺎﻥ ﺑْﻦ ﻋَﻔَّﺎﻥَ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ، ﺃﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ: ”ﺇِﻥَّ ﺍﻟْﻘَﺒْﺮَ ﺃَﻭَّﻝُ ﻣَﻨَﺎﺯِﻝِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮَﺓِ ﻓَﺈِﻥْ ﻧَﺠَﺎ ﻣِﻨْﻪُ ﻓَﻤَﺎ ﺑَﻌْﺪَﻩُ ﺃَﻳْﺴَﺮُ ﻣِﻨْﻪُ ﻭَﺇِﻥْ ﻟَﻢْ ﻳَﻨْﺞُ ﻣِﻨْﻪُ ﻓَﻤَﺎ ﺑَﻌْﺪَﻩُ ﺃَﺷَﺪُّ ﻣِﻨْﻪُ“.
{ﺍﻟﺘﺮﻣﺬي: ٢٣٠٨}
An Kar6o Daga Uthman bn Affan (R.A), Lallai Manzon Allah (S.A.W) Yace: “Lallai Kabari Shine Farkon Masaukin Lahira. Idan Ka tsira Daga Gareshi, Abinda Zai Biyo Bayansa Yafishi Sauki. Idan Kuma Baka tsira daga Gareshi ba, Abinda Zai Biyo Bayansa Ya Fishi tsanani”.
{Tirmizi:2308}
AZABAR KABARI Gaskiya ne Kuma Wajibi Ne Yin Imani dashi, Kamar Yanda Dalilai Daga Cikin Alqur'ani da Ingantattu Hadisai S**a Tabbatar, Kamar Yanda Ubangiji Ya Ambata a Cikin Suratu Ghafir da Wãqi'ah. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (S.A.W) Yace:
ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻗﺎﻝ: ”ﺇِﻥَّ ﻟِﻠْﻘَﺒْﺮِ ﺿَﻐْﻄَﺔً ﻭَﻟَﻮْ ﻛَﺎﻥَ ﺃَﺣَﺪٌ ﻧَﺎﺟِﻴًﺎ ﻣِﻨْﻬَﺎ ﻧَﺠَﺎ ﻣِﻨْﻬَﺎ ﺳَﻌْﺪُ ﺑْﻦُ ﻣُﻌَﺎﺫٍ “
{ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ}
An Kar6o Daga Aisha (R.A), Lallai Annabi (S.A.W) Yace: “Lallai Kabari Yanada Wata Matsa (da Yakeyiwa Mutum), Da Wani Zai tsira daga Wannan Matsar, da Sa'ad bn Mu'az Ne Zai Kasance Wanda Zai tsira daga Gareahi”.
{Ahmad Ya Ruwaitoshi}
YA ALLAH KA TAUSAYA MANA KA TSAREMU AZABAR KABARI BIJAHI RASULILLAHI (S.A.W)🙏🙏🙏
01/10/2024
BIDA MAZA DAN SHEHU, MAI HANKALI YAJI TSORON SARKI:🏹🔥👑
Allah Ya Kara Nunawa Maqiyan Sarki Abunda Basaso, Allah Duk Wanda Yadamu Sarki Allah Yadameshi, Allah Ya Karawa Sarki Lafiya Da Kwanciyan Hankali, Allah Yasa Sarki Ya Gama Da Duniya Lafiya.🙏👍✊🤲👑🔥🏹
01/10/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
NASIHA MAI TSADA:
Me Za Ka Lizimta?
Sheikhul Islam Ibnu Taimiyyah _rahimahullah_ yana cewa: "Abinda ya kamata ga mumini ya kiyaye wani wuridi na Zikiri (na safe) da rana da kuma lokacin bacci. Ya nace a kan haka duk yadda hidimomi s**a rutsa shi. Nan take zai samu taimakon Allah; imani mai karfi ya ratsa zuciyarsa. Abinda ya fi wannan muhimmanci shi ne ya yi kokarin cika farillai zahiran da badinan; kada ya yi sakaci da salloli biyar domin su ne ginshikin addini. Ya saba ma bakinsa da fadin: _La haula wala quwwata illa billah_ domin ita ce take yaye damuwa, ta kyautata yanayi. Kada mutum ya kosa da yin addu'a da nema daga wurin Allah. Amma fa kada ya kuskura ya yi ma Allah gaggawa; ya ce, na roka har na gaji bai karba ba. Ya san cewa, taimakon Allah yana tare da mai hakuri, sauki yana tare da tsanani, hutu yana tafe bayan wahala. Duk wanda ka ga ya samu alheri sai da ya yi hakuri tun daga Annabawa har kasa".
Majmu' Al-Fatáwá (10/137).
Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W).
Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Safiya.
30/09/2024
SARKI GARBA NA UKU 🐘🔥🤲🙏👑
KAINE MAI BUGUN MAZA.
SANNAN KAINE MAI WATSA MAZA.
KAINE DUTSE CINIKIN KIFIYA..
KAINE KAMFA SARKIN TAURI..
KAINE MAI HANA DUBGI SHIGA 'KASA.
KAINE MAI MAGANIN DAMISA KO YANZU...
Allah Ya Kara Daura Sarki Akan Maqiyansa, Allah Yasa Sarki Ya Gama Da Duniya Lafiya. 🐘🔥👑🤲🙏
30/09/2024
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
KUNSAN MECECE GIBA KUWA?
"Gulma, giba, yida mutum, duk sun yawaita a wannan zamani, kuna zaune da mutane a tare, da zarar ka tashi zasu fara yin gulmarka, ko kuma wani zaizo wucewa sai kawai su hau yin gulmarsa, sun ɗauka cewa Allah bazai tambaye su abisa duk abinda s**a kasance suna aikatawa ba"
-
"Giba, wacce da hausa ake kiranta da 'cin naman mutum' wato yi-da mutum alhalin baya-nan, to haramun ne, domin musulunci yayi hani da aikata duk abinda zai taɓa mutuncin wani, abinda bakaso, to kaima kada kayiwa wani shi, bakaso ayi gibarka, to kaima kada kayi gibar wani, domin lallai ita tanada girman zunubi a wajen Allah"
-
"An karɓo hadisi daga abu-hurairata Allah ya ƙara masa yarda yace: Manzon Allah (S.A.W), yace: shin kunsan mecece giba kuwa?, sai yace: to itace ambaton ɗan-uwanka da abinda bayaso, idan ya kasance abinda ka faɗa akansa ɗin gaskiya ne, to kayi gibarsa, idan kuma abinda ka faɗa ba haka bane, to haƙiƙa kayi masa buhtani, (kayi masa ƙage)"
Sahih Al-Jam'i (86)
Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W).
Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Safiya.