07/14/2023
MALAMA DA ƊALIBI
A duk lokacin da ta jefa ƙafarta cikin aji, yaran da ke hargowa kan ɗauke wuta, su yi tsit kamar ruwa ya ci su! Ba komai suke tsoro ba irin banbamin faɗanta da kwakwazo, sai ka ce kaza mai sabuwar ƙyanƙyasa.
A cikin ajin nan babu yaron da Malama Tina ta fi kyara kamar Audu, saboda rashin ƙoƙarinsa. Ran nan da ta ba su aiki sai ya samu sifili. Ta kuwa hau shi da masifa har ta daddangware shi tana cewa, "ba ka da wani amfani." Tun daga ranar, Audu ya ɗauke ƙafarsa daga makarantar.
Bayan wasu shekaru Malama ta yi ritaya, aka fid da ita daga gidan makaranta, ta tattara 'yan komatsanta ta koma tsohon gidanta. Ruwan farko na damina ya tabbatar mata da gidan nan na buƙatar kwaskwarima. Ta nemo masu gyara. Injiniya ya zagaya gidan nan ko'ina, ya ce mata, "Madam, wannan gida ai ya cika lalacewa, abin da na ga ya fi shi ne, a rushe shi a sake sabo, a yadda yake yanzu, ba shi da wani amfani."
Malama ta yi jugum tana tunani, ina ta ga kuɗin gina sabon gida? Da Injiniya ya ga ta shiga damuwa, sai ya matsa kusa gare ta yana murmushi ya ce, "kada ki damu, gidanki zai gyaru ko ba a rushe shi ba. Zan kuma gyara miki shi kyauta. Kin gane ni?"
Ta dube shi, ta kasa gane shi.
Ya ce, "Ni ne ɗalibinki Audu." Da ta sake duban shi, sai ta gane shi. Ya ci gaba da cewa, "kamar yadda kalamaina s**a sare miki gwiwa yanzu, haka kalaman da kika taɓa furtawa gare ni s**a so su yi tasiri a kaina. Iyayena s**a ƙarfafa mini gwiwa da kalamai masu daɗi, na ci gaba da karatu a wata makarantar, ga shi yanzu na zama babban injiniya. Da a ce na biye wa kalamanki, da wataƙila yanzu ina daji rataye da bindiga."
Malamai da iyaye, a riƙa gaya wa yara kalamai masu ƙarfafa gwiwa. Yara manyan gobe!
Bukar Mada
13/07/2022