20/04/2024
AIKIN HAJJI 51
✈️✈️✈️
🛫🛫🛫
🕋🕋🕋
👇👇👇👇👇
Wanda ya yi Harama da Hajji ko Umra daga Makka sannan tsayuwar Arfa ta kucce masa, sai ya yi Tahalluli da Umra bayan ya fita daga Hurumi ya shiga Hillu, don ya haɗa tsakanin su. Bayan haka ramuwar Hajji da Hadaya suna wajaba a kansa, a Shekara mai zuwa. Kuma Hajjin Farilla ba zai faɗi ba daga gare shi ko da tsarewar maƙiya ne.
👉Wanda aka tsare ga Hajjin Nafila, to zai rama shi, idan tsarewar ta kasance saboda rashin lafiya ne ko ɗauri na shari'a.
Ba za a biya Hajjin ba idan tsarewar maƙiya ne ko wata fitina a tsakanin Musulmi ko ɗauri da Zalunci.
( *WANNAN SHI NE DASI NA ƘARSHE A KAN AIKIN HAJJI ALLAH YA BAMU ILIMI MAI AMFANI* )
👇👇👇👇👇
WhatsApp 07031661338
Calling 0808334310
Gmail [email protected]
Aliyu Ibrahim Zuru