27/05/2026
EID AL-MUBARAK
Sayyid tare da iyalan sa cikin farin ciki da natsuwa bayan sallar EID wannan abin farin ciki ne ga daukakin Al-umma yan uwa baki daya Don haka mu ake salati guda daya da nufin Allah ya ƙarawa Sayyid da iyalansa lafiya
27/05/2026
Taujihi:
“An yi magana dangane da Shubuhohi da ake turowa, da waɗansu Afkar (Fikirori) da akan riƙa ingizowa, duk shi ma hanyar faɗa da Da'awa din ne ai. Hanyar faɗa da Da'awa shi ne a riƙa turo maka waɗansu Shubuhohi. Kuma cikin Harka ake shigowa da su, cikin 'yan uwa ake so a shigo da shi. Domin bai da amfani (daga) waje.
“In wani yana da wata irin Da'awarsa ta daban, ta sukan Harka, sai ya je kawai yana abinsa a waje guda, to ai ba zai yi tasiri ba. Ya fi son ya shigo cikin Harkar ya cusa. Saboda haka za a lura da irin wannan kutso da Afkar din da ake yi da yawa.
“Wasu kuma abin takaici daga waje suke ɗebo (irin waɗannan Afkar din), wasu har daga Jamhuriya. Don ko da kuka ga an yi revolution din nan, ana ganin kamar 100 bisa 100 duk duk mutane na tare da revolution, akwai maƙiya, har yanzu ma ana zaƙulo munafukai. Har fa akwai waɗanda suke taimakawa maƙiya, har yanzu ana zaƙulo su. Saboda haka akwai maƙiya, ko da mutum yana da rawani baƙi ko fari, za ka iya ganinshi sosai shi maƙiyi ne. Amma ban ce muku fa wai duk in ka ga mutum da rawani baƙi ko fari maƙiyi ne ba, amma a cikinsu akwai maƙiya. Kuma wasu ba za su taba nuna maka su maƙiya ba ne, sai idan sun aminta maka, sai su fito maka da wannan nau'i ɗin. To su suke kitsa wadannan abubuwa.
“Za ka ga suna kitsawa daga can, suna zuwa da waɗansu abubuwa. Har mukan ce, to ba mu ƙi (ka je) ka yi karatu ba, amma Fikira ya kamata ya zama kana da Fikirarka. Ba Fikira za a koya maka ba. In mutum ya iya Lugga, ya koyar da kai Lugga din, in ya iya Usul, ya koyar da kai Usul, in ya iya Mandiqi, ya koyar da kai Mandiqi, amma Fikira ba zai koya maka ba. Zuruf ɗin ƙasarku kuma bai sani ba. Kai ka san Zuruf din ƙasarku, kai ka san kuma yadda ya kamata ka fito ma al'amura a inda kake. Ba zai ce maka in ka je ƙasarku ka yi kaza ba. Don shi yadda yake kallonku daban ne.”
— Ɓangaren jawabin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) ga Muballigun, a yayin rufe Mu'utamar Lijanut Tarbiyya wat-Tableeg a ranar 15 Zulƙa'ada 1447 (3/5/202
24/05/2026
Sanarwa:
Game Da Batun Tashar ABS TV A YouTube
Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Ana ta tambaya mai ya samu channel ɗin ABS TV dake shafin YouTube, sakamakon kwana 2 mutane na neman tashar ba'a ganinta.
Abin da ya faru shi ne; YouTube sun sauke wasu bidiyoyin da ke shafin, irin yadda shafin Facebook su ke cire postings ɗin da basu dace da tsarinsu ba.
Daga baya kuma sai su ka dakatar da shafin, abin da ake ce ma ban; amma zuwa yanzu ana ƙoƙarin dawo da shafin. In an yi nasarar yin haka shikenan, in ba a yi nasara ba, za a sanar da sabon shafin na YouTube nan gaba, Insha Allah.
24/05/2026
24/05/2026
Kai da kaga wannan fuskar kasan ta riga da ta wuce raini ako ina na umma me komai da yakinin kenan
1_shine mafitarmu Duniya da lahira
2_shine Akbar min ansarul imamul Mahadi
3_shi musulunci ke kallo yaji yana da jagora
4_kuma shine...........
23/05/2026
ZAGE-ZAGE DA CIN MUTUNCIN BAI KAMATA GA SISTA KO BURAZA BA
___INB ABEEH (MUHAMMAD BAKIR)
Shi dan gwagwarmaya ba a sanshi da mummunan aiki ba kuma bai can canta ga sista ko BURAZA yake zage-zage ako inaba b***e kuma a social media wannan ba koyarwar jagora bace
sista/buraza yana da kyau mugane mafitarmu kawai shine yin aiki domin Allah sabo da temakon jagora kuma Hakan bayana nufin Mu fitini wasu a harka bane har su barta to idan sun barta shin hakan ƙaruwar muce ??
mu sani cewa duk abin da muke yi na Al-kairi temakon Imam Mahadi ne haka kuma idanma sharri ne zagon ƙasa muke yi agareshi yana da kyau yan, uwa mudawo hayyacinmu don mu gane kiran da jagora yake yi akan mu
Idan kuma muka cigaba da rabuwa to makiya ne zasu shiga tsakanin mu fatan mun gane ai. to Allah 🤲 ya ƙara mana juriya da sabati
17/05/2026
Da ba dan takofin Imam Ali ba da musulunci baiyi nasara ba
16/05/2026
ALMAHIRAN TSANGAYA NE KAƊAI ZASU IYA SANIN MEYE WANNAN
15/05/2026
RANAR BUNAYE TA DUNIYA
Wannan itace Ranar bunaye ta duniya wanne fata zakuyimusu
20/04/2026
Day and night view of the royal clock tower.... 🕋
Unveiling History: The 4,500-Year-Old Tunic at the Egyptian Museum"🥰🥰🥰🥰
Treasures
19/04/2026
Ga Darasu Ƴan Uwa Kowa Ya Matso Kusa Ya K**a Nashi ✍️
Tsangaya ce Asalimmu 💝✅