27/09/2026
الجملة الاسمية - JUMLAR DA TA FARA DA SUNA
التعريف / Ma'ana:
هي الجملة التي تبدأ باسم وتتكون من مبتدأ وخبر.
Hausa: Jumla ce da take farawa da suna, ta kunshi Mubtada'i (wanda aka fara da shi) da Khabar (labari game da shi). Ba ta bukatar fi'ili.
Hukuncinta: Mubtada' da Khabar kullum MARFU' ne!
# # # # أركانها - Ginshikanta Guda 2
1. المبتدأ - Mubtada' (Abin Magana)
Shi ne sunan da aka fara magana da shi. Yana buqatar labari.
Misali: الطالبُ - Dalibin (to me ya same shi?)
Misali: السماءُ - Samaniya...
2. الخبر - Khabar (Labari)
Shi ne wanda ya cika ma'anar Mubtada' din. Idan ba shi ba, ma'ana ba za ta cika ba.
Misali: الطالبُ مجتهدٌ
Mubtada' = الطالبُ
Khabar = مجتهدٌ (mai kokari)
Ma'ana ta cika: Dalibin mai kokari ne.
---
# # # # أنواع الخبر - Nau'o'in Khabar Guda 3
1. خبر مفرد - Khabar Kalma Daya
Khabar da ba jumla ba ce, kuma ba jar da majrur ba. Kalma daya ce kawai ta siffanta Mubtada'.
الطقسُ جميلٌ
Mubtada': الطقسُ | Khabar: جميلٌ
Hausa: Yanayi mai kyau ne.
المعلمُ نشيطٌ
Malami mai himma ne.
2. خبر جملة - Khabar da ke Jumla ce
Khabar din kanta jumla ce - ko dai Fi'liya ko Ismiya. Dole sai ta dawo da damir zuwa Mubtada'.
أ. خبر جملة فعلية:
الطالبُ يدرسُ بجدٍّ
Mubtada': الطالبُ
Khabar: Jumla ce يدرس بجد - Fi'ili + Fa'il mustatir (yana dawowa ga الطالب)
Hausa: Dalibi yana karatu da himma.
ب. خبر جملة اسمية:
الحديقةُ أزهارُها متفتحةٌ
Mubtada' 1: الحديقةُ
Khabar: Jumla Ismiya أزهارها متفتحة
- أزهارها = Mubtada' na 2
- متفتحة = Khabar na 2
Hausa: Lambun furanninsa a bude suke.
3. خبر شبه جملة - Khabar da ke kamar Jumla
Yana kasancewa Jar da Majrur, ko Zarf (lokaci ko wuri).
الماءُ في الكأسِ باردٌ
Amma idan muka tsaya a الماءُ في الكأسِ ma'ana ta cika?
Eh, ta cika a iya fahimta, don haka في الكأس shine Khabar Shibh Jumla.
Hausa: Ruwa yana cikin kofi.
الكتابُ فوقَ الطاولةِ
Littafi yana saman tebur. فوق الطاولة shine Khabar.
---
نصيحة ذهبية - Nasiha ta Zinari:
> المبتدأ دائماً مرفوع • الخبر دائماً مرفوع
Kuyi following dinmu