08/11/2023
NASIHA MAI MUHIMMANCI
Sheikh Mashoor Binu Hassan Âlu Salman (HafizahulLah) yana cewa: "Manyan mas'aloli ba wanda ya cancanta ya yi magana akan su sai manyan malamai. Saboda sune s**a san yadda ya kamata a mu'amalanci mas'alolin. Sune s**a san lokacin da ya dace a yi magana da kuma lokacin da ya dace a yi shiru. Kai ɗalibin ilimi tsoma baki ko tofa albarkacin baki akan kowace sabuwar mas'ala, ba wajibi ba ne akan ka; Allah bai kallafa maka ba, haka kuma al'umma ba ta buƙatar haka daga gare ka. Saboda haka bai dace ba ka ɗaura wa kanka aikin tsoma baki a cikin duk wata sabuwar mas'ala"