19/08/2026
SANARWAR KAMMALA DAURAR HUTU DA KOMAWA MAKARANTA
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
In shā Allah, idan Allah Ya kai mu gobe lafiya, za mu kammala Daurar Hutu ta tsawon makonni huɗu (4) da muka gudanar.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya albarka da amfani a cikin ilimin da muka koya, Ya kuma ba mu ikon yin aiki da shi.
📚 RANAR KOMAWA MAKARANTA
- Sashen Hadda (Tahfīẓ): Alhamis, 27/08/2026
- Sashen Islamiyya: Asabar, 29/08/2026
- Sashen Boko: Litinin, 07/09/2026
📝 ANA CI GABA DA ƊAUKAR SABABBIN ƊALIBAI
Muna sanar da iyaye da masu ruwa da tsaki cewa ana ci gaba da ɗaukar sabbin ɗalibai a dukkan sassan makarantar mu masu albarka.
🎯 Manufarmu:
Samar wa yara ingantaccen ilimin Addini da na Boko, tare da kyakkyawar tarbiyya da ɗabi’a.
«KU TUNA: TARBIYYA AMANA CE!»
A ƙarshe, muna roƙon Allah Ubangiji Ya dawo da mu makaranta lafiya, Ya ƙara wa makarantar mu albarka, Ya sanya karatunmu ya zama mai amfani a duniya da Lahira.
آمِين يَا رَبَّ الْعَالَمِينَ
19/08/2026
18/08/2026
17/08/2026
17/08/2026
14/08/2026
14/08/2026