Daarus Siddiq Abi Bakrin Litahfizil Qur'an Waddiraasaatil Islaamiyyah

Daarus Siddiq Abi Bakrin Litahfizil Qur'an Waddiraasaatil Islaamiyyah

Share

التصفية ثم التربية على المصفى

13/07/2026

END OF TERM NEWSLETTER (TAKARDAR SANARWA NA KARSHEN ZANGO)

13/07/2026

SAƘON BAN GAJIYA GA IYAYE/WAKILAN ƊALIBAI, MALAMAI, DALIBAI, MANYAN BAƘI, DA SAURAN MAHALARTA

Assalaamu Alaykum waRahmatulLah waBarakaatuh.

Alhamdu LilLah, cikin matuƙar farin ciki da godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa nasarar da Ya ba mu na gudanar da Yaumul Arab 1448AH/2026, muna miƙa saƙon ban gajiya ga dukkan iyaye/wakilan ɗalibai, malamai, ɗalibai, baƙi na musamman, da sauran mahalarta da s**a halarci wannan gagarumin taro.

Muna matuƙar godiya ta musamman ga iyaye/wakilan ɗalibai bisa goyon bayan da suke bai wa makaranta wajen tarbiyyar 'ya'yansu da ƙarfafa su wajen koyon harshen Larabci da ilimin addinin Musulunci. Allah Ya saka muku da mafificin alheri.

Haka kuma, muna yaba wa dukkan malaman makaranta (shuwagabannin gidaje) bisa jajircewarsa, sadaukarwarsu da ƙoƙarin da s**a yi domin ganin an gudanar da taron cikin tsari da nasara. Haƙiƙa ko wane gida daga cikin gidajen sun yi nasara. Allah Ya sanya hakan a cikin mizanin ayyukansu na alheri.

Ga ɗalibanmu kuwa, muna taya ku murna bisa irin ƙwazon da kuka nuna a dukkanin gasa da aka gabatar tsakanin gidaje na: waƙoƙi, wasan kwaikwayo (zaman kotu), da sauran abubuwan da aka gabatar. Allah Ya ƙara muku basira, fahimta, da ɗaukaka a duniya da Lahira.

Muna kuma godiya ga dukkanin baƙi da sauran mahalarta da s**a samu damar halarta tare da ƙarfafa mana gwiwa. Halartarku ta ƙara wa taron armashi da daraja.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi wannan aiki, Ya albarkaci makarantarmu DAARUS SIDDIQ ABI BAKRIN LI-TAHFEEZIL QUR'ANI WAD-DIRAASAATIL ISLAAMIYYAH, Ya ƙara bunƙasa harshen Larabci da ilimin Musulunci a tsakaninmu, kuma Ya ba mu ikon sake haɗuwa a karo na gaba a irin wannan shiri cikin ƙoshin lafiya da zaman lafiya.

Domin kallon cikakken ɗaukar taro, link na comment section

JazaakumulLahu khayran.
Wassalaamu Alaykum waRahmatulLahi wa Barakaatuhu

HUKUMAR MAKARANTA.

✍️
Abdullah AB
Sec. Media and Publicity, Daarus siddiq AbiBakrin..
27.01.1448 AH - 12.07.2026

12/07/2026
30/09/2025

دار الصديق أبي بكرٍ لتحفيظ القرآن والدراسات الإسلامية

دارنا الصديق ••• للتحفيظ والتربية
والعلم والإيمان ••• والأخلاق والقرآن
أخلاق والقرآن

حمدًا إلى الرحمن ••• يا خالق الإنسان
والجن والحيوان ••• يا منزل القرآن
يا منزل القرآن

12/08/2025

DAARUS SIDDIQ ABI BAKRIN LITAHFEEZIL QUR'ANI WADDIRAASAATIL ISLAAMIYYAH
_التصفية ثم التربية على المصفى_
TEL: 08131476446, 07039680980, 08146666946
Reminder International School, Opposite S/Gari Local Government Secretariat, Dogarawa, S/Gari, Zaria.
Annex: Kabama Phase III, Bagadaza, New Extension, Dogarawa, Sabon Gari, Zaria.

Our Ref.:………………………………….. Your Ref.:………………………………… Date: 10th August, 2025

Assalaamu Alaykum Wa RahmatulLahi Wa Barakaatuh..

TAKARADAR SANARWA NA KARSHEN ZANGO (END OF TERM NEWSLETTER)

Muna mika godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bamu ikon kammala wannan zango, Zango na uku (na ƙarshe) a shekarar karatu ta 2024/2025 (3rd Term 2024/2025 Academic session) cikin aminci.
Don haka Hukumar Makaranta na sanar da Iyaye/Wakilan ɗalibai abubuwa kamar haka:

1. HUTU: Za a tafi hutun ƙarshen zango na uku (3rd Term) a yau Lahadi 16, ga watan Safar, 1447 AH (10th August, 2025).
Za a dawo a ranar Asabar, 14/15 ga watan Rabi’ul Awwal, 1447 AH (6th September, 2025) In sha’Allahu.

2. ABUBUWAN DA MAKARANTA TA SABA TUNATARWA A KAN SU:(KUDIN MAKARANTA, LATTI DA FASHI, KAYAN MAKARANTA DA SAURANSU): Makaranta na ƙara jan hankalin ɗalibai da iyaye/wakilan ɗalibai musamman dangane da Latti (Rashin zuwa makaranta a kan lokaci), biyo bayan yawaituwar yin hakan, Wanda so da yawa yake da alaƙa da rashin kulawa ko rashin muhimmantawa da sakaci da ake samu daga wasu ɗalibai ko iyaye. Don haka makaranta na ƙara jaddada hukuncin mayar da ɗalibi gida idan ya kai 8:15am bai iso makaranta ba, kuma za a hukunta hakan a matsayin fashi.

Daga ƙarshe, Hukumar Makaranta na yi ma iyaye/wakilan ɗalibai tuni akan kuɗin makaranta, tare da yi muku fatan Alkhairi a ko da yaushe, Allah yasa muyi hutu lafiya. JazaakumulLahu
Khayraa..

HUKUMAR MAKARANTA

✍️
Abdullah Ahmad Bello
Sec. Media and Publicity
Daarus Siddiq Abi Bakrin..

25/04/2025

DAARUS SIDDIQ ABI BAKRIN LI TAHFEEZIL QUR’ANI WADDIRAASAATIL ISLAAMIYYAH
Tel.: 08131476446, 07039680980, 08146666946.

27-Shawwāl-1446H
25th April, 2025G

Assalamu Alaykum waRahmatulLah..

MUHIMMIYAR SANARWA GAME DA KOMAWA MAKARANTA

Hukumar makaranta tana mai sanar da iyaye/wakilai ɗalibai cewan an sake ɗage komawa makaranta (a karo na biyu), wanda a baya aka ambaci za'a koma a gobe Asabar, 26/04/2025 (28/10/1446H) - sashen Haddar Al-Qur'ani da Islamiyyah (da ke Meridian Dogarawa) saboda uzurin cigaba da aikace aikacen gyara da ake yi domin inganta makaranta da wurin karatu.

Alhamdu LilLahi, Zuwa yanzu an ci ƙarfin aikin gyare-gyaren, saidai ba'a kai ga gama gyaran bayi (Toilet) ba, wanda sanannen abu ne cewan ba zai yiyu ayi karatu a makarantar ba tare da an buƙaci mu'amala da bayi (Toilet) ba.

SASHEN ISLAAMIYYAH NA YAMMA (DOGARAWA - KUSA SA SAKATERIYA):
Hukumar makarantar ta ƙara hutun kwanaki biyu a sashen saboda uzurin da aka ambata.
Za'a dawo makaranta (a cigaba da karatu) a ranar Litinin, 28-05-2025 (01-11-1446H) inn sha'Allah.

SASHEN HADDAN AL-QUR'ANI MAI GIRMA:
Hukumar makaranta ta ƙara hutun sati ɗaya a sashen ƙarƙashin uzurin da aka ambata.
Za'a dawo makaranta (a cigaba da karatu a sashen) a sati mai zuwa, ranar Asabar, 02-05-2025 (4/5-11-1446H) Inn sha'Allah.

TUNATARWA:
A ƙarshe, Hukumar makaranta tana mai tunatar da iyaye/wakilan ɗalibai game da kuɗin makaranta na sabon zangon da za'a shiga, ayi ƙoƙarin biyan kuɗin makaranta kafin dawowa.
Kuɗin makarantar kowane ɗalibi:
• Sashen Haddan Al-Qur'ani - #3,500
• Sashen Islaamiyyah (Dogarawa) - #3,000

Muna yi muku fatan Alkhairi a koda yaushe.

✍️
Abdullah Ahmad Bello
Sakataren Makaranta,
Sashen Sabbin Zauruka na sada zumunta.
Jumu'ah (27.10.1446H - 25.04.2025G)

13/04/2025

SAKON TA'AZIYYA

Hukumar wannan makaranta tana miƙa saƙon Ta'aziyyar ta zuwa ga Malaminmu Mal Abubakar Hussaini Al'athariy Cikaji (Director, Daarul Hadeethil Ashrafiyyah Chikaji, Sabon Gari, Zaria.) bisa ga rasuwar iyalinshi a yau, wacce take 'yar uwa (ƙanwa) ga Malaminmu AlHafiz Imam Abbas Uzairu Cikaji.

Ta'aziyya zuwa ga dukkanin 'Yan uwa (Yayyi, Ƙanni, 'Ya'ya) da abokan arziki bisa ga wannan rashi.

Za'a gabatar da Sallar Jana'iza da ƙarfe 2:00pm a Chikaji, Sabon Gari, Zaria.

Muna roƙon Ubangiji Ya jiƙanta, Ya gafarta mata, Allah Ya ƙara ma malam da sauran 'yan uwa haƙuri da juriyar rashin ta.

✍️
Abdullah Ahmad Bello
Sakataren Hukumar Makaranta,
Sashen Sabbin Zauruka na sada zumunta.
15/10/1446H
13/04/2025G

11/04/2025

DAARUS SIDDIQ ABI BAKRIN LI TAHFEEZIL QUR’ANI WADDIRAASAATIL ISLAAMIYYAH
Tel.: 08131476446, 07039680980, 08146666946.

13-Shawwāl-1446H
11th April, 2025G

Assalamu Alaykum waRahmatulLah..

MUHIMMIYAR SANARWA GAME DA KOMAWA MAKARANTA

Da fatan anyi sallah lafiya, Allah ya karɓa mana ibadunmu.

Hukumar makaranta tana sanar da iyaye/wakilai ɗalibai cewan an ɗage komawa makaranta a gobe Asabar, 12/04/2025 (14/10/1446H) a sashen Haddar Al-Qur'ani da Islamiyyah (da ke Meridian Dogarawa) saboda uzurin aikace aikacen gyara da ake yi domin inganta makaranta da wurin karatu.

Za'a dawo makaranta a ranar Asabar, 26/04/2025 - 28/10/1446H Inn sha'Allah

A KULA (SASHEN ISLAAMIYYAH - BAGADAZA):
Za'a koma makaranta a gobe inn sha'Allahu kasancewar uzurin bai shafi sashen ba.

A ƙarshe, Ana tunatar da iyaye/wakilan ɗalibai game da kuɗin makaranta na sabon zangon da za'a shiga, ayi ƙoƙarin biyan kuɗin makaranta kafin dawowa.

JAN HANKALI:

A kula da duk wani labari da yake yawo na jita-jita da sunan za'a haɗe ɗaliban wani sashe da wani sashe (domin ayi karatu), babu gaskiya a cikin wannan labarin ko kaɗan.
Hukumar makaranta ce take da Hurumin yaɗa bayananta da kanta ta hanyoyin da s**a dace.

Ƙarƙashin wannan ana iya tuntuɓar ɗaya daga cikin lambobin makaranta domin tabbatar da ingancin duk wani jita-jita.

Muna yi muku fatan Alkhairi a koda yaushe.

✍️
Abdullah Ahmad Bello
Sakataren Makaranta,
Sashen Sabbin Zauruka na sada zumunta.
13.10.1446H - 11.04.2025G

Want your school to be the top-listed School/college in Zaria?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address

Meridian International School, Opposite Sabon Gari Local Government Secretariat, Dogarawa
Zaria

Opening Hours

Thursday 16:00 - 18:00
Friday 15:00 - 18:00
Saturday 08:00 - 13:00
Sunday 08:00 - 13:00