09/05/2026
Da ɗumi-ɗumi: A cikin awa 4 kacal an tara naira milyan N45.7m domin sayen fom ɗin takarar El-Rufai a 2027
Ƙungiyar magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, , ta bayyana cewa ta samu nasarar tara kuɗi har Naira miliyan 45 da dubu 750 cikin sa’o’i huɗu kacal domin sayen fom ɗin nuna sha’awa da tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC a zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin babban nuna goyon baya da haɗin kai daga magoya bayan El-Rufai, tana mai cewa wannan ba tara kuɗi ba ne kawai, illa wata alama ce da ke nuna yadda jama’a s**a rungumi tafiyar siyasar tasa.
A cewar ƙungiyar, “Wannan murya ce daga dubban magoya baya masu cewa da zuciya ɗaya: Mallam, muna tare da kai.”
Ƙungiyar ta kuma gode wa duk waɗanda s**a bayar da gudummawa, tana mai cewa wannan goyon baya ya nuna cewa har yanzu tafiyar siyasar El-Rufai na ƙara samun karɓuwa a faɗin ƙasar nan.
“The Movement is Rising” — in ji sanarwar da aka fitar tare da jaddada cewa tarihi na ci gaba da sauyawa ta hannun jama’a.
17/04/2026
17/04/2026
08/09/2025
08/08/2025