11/06/2026
Masu Hidima ga Littafin Allah
Ya ku masu hidima ga Al-Qur'ani, Masu karatu da koyarwa dare da rana, Ku ne fitilun al'umma, Masu yada hasken shiriya a ko'ina.
Kun rungumi kalmar Allah, Kun sadaukar da lokaci da rayuwa saboda ta, Albarkar Al-Qur'ani na tare da ku, Kuma ladan Ubangiji na jiran ku.
Masu haddar Al-Qur'ani, masu koyarwa da masu aiki da shi, Ku ne taurarin shiriya ga al'umma, Allah Ya ƙara ɗaukaka ku, Ya sanya Al-Qur'ani hujja gare ku ba hujja a kanku ba.
إِنَّ الَّذِينَ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَنفَقُوا مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً يَرْجُونَ تِجَارَةً لَنْ تَبُورَ لِيُوَفِّيَهُمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدَهُمْ مِنْ فَضْلِهِ ۚ إِنَّهُ غَفُورٌ شَكُورٌ
Ma'ana: “Lallai waɗanda suke karanta Littafin Allah, s**a tsayar da Sallah, kuma s**a ciyar daga abin da Muka azurta su da shi a asirce da bayyane, suna fatan wata kasuwanci wadda ba za ta taɓa yin asara ba. Domin Ya cika musu ladansu, kuma Ya ƙara musu daga falalarsa. Lallai Shi Mai yawan gafara ne, Mai yawan godiya (ga ayyukan bayinsa).”