Tech With Raizsan

Tech With Raizsan

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tech With Raizsan, Computer training school, Delivery Available (With Yola Included), Yola.

11/07/2026

📱 Meta Ta Cire AI Feature Da Ke Bawa Kowa Damar Yin Deepfake Da Hotonka — Ba Tare Da Izininka Ba!

Shin ka san cewa Meta ta taɓa gabatar da wani AI feature akan Instagram mai suna Muse Image, wanda ke bawa kowa damar @-mention wani public account (koda ba naka bane) sannan AI ta generate hotuna daga posts din, ba tare da an tambayi mai account din izini ba?

Meta ta ce manufar feature din shine domin taimaka wa mutane su design custom invitation ko su yi creative concepts. Amma bayan mutane da yawa s**a koka, har da kamfanin Hollywood na CAA (wanda ke wakiltar shahararrun mutane kamar Tom Hanks da Meryl Streep) da kuma union din SAG-AFTRA, Meta ta yanke shawarar cire feature din gaba daya, tana mai cewa feature din "bai yi daidai ba" (missed the mark).

💡 Darasi: Idan account naka public ne akan Instagram, koyaushe duba Settings dinka — musamman option din "Allow people to create with and reuse your content." Idan baka son wani ya yi amfani da hotonka wajen AI generation, ka toggle off wannan option ko ka mai da account dinka private.

Privacy dinka na hannunka ne — kar ka bari technology ta wuce ka!

Shin ka taɓa duba Settings na Instagram dinka domin ka ga ko wani zai iya yin amfani da hotonka ta hanyar AI? Bari mu ji ra'ayinka a comment! 👇

30/06/2026

Samsung Galaxy na da wani Hidden Multitasking Feature da mutane da yawa ba su sani ba Yana baka damar amfani da Apps biyu a lokaci guda!

đź“° Menene ya faru? (What happened?)

Samsung ya dade yana da wani feature mai suna Pop-Up View a cikin Galaxy phones, wanda yake taimaka maka ka yi amfani da apps fiye da É—aya a lokaci guda.

Yanzu ana magana sosai akan sabon App Bubbles da ake shirin samu a Android 17, amma gaskiyar magana ita ce Samsung ya riga ya kawo irin wannan tsarin tun shekaru da s**a wuce.

Wannan feature yana baka damar buɗe app kamar WhatsApp, YouTube, Browser ko Calculator a ƙaramin floating window yayin da kake amfani da wani app daban.

đź’ˇ Me yasa wannan yake da muhimmanci? (Why is it important?)

Yawancin mutane suna amfani da waya ne kawai ta hanyar buÉ—e app É—aya su rufe shi kafin su shiga wani.

Amma wayar zamani tana iya yin abubuwa da yawa.

Misali:
Kana kallon YouTube amma kana son amsa WhatsApp.

Kana karanta bayani a Browser amma kana son rubuta notes.

Kana lissafin kudi yayin da kake duba wani message.

Pop-Up View yana taimaka maka ka yi hakan cikin sauƙi.

👥 Wa zai amfana? (Who will benefit?)

Wannan zai taimaka sosai ga:

âś… Dalibai masu karatu da bincike online
âś… Masu kasuwanci masu amfani da WhatsApp da sauran apps
âś… Content creators
✅ Ma’aikatan office
✅ Duk wanda yake son amfani da wayarsa cikin sauri da ƙwarewa

📱 Yadda zaka amfani da shi (How to use it)

Idan kana da Samsung Galaxy:

1. BuÉ—e Recent Apps
2. Danna alamar app É—in da kake so
3. Zaɓi Open in pop-up view

Ko kuma:

1. Je zuwa: Settings → Advanced Features → Multi Window

2. Kunna: Swipe for pop-up view

Daga nan zaka iya jan app ɗin, rage shi, ƙara girmansa, ko mayar da shi kamar ƙaramin icon.

🌍 Misali na rayuwa (Real-life example)

Misali kai É—alibi ne:

Kana kallon wani lesson video akan YouTube, amma kana son rubuta muhimman bayanai a Notes.

Maimakon ka fita daga YouTube, zaka iya saka YouTube a ƙaramin window sannan ka buɗe Notes a gefe.

Hakan yana sa ka yi aiki kamar kana amfani da ƙaramin computer.



✍ Muhammed Bala

11/01/2026
10/01/2026

Cikin wadannan Company wanne kataba amfani da, kuma kafi jin dadi HP, Dell, Lenovo, Asus, Apple, Acer, Toshiba, Compaq, ko Samsung?

09/01/2026

Dell Latitude 5470, mai Lightning keyboard, Core i5, Battery 🔋 Excellent👇👇

08/01/2026

Wannan itace geo very portable computer mai long battery life wacce zaku iya mallaka a farashin 85k kachal.👇👇

07/01/2026

Na'urar Computer zai maka abinda kake so ne kadai ta hanyar (Maintenance).

06/01/2026

Lenovo IdeaPad, Slim design

For office worker, graphics designer, web/ software developer, student e.t.c

As usual for consultation_
kada ka wuce wannan💯 👇👇

Want your school to be the top-listed School/college in Yola?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Delivery Available (With Yola Included)
Yola