Mai Tabara Unlimited

Mai Tabara Unlimited

Share

Health education

12/09/2025

HUƊUBAR JUMA'A!

Ya ku talakawa ƴan uwana...

Kun ga wannan duniyar? Allah Ya raba tsakanin talaka da mai kuɗi kamar yadda ya raba tsakanin sama da ƙasa.

A duk inda ka shiga a wannan duniyar, ana bambanta talaka da mai kuɗi, a gefen hidimomi da sauran al'amura na rayuwa.

Misali; idan kaje Asibiti, akwai wasu ɗakuna da ake kira “private suit" inda zaka tarar akwai A/C, katifa mai laushi, yana kamshi, kuma mutum ɗaya kacal a kowane ɗaki. Hakan nan zaka ga likitoci suna kai komo tsakanin waɗannan ɗakunan. Shi kuma Talaka an bar shi a ward... Daga shi sai fanka, ga bala'in wari in ka shiga ward ɗin, sau daya likita yake zagayawa a rana.

Duk da haka, shi mai kuɗi yawancin lokaci ya fi yarda da yaje private hospital, saboda an fi samun kulawa a can, amma fa kuɗin jinyan su ya ninka na asibitin gwamnati sau biyar, ko ma fiye da haka.

Idan zaka shiga jirgi, akwai Business class (VIP) wanda aka tanadarwa masu kuɗi, idan kai talaka ne sai a ɗura ku a cikin "Economy class" kamar yadda ake ɗura Awaki a babbar mota, in za a kai su Kurmi ko Onitsha. Wani zubin zaka shiga pasinja da wani attajirin har ku sauka baka san yana jirgin ba.

A ɓangaren auratayya kam ba a magana, da wuya ka ga yaron Honourable ya auri ƴar Mallam Shehu, hakan nan ɗan Mallam Shehu sai dai ya hangi ƴar Honourable a Instagram ko Twitter idan yana da babbar waya.

Toh a ina ma zaka hadu da su har soyayya ta kullu? Jirgin su a VIP suke zama, idan ma ba private jet ko chartered flight s**a hau ba. Karatun su a London ne ko USA, shopping nasu a Dubai, hutun su a France ko Germany. Kai da baka taɓa tsallaka wa ko Niger ba a ina zaku hadu?

Kai, ko aikin Hajji ka je, zaka tarar yawancin hotels din da s**a fi kusanci da Harami, masu kuɗi ne suke occupying nashi saboda tsadar sa... Kai kuma talaka wani lokacin daga hotel naka zuwa Harami sai kayi tafiya kamar daga sokoto zuwa Rabah.

Kai! Ko a maqabarta, yawancin kaburburan masu kuɗi zaka gansu daban, zaka ga an zo an zuba yashi da wasu duwatsu, an kewaye shi da block an gyara shi. Zaka tarar duk kaburburan dake gefen shi sun ɓurme, amma shi yana nan kamar yau aka binne shi.

Wannan fa misalai kaɗan ne na kawo... Idan ka duba ko ta ina zaka tarar akwai irin wadannan abubuwan.

Kai Mallam talaka, aikin hankali da zaka yi shine ka bi Allah kayi aikin alheri, kuma ka guji haramun da duk dangogin sa... Saboda kai Lahiran nan ne kadai last hope naka.

In dai talaka ya mutu ya shiga wuta, Wallahi anyi masa 2-0, idan kuma mai kuɗin ya bi Allah yayi aikin alheri da kuɗin, watakila sai ka sake ganin shi a “VIP section" na gidan Aljannah 😆

Ka ga kenan ya yiwa talaka 5-0 irin yadda Barcelona ta saba yiwa yiwa Real Madrid.

Allah Ya tsare mu daga talauci da wutar Jahannama, ya bamu tsaro da kwanciya hankali da dukiya mai albarka da kuma Aljannah fiddausiiii... Ameen

Huɗubar mu na yau kenan... Duk wanda yayi taurin kai Allah Ya sa wayar sa ta yi shutdown alhali tana da chaji 98%.

09/09/2025

Shawara ce 🤫🤫

Want your school to be the top-listed School/college in Yola?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Bye Pass Yola
Yola
22