09/05/2026
ƙarfin addu'ar waliyin ALLAH
Addu’ar waliyin Allah tana kawo rahama, tana kare masifa, tana kuma haskaka zukata.
Idan waliyyin Allah ya ɗaga hannu ya yi addu’a, sai al’umma ta amfana da sauyin alheri.
Ƙarfin addu’ar waliyin Allah tamkar haske ne da yake korar duhu daga rayuwar muminai.
tambayata waliyin Allah ya taɓa yimaka/ki addu'a
09/05/2026
Ko kun gane wanene nan,da wanda ke riqe da keken?
19/04/2026
Samar da tazkiya university abin godiyan Allah ne.
Muna alfahari da wannan namijin aiki prof ibrahim maqari
19/04/2026
Maulana prof kenan,ɗa ga Sheikh Ahmad Sa'id Maqari,jika ga Sheikh umarul Wali,Allahu Akbar,nasaba ta tsarkaka.
لم تزل في ضمائر الكون تختا رلك الأمهات والآباء
19/04/2026
Hotunan Maulana a wajen Matriculation ( Taron qaddamar da ɗalibai) na Tazkiyyah University Zaria.
Jami'ar Mata zallah da Maulana Prof Rta ya assasa.
19/04/2026
Hotunan Maulana a wajen Matriculation ( Taron qaddamar da ɗalibai) na Tazkiyyah University Zaria.
Jami'ar Mata zallah da Maulana Prof Rta ya assasa.
15/04/2026
Duk da an kawo masa kujera, sai ya zauna a ƙasa—lallai tawali’u ya kai matuƙa 🥰
Allah yaqara lafia maulana Prof. Ibrahim Maqari H
15/04/2026
Daga cikin makullan samun daukaka a rayuwa dakwai tawali'u,indai kana da kaskantar dakai to zakayi daukaka da farin jini,to akwai wannan sirrin tattare da maulana prof,kayi nazari kagani.
09/04/2026
AKWAI WANI SIRRI DA WASU BASU SANI BA!
Mama ta ta taɓa faɗi min,a duk inda naje baƙunta,kar insake in taɓa nuna tsana ga yaran gidan,duk yadda s**a kai ga ɓatamin rai,kar insake in ɗau hannu in bugi ɗaya daga cikin su,domin yana kawo baƙin jini, hasalima yadda ya kamata iringa yi shine,in dinga nuna masu soyayya,ta hanyar daukansu ina wasa dasu,kokuma siya masu kayan tsostso da sauransu,hakan ze faranta ma en gidan,kuma soyayya ze kara ƙulluwa tsakanin Ni da su.
Duk wani ɗabi'a me kyau,banga wanda maulana beda shi ba,sede muce Allah ya kare shi yakuma ƙara masa lapiya da ɗaukaka.
22/03/2026
Alhamdulillah Allah Ubangiji Ya karbi ibadunmu🙏
Ameen Don Nabiyul Rahamati