Abban Malam

Abban Malam Zaku rinƙa samun Labarai, Wazantarwa, Finafinai, Kwallon Kafa da Wakoki

Tsohon dan wasan Arsenal, Martin Keown, ya mayar da martani ga Peter Schmeichel bayan kalamansa kan hukuncin VAR a wasan...
11/05/2026

Tsohon dan wasan Arsenal, Martin Keown, ya mayar da martani ga Peter Schmeichel bayan kalamansa kan hukuncin VAR a wasan West Ham da Arsenal.

Schmeichel ya soki hukuncin da aka yanke na soke kwallon West Ham bayan an gano laifi kan mai tsaron ragar Arsenal, David Raya. Sai dai Keown ya ce hukuncin ya yi daidai, yana mai cewa tsohon mai tsaron ragar Manchester United na nuna son zuciya ne saboda Arsenal.

Keown ya kuma bayyana cewa da ace irin wannan abin ya faru da Schmeichel a lokacin yana wasa, da shi ma zai yi korafi a matsayin mai tsaron gida.

11/05/2026

Gwamnatin tarayyar Najeriya sake tabbatar da shekaru 16 a matsayin mafi karancin shekarun shiga manyan makarantu a kasar.

Idan ba a manta a watan Yulin 2025 ne gwamnati ta tsayar da shekaru 16 a matsayin mafi karancin shekarun shiga manyan makarantu a kasar, inda ta sauya matsayar da Tahir Mamman, tsohon ministan ilimi ya sanar a baya.

Ministan ilmi Dr Ma'aruf Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja, a wajen taron tsara manufofin manyan makarantu na shekarar 2026.

Ministan ilimi ya ce matakin na da nufin samar da daidaito da bai'wa kowa dama don ganin dalibai sun shiryawa fannin ilmi.

Ministan ya ce dukkan dalibin da ya cancanta za a iya daukarsa kai tsaye.

Ya yi gargadin cewa dukkan makarantar da a ka samu da karya tsarin a ka amince da shi za su iya fuskantar barazanar sanya takunkumi, da kuma janye lasisinta.

11/05/2026

🚨 𝐁𝐑𝐄𝐀𝐊𝐈𝐍𝐆: Kylian Mbappé is set to RETURN this week with Real Madrid, Marca report. 🔙✅

The player will try to be fit to play either Thursday vs Oviedo, or Sunday against Sevilla. ⏳

Congratulations to all NCE students nationwide on the approval and implementation of the Continuous Five (5)-Year NCE–De...
11/05/2026

Congratulations to all NCE students nationwide on the approval and implementation of the Continuous Five (5)-Year NCE–Degree Programme by the National Commission for Colleges of Education (NCCE).

According to the ministerial directives issued by the NCCE on 5th May, 2026, all Colleges of Education operating the Dual Mandate programme are to commence full implementation of the new structure from the 2026/2027 academic session. This new system provides a smooth academic pathway of 3 years for the Nigeria Certificate in Education (NCE) and an additional 2 years degree programme for eligible NCE graduates.

This means that students who successfully complete their NCE programme will now have the opportunity to proceed directly into the degree programme at 300 Level within the same academic structure, making the process easier, faster, and more coordinated.

The initiative is aimed at strengthening the value of the NCE qualification as the minimum teaching standard while also creating a seamless transition to Bachelor’s degree certification within Colleges of Education.

We sincerely appreciate the Federal Ministry of Education and the NCCE for this remarkable development which will greatly benefit students and the education sector nationwide.

Congratulations once again to all NCE students, aspirants, and stakeholders across Nigeria. Greater opportunities are ahead.

Mikel Arteta ya tabbatar cewa Bukayo Saka ba zai buga wasan da Arsenal za ta  fafata da Manchester City a ranar Lahadi b...
17/04/2026

Mikel Arteta ya tabbatar cewa Bukayo Saka ba zai buga wasan da Arsenal za ta fafata da Manchester City a ranar Lahadi ba.

Kocin Arsenal ya bayyana cewa yana da kwarin guiwa cewa Noni Madueke zai iya samun lafiya ya buga wasan. Dangane da Martin Ødegaard, Jurrien Timber da Riccardo Calafiori, Arteta ya ce wasu daga cikin ‘yan wasan na dab da komawa cikin sahun ‘yan wasannin kungiyar.

15/04/2026

An kori Nafi'u Gombe ne dalilin "yi wa jam'iyya zagon ƙasa", kamar yadda Faisal Kabiru ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar ya shaida wa BBC Hausa, wanda hakan ya jefa jam'iyyar cikin mawuyacin hali.

👇👇👇👇

15/04/2026

Gwamnatin tarayya ta cire zargin ɗaukar nauyin ta’addanci daga tuhume-tuhumen da ake yi wa Malami

Gwamnatin tarayya ta gyara tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, da ɗansa Abdulaziz, inda ta cire zargin da ya shafi tallafawa ta’addanci kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

A zaman kotu na ranar Laraba, lauyan Hukumar DSS, Akinlolu Kehinde, ya sanar da kotu cewa an yi wannan gyara, tare da neman a maye gurbin tsohuwar ƙarar da sabuwa. Sabuwar tuhumar ta ta’allaka ne kan mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Lauyan waɗanda ake ƙara, Shaibu Aruwa, ya tabbatar da cewa an ba su sabuwar takardar ƙarar, kuma ya amince a karanta musu. Bayan an karanta, Malami da ɗansa sun musanta dukkan tuhume-tuhumen.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince su ci gaba da kasancewa a kan belin da aka ba su tun ranar 27 ga Fabrairu.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranakun 26 ga Mayu da 15 ga Yuni domin ci gaba da shari’a.

A cikin sabuwar ƙarar, ana zargin an gano makamai da harsasai a gidan Malami da ke Birnin Kebbi.

Tun farko dai, DSS ta gurfanar da Malami da ɗansa a ranar 3 ga Fabrairu bisa tuhume-tuhume guda biyar da s**a haɗa da zargin tallafin ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba. A ranar 27 ga Fabrairu, kotu ta bada belinsu kan naira miliyan 200 kowannensu tare da sharuɗɗa.

14/04/2026

Kotun ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan shari'ar jam'iyyar ADC.

A duba comment section 👇👇👇👇👇

14/04/2026

Address

Ungogo Kano
Ungogo

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abban Malam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category