10/05/2024
Assalamu Alaikum
Kamar yadda mukayi alkawari na bayar da gurbin karatu na mutane (80) kyauta ga Magidanta Maza da Mata tun a ranar da mukayi Walimar yaranmu data gabata.
A halin yanzu zamu fara da daukar Magidanta Maza mutum (20) da kuma Matan Aure mutum (20) don koyar dasu Al-qur'ani Mai Girma, tun daga matakin koyon baki, Rubutu da karatu, da kuma Haddacewa.
Tsarin Karatun Maza zai kasance a ranakun Asabar da Lahadi na kowanne mako, da misalin 08:00 zuwa 10:00 na dare.
Tsarin Karatun Mata zai kasance a ranakun *Litinin, Talata da Laraba, da misalin 09:30 zuwa 11:30 na safe.
Zamu tantance masu sha'awar shiga a ranakun Asabar da Lahadi masu zuwa da iznin Allah.
Karatun kyautane, har tsahon lokacin da mutum zai kammala, amma za'a biya kudin Application Form, Bude File, da kuma ID card.
Ku hanzarto domin tan-tanceku a ranar Asabar ko Lahadi idan Allah ya kaimu.
Bissalam,
Hukumar Makaranta.