03/09/2026
YANA KWANA A ƘARƘASHIN GADA, YANA DA NAUYI 42 KAWAI, AMMA YA SAMU SABUWAR RAYUWA!
A lokacin da Danny Ellerd yake cikin mawuyacin hali na rayuwarsa, yana kwana a ƙarƙashin gada, kuma nauyinsa ya kai kusan kilogiram 42 kacal.
Ya shafe kusan shekaru 15 yana fama da jarabar ƙwayoyi, kuma lafiyarsa tana ƙara lalacewa a hankali. 😢
Sai a watan Agusta 2019, aka je domin duba halin da yake ciki.
Jami’an da s**a same shi sun fahimci cewa Danny yana cikin mummunan yanayin lafiya, maimakon su wuce su bar shi, sai s**a garzaya da shi asibiti. Wannan taimakon ya ba shi damar samun damar rayuwa ta biyu da yake matuƙar buƙata.
Bayan ya tsallake wannan mawuyacin yanayin, Danny ya shiga rehabilitation domin ya daina amfani da ƙwayoyi. Ya kuma kammala shirin kotun da aka tsara domin taimaka wa masu fama da jarabar ƙwayoyi, sannan ya fara aiki tuƙuru wajen gina lafiyarsa da rayuwarsa daga farko,Amma abin da ya faru daga baya ya fi ban mamaki.
Danny bai tsaya kawai da samun sauƙi ba.
Ya samu digirin jami'a, sannan ya fara aiki a matsayin ƙwararren mai fafutukar wayar da kan jama'a game da lafiyar kwakwalwa da farfadowa daga jarabar ƙwayoyi.
Yau, yana amfani da labarin rayuwarsa domin taimaka wa wasu mutanen da suke cikin duhu, yana nuna musu cewa: Ko da mutum ya faɗi ƙasa sosai, har yanzu akwai damar tashi.
Rayuwarsa ta sauya daga kwana a ƙarƙashin gada zuwa samun ilimi da taimaka wa wasu.
Wataƙila mutumin da kake ganin ya lalace gaba ɗaya a yau, yana da damar zama abin koyi ga wasu gobe.
Idan za ku ba mutumin da yake cikin mawuyacin hali kalma ɗaya ta ƙarfafa gwiwa, wace kalma ce za ku ce masa?
-Mamman Modukur