23/07/2026
Ma sha Allah
A madadin hukumar gudanarwa l, da malaman Makka International Academy muna taya sabon Dallatun Sokoto Alhaji Murtala Abdulƙadir Ɗan Iya murna bisa wannan naɗi da mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi masa. Babu shakka ya cancanta. Mutum ne mai hidima da jama'a kuma mai taimakon addini.
Allah ya sa da yawancin rai mai amfani.
✍️ Prof. Mansur Sokoto, mni
Hadimin Makaranta