Fiqhun Madina

Fiqhun Madina Sharing Islamic knowledge and educational updates daily

02/06/2026

AIKIN MUTANEN MADINA YANA FASSARA SUNNAR MANZON ALLAH NE, BA WAI YANA RUSA TA BA.

02/06/2026

MALIKIYYA SUNA ƊAUKAR AIKIN MUTANEN MADINA A MATSAYIN HUJJA NE; SABODA KASANCEWARSU MAFI KUSA DA RAYUWAR MANZON ALLAH SALLALLAHU ALIHI WA SALLAM.

01/06/2026
26/05/2026

RANAR ARFA DA MUHIMMANCINTA

Ma’anar Ranar Arfa
Ranar Arfa ita ce ranar tara ga watan Zul-Hijja, ranar da mahajjata suke tsayuwa a filin Dutsen Arafat domin gudanar da babban rukuni na aikin Hajji. Wannan rana tana daga cikin ranaku mafiya alfarma a Musulunci.

Muhimmancin Ranar Arfa
1. Rana mafi girman falala
Annabi ﷺ ya bayyana cewa babu ranar da Allah yake yawan ‘yanta bayinsa daga wuta k**ar ranar Arfa.
Daga Sahih Muslim, Annabi ﷺ ya ce:
“Babu wata rana da Allah yake ‘yanta bayi daga wuta k**ar ranar Arfa.”
2. Ranar cikar addini
A wannan rana ne Allah Ya saukar da ayar:
“A yau Na cika muku addininku…”
(Suratul Ma’ida: 3)
Wannan yana nuna girman ranar da daukakarta.
3. Muhimmin rukuni na Hajji
Annabi ﷺ ya ce:
“Hajji shi ne Arfa.”
Wato tsayuwar Arfa ita ce ginshikin Hajji mafi girma. Duk wanda bai samu tsayuwar Arfa ba, Hajjin sa bai cika ba.

Ayyukan da ake so a yi a Ranar Arfa
1. Yin Azumi ga wanda ba ya Hajji
Yin azumin ranar Arfa yana da falala mai yawa.
Annabi ﷺ ya ce:
“Ina fatan Allah Ya kankare zunuban shekara ta baya da ta gaba saboda azumin ranar Arfa.”
2. Yawaita addu’a
Ranar Arfa tana daga cikin lokutan da addu’a take fi karɓuwa.
Annabi ﷺ ya ce:
“Mafi alherin addu’a ita ce addu’ar ranar Arfa.”
3. Yawaita zikiri da istigfari
Ana son musulmi ya:
yawaita ambaton Allah,
yin tasbihi,
tahmidi,
tahlili,
da neman gafara.
Misali:
Subhanallah
Alhamdulillah
La ilaha illallah
Allahu Akbar
Astaghfirullah
Hikimomin Ranar Arfa
Tana tunatar da ranar Alkiyama da taruwar mutane.
Tana koyar da tawali’u da daidaito tsakanin musulmi.
Tana ƙarfafa tuba da komawa ga Allah.
Abubuwan da ya k**ata musulmi ya kula da su
Nisantar zunubi da rigima.
Yin salloli akan lokaci.
Yawaita karatun Alƙur’ani.
Yin addu’a ga iyaye, malamai, da al’ummar Musulmi.
Kammalawa
Ranar Arfa wata babbar ni’ima ce daga Allah. Ya k**ata musulmi ya yi anfani da ita wajen:
tuba,
ibada,
azumi,
zikiri,
da addu’a.
Allah Ya sa mu dace da cin moriyar falalar Ranar Arfa, Ya gafarta mana zunubanmu baki ɗaya. Amin.

21/05/2026

BAYANIN HUKUNCIN LAYYA A AIKACE

Abdullahi Bin Abbas (R.A), ya taɓa aika ɗalibinsa Ikrima, domin ya saya masa nama ranar babbar Sallah. Sai Ikrima ya ce masa: "Kamarka a irin wannan rana, a ce ba za kayi layya ba"!?

Sai Abdullahi Bin Abbas ya ce da shi: "Idan wani ya haɗu da kai, ka ce da shi wannan - daman ka sayi - ita ce layyar Abdullahi Bin Abbas"!

ABIN LURA:

1.Anan, Abdullahi Bin Abbas ya bayyana hukuncin layya aikace; cewa ba wajibi ba ce, wajabcin Farillah.

2. Kuma kada wani yayi anfani da girmansa acikin al'umma, ya ɗora musu nauyin da shi kanshi bai wajaba ba a kanshi ballantana su.

14/05/2026

YIN FATAWA KO BADA LABARIN FATAWA!?

Da yawa daga cikin masu ƙoƙarin amsa tambayoyin fiƙhu suna faɗawa cikin kuskure, a lokacin da mai tambaya yake tambayarsu akan wata matsalar fiƙhu;

A maimakon su bashi amsar tambayarsa kai tsaye, sai kawai su bige da hakaito saɓanin malamai akan wannan matsala!

Shi mai tambaya tamkar marar lafiya ne, a yayinda shi kuma Malami yake a matsayin Likita; alaƙar dake tsakaninsu kawai, ita ce ta bayanin matsalar mai tambaya, da kuma bayarda amsa daga mai fatawa.

Ba daidai ba ne, ka cika shi da ambaton saɓanin malamai game da wannan matsalar; domin yin hakan ba abinda zai ƙara masa banda ruɗani a cikin sha'aninsa.

Bayarda fatawa a bisa mazhabar yankin da mai tambaya yake ciki, yana daga abinda zai warware matsalar mai tambaya cikin ruwa sanyi.

Ku bamu misalin wani ruɗu da kuka taɓa shiga sak**akon irin wannan salon da bada fatawa?

13/05/2026

Wasu Maudu’ai Masu Alaƙa da Fiqhun Mutanen Madina

1. Ahlul Madina Su Waye?

“Ahlul Madina” su ne malamai, Sahabbai, Tabi’ai, da mutanen kirki na birnin Medina waɗanda s**a rayu a zamanin farko na Musulunci. Su ne s**a riƙe ilimin Annabi ﷺ da aikace-aikacen addini kai tsaye.
A wajen Imam Malik ibn Anas, haɗuwar malamai da mutanen Madina a kan wani aiki tana da ƙarfi sosai a matsayin hujja.

2. Ma’anar “Amalu Ahlil Madina”

“Amalu Ahlil Madina” na nufin:
Ayyuka da dabi’un addini da mutanen Madina s**a ci gaba da yi tun daga zamanin Annabi ﷺ ba tare da yankewa ba.
Misalai:
Yadda ake kiran sallah
Yadda ake gudanar da sallah
Mu’amalolin kasuwanci
Hanyoyin ibada
Wannan aiki yana k**a da riwaya mai rai, domin mutane suna gadar shi daga malamai zuwa almajirai.

13/05/2026

LITTATTAFAN DA S**A DA KUMA WURAREN YAƊUWAR MAZHABAR MALIKIYYA:

1. Littattafan da s**a shahara
Daga cikin littattafan da s**a yi fice a wannan fanni akwai:
Al-Muwatta
Al-Mudawwana
Ar-Risala ta Ibn Abi Zaid
Bidayatul Mujtahid

2. Tasirin Mazhabar Malikiyya
Mazhabar Malikiyya ta bazu sosai a:
Arewacin Afirka
Yammacin Afirka
Najeriya
Mauritania
Mali
A yau mafi yawan malamai a yankin Hausa suna amfani da fikihun Malikiyya.

Address

Gada Junction, Illela
Sokoto

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fiqhun Madina posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category