20/05/2026
🧪 Topic: Hydrocarbons (Alkanes, Alkenes and Alkynes)
Hydrocarbons su ne sinadarai da s**a ƙunshi Carbon (C) da Hydrogen (H) kawai. Su ne ginshikin dukkanin Organic Chemistry.
🔹 Nau’ikan Hydrocarbons:
1. Alkanes
* Sun ƙunshi single bond (C–C)
* Misali: Methane (CH₄), Ethane (C₂H₆)
* Su ne “saturated hydrocarbons”
2. Alkenes
* Sun ƙunshi double bond (C=C)
* Misali: Ethene (C₂H₄)
* Su ne “unsaturated hydrocarbons”
3. Alkynes
* Sun ƙunshi triple bond (C≡C)
* Misali: Ethyne (C₂H₂)
🔥 Muhimmanci:
* Ana amfani da su wajen samar da fuel (gas, petrol)
* Suna shiga cikin masana’antar roba da plastic
* Su ne asalin sinadarai da yawa a rayuwa
Hydrocarbons su ne tushen dukkan Organic Chemistry 🔬💡 Ka fahimce su domin gina strong foundation a Chemistry. Alkanes, Alkenes & Alkynes — kowa yana da muhimmanci!
20/05/2026
POST NA GABA – PROCESS SCIENCE 🧪
Menene Heat Exchanger? 🔥❄️
Heat Exchanger wata na’ura ce da ake amfani da ita wajen canja zafi daga wani fluid zuwa wani ba tare da sun gauraya ba.
📌 Ana samun sa a:
✅ Masana’antar abinci
✅ Oil refinery
✅ Air conditioner
✅ Power plants
Yadda yake aiki:
➡️ Fluid mai zafi yana bayar da zafinsa
➡️ Fluid mai sanyi yana karɓar zafin
📚 Darasi:
Heat Exchanger na taimakawa wajen rage asarar energy da kuma inganta aikin masana’antu.
20/05/2026
Thanks for being a top engager and making it onto my weekly engagement list! 🎉
Hauwau Aliyu, Ballkisu Umar, Amina Jibrin
20/05/2026
🧪 Topic: Me yasa apple yake canza launi bayan an yanke shi? 🍎
Idan ka yanke apple ka barshi na ɗan lokaci, zaka ga ya fara zama ruwan kasa. Wannan yana faruwa ne saboda wani process da ake kira oxidation.
📌 Lokacin da cikin apple ya haɗu da iska, wani enzyme a ciki yana reacting da oxygen, sai launin ya canza.
💡 Hanya mafi sauƙi da za’a hana hakan:
➡️ A shafa lemon tsami kaɗan a saman apple ɗin. Acid ɗin lemon yana rage oxidation.
🎓 Wannan yana nuna yadda chemistry take faruwa a rayuwarmu ta yau da kullum!
18/05/2026
Topic: Dalilin Da Yasa Karfe Ke Faɗaɗa Idan Yayi Zafi? 🔥🔩
Shin ka taɓa lura cewa wayoyin wuta ko ƙarfe suna ɗan tsawo idan rana tayi zafi? 🤔
A Chemistry da Physics, idan ƙarfe ya samu zafi, ƙwayoyin cikinsa suna fara motsi da sauri. Wannan motsin yana sa ƙarfen ya ɗan faɗaɗa (expand).
Amma idan yayi sanyi, ƙwayoyin suna rage motsi kuma ƙarfen yana komawa ya taƙaita (contract). ❄️
👉 Wannan ne yasa ake barin ɗan sarari a gada ko layin dogo domin kada su karye lokacin zafi.
📚 Chemistry Hausa Hub
Ilimi cikin sauƙi da misalai na rayuwa 😊
18/05/2026
🧪 TA YAYA DIAMOND DA GRAPHITE SUKE DAGA CARBON ƊAYA?
Abu mai ban mamaki shine, diamond da graphite dukansu daga element ɗaya suke — wato carbon. Amma yadda atoms ɗinsu suke haɗuwa ne yasa s**a bambanta sosai.
💎 Diamond:
• Atoms ɗin carbon sun haɗu sosai cikin ƙarfi
• Yana da matuƙar tauri
• Ba ya wuce wuta ko lantarki sosai
✏️ Graphite:
• Atoms ɗin carbon suna layi-layi ne masu sauƙin zamewa
• Yana da laushi (ana amfani da shi a pencil)
• Yana wuce lantarki sosai
📌 Wannan yana nuna cewa yadda atoms suke jere na iya canja halayen abu gaba ɗaya.
💡 Shin ka sani?
Diamond shine ɗaya daga cikin abubuwa mafi tauri a duniya, amma graphite yana da laushi sosai duk da dukansu carbon ne!
16/05/2026
🧪 Me Yasa Cold Drink Ke Yin Kumfa Idan An Bude? 🥤
A cikin soft drinks akwai wani gas mai suna Carbon dioxide (CO₂).
📌 Ana matse wannan gas ɗin cikin drink ɗin da pressure mai ƙarfi.
Lokacin da aka bude kwalban:
➡️ Pressure ɗin yana raguwa
➡️ Gas ɗin sai ya fara fita waje
➡️ Sai kaga kumfa da ƙara “fissss” 😄
💡 Idan aka jijjiga drink kafin a bude, gas ɗin zai ƙara fitowa da ƙarfi sosai.
📚 Wannan duk chemistry ce ta gases da pressure!
16/05/2026
🧪 Me Yasa Ake Saka Gishiri Akan Kankara?
A wasu ƙasashe masu sanyi, ana saka gishiri (salt) akan kankara dake hanya domin ta narke da sauri. ❄️➡️💧
📌 Dalili kuwa shine:
Gishiri yana rage temperature ɗin da ruwa ke daskarewa (freezing point).
Saboda haka kankarar zata fara narkewa ko da har yanzu yanayin sanyi ne.
👉 Wannan shine dalilin da yasa hanyoyi basa yawan yin slippery sosai bayan an zuba gishiri.
📚 Wannan concept ɗin a chemistry ana kiransa:
“Freezing Point Depression.”
💡 Chemistry tana bayyana abubuwan da muke gani a rayuwar yau da kullum!
15/05/2026
CHEMISTRY HAUSA HUB 🧪
⚡ Menene Catalyst a Chemistry?
Catalyst wani sinadari ne da yake saurin faruwar reaction ba tare da shi kansa ya ƙare ba.
📌 Misali:
A masana’antu ana amfani da Iron a matsayin catalyst wajen samar da ammonia.
🧠 A sauƙaƙe:
Catalyst kamar mutum ne da yake taimakawa mutane suyi aiki cikin sauri amma shi bai gaji ba 😄
🔥 Abubuwan da catalyst yake yi:
• Yana rage lokacin reaction
• Yana taimakawa ajiye kuzari
• Ana amfani da shi sosai a industries
💡 Tambaya:
Shin catalyst yana ƙarewa bayan reaction? 👀
15/05/2026
⚛️ Menene Isotopes?
Isotopes su ne atoms na element guda ɗaya amma suna da:
✅ Yawan protons iri ɗaya
❌ Yawan neutrons daban
Saboda haka weight ɗinsu yana bambanta.
Misali:
Carbon yana da isotopes kamar:
* Carbon-12
* Carbon-14
Duk carbon ne, amma neutrons ɗinsu sun bambanta.
Amfanin Isotopes:
🩺 A asibiti — wajen gano wasu cututtuka
⚡ A masana’antu
📚 A binciken shekaru na tsofaffin abubuwa (carbon dating)
📌 Isotopes suna da matuƙar amfani a science da rayuwar yau da kullum.
📚 Chemistry Hausa Hub
Sauƙaƙen Chemistry cikin Hausa 🔥
15/05/2026
⚗️ CHEMISTRY HAUSA HUB ⚗️
🧪 Shin Ka San?
Idan aka bar ƙarfen iron a waje yana haɗuwa da oxygen da ruwa, sai ya fara yin rust (tsatsa). Wannan reaction ɗin ana kiransa:
🔥 Oxidation Reaction
📌 Wannan shine dalilin da yasa motoci ko ƙofofin ƙarfe suke tsatsa idan suna yawan haɗuwa da ruwa.
✅ Yadda ake rage tsatsa:
• Yin fenti
• Shafa mai
• Ajiye ƙarfe a busasshen wuri
💡 Chemistry tana rayuwarmu kullum!