24/09/2025
SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU ZAI JAGORANCI TARON KUNGIYOYIN AHLUS SUNNAH NA NAJERIYA A YANKIN KUDU MASO YAMMA
Daga Sani Umar Maiyara
Shugaban JIBWIS na kudu maso Yamma (Southwest Zone) a tarayyar Najeriya Alh Salisu Abdullahi Umar na Farin cikin gayyatar Al’umar Musulmin Nigeria Musamman mazauna Kudancin kasar gagarumin taro (Conference) Wanda aka shirya a karkashin Kungiyoyin Ahlus Sunnah (FASON) a Garin Ibadan.
Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau Zai Jagoranci taron Kuma daya daga cikin masu gabatar da Kasidu a taron tareda wasu mashahuran Malamai daga Yankin na Yarbawa.
MALAMAI MASU GABATARDA TAKARDU
*Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau
*Shk. (Dr.) Abdul Mojeed Imran Eleha
*Prof. Ishaq Lakin Akintola
*Dr. Idris Sekoni
*Dr. Musharaf Aderogba
*Shk. Isa Akindele Solahudeen
*Prof. AbfulGaniy Raji
*Shk. Masud Ibrahim (Offa)
*Shk. Dr Dhikrullah Shafli
*Dr. Tawadhul Adeoye
*Shk. Mukadam Hussein
*Shk. AbdulFatah Thani
*Dr. Abdul Haadi Thiamiyy
MAI MASAUKIN BAKI:
Sheikh Tajudeen Abdul Kareem Al Adabiyy (Baba Lagbeni)
Allah ya bada ikon halarta, Amin
Jibwis Nigeria