20/01/2024
KIRA GA MALAMMAN FURAMARE NA MA’AIKATAR HUKUMAR ILIMI TA ISA LGEA…
Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace “DUKKANIN KU MAKIYAYANE ZA’A TAMBAYE KU ABUNDA AKA BAKU KIYO A GOBE QIYAMA” Dayawan mutane suna yiwa wannan hadisin gurguwar dauka, wasu tunanin su kawai akan iyalin mutum ne, wasu kuma sun fahimce shi akan jagoranchi, koma dai ya muka doke shi mu sani Allah zai tambaye mu din ko shakka babu.
Cikin kashi 70 cikin 100 nadaga malamman furamare na ma’aikatar hukumar ilimi ta Isa, basu wuraren ayukkansu a halinda ake ciki yanzu, wannan abune karara ga hilin Allah!
Wasu suna unguwa (Chirani), wasu kuma suna cikin gari zanninsu dangal-gal! ba tareda sunje wuraren ayukkansu ba, dalillansu wai sunyi siyasar jam’iyyar Apc kuma tachi, yayinda wasu kuma ke ikirarin ai har yanzu kotu ake ba’ayanke shari’a ba b***e asan matsayin kowa.
Duk kuma wannan, rashin sanin darajjar ilimine da rashin kishin kasa tareda karanchin jin tsoron Allah!
A takaiche, matsayina na wakili ga dukkanin ma’aikatan (Malamman) hukumar ilimi ta karamar hukumar mulkin Isa, danku, kanenku, wasu kuma yayansu, ina kira ga wadanda s**a bar gari da niyar kasuwanchi ko neman kudi, kai harma da wadanda ke zaune gida ba tareda komawa wuraren ayukkansu ba, cewa dan Allah! da darajjar Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam, kowa yadawo wurin aikinsa dan tabbatar da ingancin ilimin yaran mu.
Ta fannin sha’anin samarda wal-wala ko jin dadin malammai, ba karya ba ko dadin baki, wannan gwamnati mai albarka, karkashin jagorancin mai girma gwamna Dr. Ahmad Aliyu Sokoto Fcna, insha Allahu zata farfado da darajjar ilimi da malammai a fadin jahar nan.
A yanzu haka, nan da ‘yan satukka kalilan, kowane asusun ajiya na malammai sai yaji kudaden da yaiyi shekaru bai ji su ba da yardar Allah! Haka zalika kuma, duk malaminda yaiyi karatun gaba ga sakandire sai ya amfanu da karatunsa matukar ya nemi takarardar karin girma (Promotion) koda kuwa yana rike da ta karshe ne.
Zamu kula tareda dokar matakin tsarin dokar aiki ga duk wanda yasso yiwa malami ba dai-dai ba (Chin hakkinsa) ko wanene insha Allahu! Haka zalika kuma ba zamu lamunchi duk malamin da zaiyi wasa da aikinsa ba ko wanene da yardar Allah!
Allah ta’ala yakara daukaka darajjar malami kuma yacilastawa mai girma gwamna akan gaggauta maida hankali kan malammai amin.
JIYA BA YAU BA………
Naku!
Comrd Isma'ila Abubakar Isa
NUT Chairman, Isa Branch.
Secretary, 23 Local Government NUT Chairmen Forum, Sokoto State.
20th January 2024