TAFAR KIN TSIRA

TAFAR KIN TSIRA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from TAFAR KIN TSIRA, Religious school, Madinatul Qur, an, Rijiyar Zaki.

26/06/2023

WANI MAI HIDIMA DA UBANGIDANSA.

Wani mutum mashayin giya yatara abokanansa don su hadu susha giya, sai ya aika mai hidimansa da dirhami hudu don yasiya musu ya'yan 'itatuwa.

Lokacin damai hidiman nasa yatafi kan hanya, sai yahadu da wani mai gudun duniya wanda ake kira Almansur bn Ammar yana cewa, waye zai bada dirhami hudu ga faqiri bako nikuma inyi masa addu'a hudu? Sai wannan yaro mai hidima yabashi dirhaminnan hudu da aka aikeshi saboda wannan addu'a.

Sai mansur bn ammar yace me kake so inyi maka addu'a akanshi? Sai yaron yace a 'yantani daga bauta, 2 Allah ya maye min dirhaminnan hudu, 3 shugabana yatuba daga shan giya, 4 Allah ya gafarta min da shugabana da kai da mutanen dasuke nan, sai kuwa mansur bn Muhammad ya roka masa.

Sai yaro yadawo wurin shugabansa, sai shugabana ya tambaye shi meyasa kayi jinkiri? Kuma 'ina yayan 'itatuwan? Sai yabashi labarin haduwarsa da mansur mai gudun duniya, da yadda yabashi dirhami hudu a madadin addu'a hudu. Sai shugaban yace kaikuwa wace addu'a ka bukaci yayi maka?

Sai yace farko dai naroka wa kaina yanci daga bauta. Sai shugaban yace kaje na yantaka saboda Allah madaukaki.

Sai yace na biyu, Allah ya maye min dirhami hudun, sai shugabana yace kana da dinari dubu hudu.

Sai shugaban yace wace addu'a kanema ta uku? Sai yaron yace Allah yasa katuba daga shan giya, sai shugaban ya girgiza kansa yayi kuka sannan ya fasa tukunyar giyar yace nadaina shan giya har abada.

Sai yace wace addu'a kanema ta hudu? Sai yaron yace, nace aroka Allah ya gafarta min dani dakai da mansur bn Muhammad da mutane dasuke wurin baki daya. Sai yace wannan bani da 'iko wannan hurumi ne na Allah madaukakin sarki.

Lokacin da shugaban ya kwanta bacci wannan dare sai yayi mafarki ana cemasa, kai kayi abinda zaka 'iya, kana tsammani Allah bazaiyi abinda shi kadai dinne ke iya yiba!? To haqiqa Allah ya gafarta maka dakai da yaron da mansur bn Muhammad da wadanda suke wurin.

Addu'a ibada CE, yin addu'a ga dan'uwanka musulmi ba tareda saninsa ba t

Address

Madinatul Qur, An
Rijiyar Zaki

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TAFAR KIN TSIRA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share