16/06/2026
Mu Tuna Da Jaruman Mu Na Arewa...
Yau shekaru tara (9) kenan da shahadar marigayi Yakubu Muhammad Fannami, matashin ɗalibin da ya sadaukar da ransa domin ceton rayukan bayin Allah da dama a Maiduguri, Jihar Borno.
A ranar 25 ga Janairu, 2017, Yakubu Muhammad Fannami, ɗalibin ajin SS1 a makarantar Darussalam Science and Islamic Academy, mai shekaru 19 a duniya, ya nuna jarumta irin wadda ba kasafai ake samu ba. A lokacin da masu ibada ke tsaka da gudanar da Sallar Asuba a wani masallaci da ke unguwar Kaleri, ya hango wata yar kunar bakin wake da ke ƙoƙarin shiga cikin masallacin.
Cikin gaggawa da ƙarfin hali, Yakubu ya tunkare ta domin hana ta isa cikin taron jama'a. Nan take bam ɗin da ke jikinta ya fashe, inda shi da ita s**a rasa rayukansu. Sai dai ana kyautata zaton cewa wannan sadaukarwa tasa ta ceci rayukan masu ibada da dama da ke cikin masallacin a lokacin.
Tun daga lokacin, ana ci gaba da tunawa da Yakubu Muhammad Fannami a matsayin ɗaya daga cikin jaruman da s**a sadaukar da rayuwarsu domin kare al'umma. Kowace shekara, mutane da dama na tunawa da shi a shafukan sada zumunta, ciki har da fitattun mutane kamar tsohon Sanata Shehu Sani, wanda ya taɓa bayyana shi a matsayin "Jarumin da ba a san shi ba."
Allah Ya jiƙan Yakubu Muhammad Fannami, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannar Firdausi ce makomarsa. Amin.