14/12/2021
Alhamdulillah
Abin gwanin sha'awa yadda tallafin raya Ilime yake gudana a cikin Jihar Yobe, gaskiya abin sai son barka.
Wannan tsari da mai girma gwamnan Yobe Hon.Alha Mai Mala Buni ya assasa shi yakara kawo hadin kai, kaunar juna tare da cigaba mai albarka
Sadaukar da Naira miliyan biyar (5,000,000) da mukayi a karamar hukumar potiskum dan raya Ilime na daga cikin babban riba, abin Farin ciki domin tallafawa Ilime, tamkar raya abinda ya mace ne, tsaro da aminci na kara dauwama ne awaje matukar anabawa Ilime mahimmanci da tallafin da ya dace.
Karamar hukumar Fika sun nunawa duniya kan su a hade yake, kasancewar yadda aka gudanar da gidauniyar tallafawa Ilime cikin tsari da mutuntata juna, munyi Farin ciki tare da godiya ga Allah S.W.T yadda yabamu damar sa hanun jarin Naira miliyan daya (1,000,000) sabida Ilime da cigaba yayan Mu na karamar hukumar Fika
Allah Ya bawa yaran Mu Ilime mai albarka tare da amfanar da al'umma, Allah Ya albarkaci Yobe da Najeriya bakidaya.
Allah Ya kara mana zaman lafiya, Allah Ya karawa shugabannin Mu basira tare da sauke nauyin da ke Kansu.
Ma Sha Allah.