26/08/2026
KANEMI TSARI DAGA MUTANE BIYU:
Sufyan al-Thawri, Allah ya yi masa rahama, ya ce: "Ku nemi tsari daga Allah daga fitinar jahili mai bauta, da kuma fitinar malami fajiri, domin jarabawarsu jarabawa ce ga mafi yawan mutane."
Ma'anar wannan magana: Ku nemi tsari daga Allah daga fitinar jahilin da yake bauta da yawa amma bai san hukunce-hukuncen shari'ar Musulunci ba, kuma bai mallaki ilimin da zai gyara ibadarsa ba, ko hukunce hukuncen shari'a ba.
Domin mai bauta yana iya zama mai gaskiya kuma yana yin addu'o'i da yawa, azumi, da kuma sallar dare, sannan yana iya:
-Haramta abin da Allah ya halatta.
-Ko halatta abin da Allah ya haramta.
-Ko ya yi tsauri ga mutane game da al'amuran da shari'ar Musulunci ta saukaka.
-Ko ya musanta al'amuran da suke ingantattu a shar’ance saboda jahilcinsa.
-Yana kiran mutane zuwa ga bauta ko imani na ƙarya, a tunanisa yana yin abu me kyau ne.
Saboda haka, haɗarinsa yana da yawa, domin mutane zasu iya ruɗuwa da yawan ibadarsa, suna gaskata duk abin da ya faɗa .
amma jarabawar Fajirin malami: yana nufin: Nemi tsari ga Allah daga malamin da ke da ilimi amma ba ya aiki da shi, ko kuma yana amfani da shi don cimma burin duniya wato samun abin hannun mutane.
Sannan Mugun malami ya fi jahili haɗari a wani ɓangaren, domin ya san gaskiya amma yana iya barin ta saboda, kwadayi, tsoro, ko neman matsayi da girma.
Yana iya ƙawata ƙarya ga mutane, ya yi shiru game da gaskiya, ko kuma ya yi amfani da rubuce-rubucen addini don biyan buƙatunsa.
Allah ya kare mu d ruɗuwa daga waɗannan.
Muhammad Baba Nguru Ph.D