Jamilu Ibrahim Mukhtar

Jamilu Ibrahim Mukhtar Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Jamilu Ibrahim Mukhtar, Tutor/Teacher, Nguru.

Congratulations
15/01/2026

Congratulations

ABILITY IN DISABILITY: A Call for Support for a Disabled Child Who Wants to Study Nursing.Bashir, who lost his legs due ...
04/11/2025

ABILITY IN DISABILITY: A Call for Support for a Disabled Child Who Wants to Study Nursing.

Bashir, who lost his legs due to polio, never lost hope of actualizing his dreams. He used to sell MTN and Airtel data to earn a living and never considered begging as a source of income.

If you recall, some weeks ago I posted his UTME (Jamb) result, in which he scored over 200+. He applied to the College of Nursing Sciences, FMC N'guru, to study nursing and he got an admission.

On behalf of his family, I am writing this piece to solicit support from philanthropists, individuals, or the government to aid him in pursuing his dream. I believe Bashir will become a role model for other disabled children who have lost hope. Education is a right, not a privilege.

You can contact him directly via this number: 07035255638 for more details.

JazakumulLahu Khairah

05/10/2024

Thanks to my TEACHERS

12/06/2023

HARAMUN NE MIJI YA MARI MATARSA:
Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

1. Haramun ne har abada namiji ya daga hannu ya mari matarsa, ko ya bude baki ya zage ta, musamman ma ya ce da ita: mummuna!

2. Abu Dawud da Ibnu Majah da Ahmad sun ruwaito hadithi sahihi daga Sahabi Mu’awiyah Bin Haidah Allah Ya kara masa yarda, cewa ya tambayi Manzon Allah mai tsira da amincin Allah hakkin matar mutum a kansa, sai Manzon Allah ya ce: ((Ka ciyar da ita idan ka ci, ka suturtar da ita idan ka yi sutura, kada ka bugi fiska, kada ka munana (kada ka yi zagi), kada ka kaurace sai a cikin daki)).

3. Haka nan Imamu Muslim ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Sahabi Jabir Bin Abdilla Allah Ya kara masa yarda ya ce: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya hana duka a fiska)).
((يا رسول الله، ما حَقُّ زوجة أحَدِنَا عليه؟، قال: «أن تُطْعِمَهَا إذا طَعِمْتَ، وَتَكْسُوَهَا إِذَا اكْتَسَيْتَ، ولا تضرب الوجه، ولا تُقَبِّحْ، ولا تَهْجُرْ إلا في البيت)). ((نهى رسول اللَّهِ صلى الله عليه وسلم عن الضَّرْبِ في الْوَجْهِ)).

4. Wajibi ne maza su kula. Allah Ya kare mu daga sharrin Shaidan. Ameen.

24/05/2023

ƘUDA A CIKIN MUTANE...

Wasu mutanen kamar Ƙuda suke,
Wajen da zaƙi yake su ma nan suke,
Wajen da ƙazanta take shi ma nan suke.

Wani loton zaƙi ya kan zama ƙazanta, shi yasa zai yi wahala ka kalli Ƙuda a waje mai tsafta; lokuta da dama ya kan laɓe a gafe da zarar an yi tsartuwa da dauɗa caraf sai ka ga ya dira wajen-yadda ka san wahayi aka yi masa.

Babban abin takaici, ba ya iya amfanar da mahalli da komai, idan ya dira jikinka ko ya tsaya samanka sai ya ɓata maka fararen tufafi da ƙazantarsa-bayan ya ribace ka!

Idan ya ji ƙamshi irin na dahuwa ba turare ba, duk nisa sai ya nemi kusanci don kar a sha lagwada ban da shi.

Da zarar an kammala sharholiya sai ya tafi ya bar ku da kwalara. Assha!

Shin kuna fama da Ƙuda a cikin rayuwarku?

Shin ko ana iya rabuwa da wannan Ƙudan?

Wace irin illa yake da ita gare ka?

Allah ya sa mu wanye lafiya, amin.

22/04/2023

AIYUKAN MU SUNA TASIRI A RAYUWAR ƳAƳAN MU

Naga da yawa daga bayin Allah da s**a yi kyakkyawar rayuwa ta ɗa'a ga Allah da yiwa addini hidima, Allah Ya basu zuriya masu albarka.

Naga ƙalilan da s**a yiwa addini hidima da ɗa'a ga Allah, wadanda wasu daga cikin ƴaƴan su s**a kauce hanya.

Naga da yawa daga cikin mutane da s**a kauce hanya ta hanyar saɓo, zaluntar bayin Allah da yiwa addini zagon ƙasa, wadanda da yawa daga cikin ƴaƴan su s**a biyo halayen su na ash-sha.

Naga ƙalilan daga cikin mutane da s**a kauce hanya ta hanyar saɓo, zaluntar bayin Allah da yiwa addini zagon ƙasa, amma ƙalilan daga cikin ƴaƴan su s**a zama mutanen ƙwarai.
Lissafin anan shine, idon ka samu kanka cikin masu addini, tsoron Allah da kyawawan halaye, toh akwai kyakkyawan zato cewa mafi yawancin ƴaƴan ka zasuyi albarka, Insha Allah.
Idon kuma ka samu kanka cikin masu saɓawa Allah da cutar da mutane, toh inba taimakon Allah ba, mafi yawancin ƴaƴan da wuya suyi albarka.

20/04/2023

“Gobe ɗaya ga watan Shawwal a Najeriya...”
~NMSC

20/04/2023

Ya ƴan uwa Musulmi kada mu yi saiɓin jiki wajen aikata ayyukan alkhairi, sannan kada mu gajiya wajen roƙon Allah kan ya amsa mana ibadunmu, don kuwa asara mafi muni ita ce mutum ya yi ibada yana tsammanin an karɓa amma ba a karɓa. Allah ya kiyaye, amin.

Ubangiji Allah Ya karɓi ibadunmu Ya gafarta zunubanmu, amin.
Ubangiji Allah Ya gafarta mana

17/04/2023

Allahummah InnaKa 'Afuwwun Tuhibbul 'Afwa Fa'afu Annee

15/04/2023

Kun ga Ramadhan ya kusa ƙarewa, ku himmatu wajen aikata ayyukan alkhairi ba lallai Ramadhan mai zuwa a yi da mu ba; Ubangiji Allah Ya karɓi ibadunmu amin.

17/03/2023

Yaa Ubangiji Allah! Ka zaɓa mana shugabanni na-gari masu tsoron Allah da riƙon amana.

Yaa Allah! Ka gyara zukatanmu , Ka tabbatar da diga-diganmu bisa gaskiya; ka shiryar da zukatanmu Ka karkatar da hannayenmu ga dangwalawa mutanen kirki wadanda ka yarda da su ko da mu ba mu yarda su ba.

Yaa Allah! Ka tsare mu yin mugunyar da-na-sani.

Allah Yasa mu wanye lafiya, amin.

10/03/2023

Allahummah Salli 'Ala Muhammadin Wasallim.

Address

Nguru
603101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jamilu Ibrahim Mukhtar posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category