The Greatest Man Prophet Muhammad ﷺ

The Greatest Man Prophet Muhammad ﷺ To promote the love of prophet muhammad ﷺ wama arsalnaka illah rahmatan lil-alamin ﷺ

Big shout out to my new rising fans! Musty Jaji
23/08/2026

Big shout out to my new rising fans! Musty Jaji

05/08/2026
04/08/2026

(Suratun An-Naml: 62)
أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَاءَ الْأَرْضِ ۗ أَإِلَٰهٌ مَعَ اللَّهِ ۚ قَلِيلًا مَا تَذَكَّرُونَ
FASARAR HAUSA
"Ko wane ne yake amsa wa wanda tsananin buƙata ko wata ƙunci ta same shi idan ya roƙe Shi? Kuma yake kawar da bala'i da wahala, sannan ya sanya ku magada a bayan ƙasa? Shin akwai wani abin bautawa tare da Allah? Kaɗan ƙwarai ne kuke tunani da ɗaukar darasi."

TAFSIRI
(1) Wa yake amsa wa mai tsananin buƙata?" Amsar ita ce: Allah kaɗai. Idan mutum ya shiga wata matsananciyar wahala, ya koma ga Allah da zuciya ɗaya, Allah ne Mai amsa addu'a idan Ya so.
(2)Wa yake kawar da bala'i." Duk wata cuta, damuwa, talauci, rashin lafiya ko wata fitina, Allah ne Mai ikon kawar da ita.

(3)Wa yake sanya ku magada a bayan ƙasa." Allah ne yake ba mutane iko su rayu a duniya, ya maye gurbin waɗanda s**a gabace su, kuma ya ba su damar mulki da amfani da ni'imomin ƙasa.

(4) Sai Allah Ya ƙare da cewa: Shin akwai wani abin bautawa tare da Allah?" Wannan yana tabbatar da cewa babu wani da ya cancanci bauta sai Allah Shi kaɗai.

(5) Sai Allahu maigirma da daukaka yace " kaɗan ne kuke tunani." Wato mutane kaɗan ne suke yin tunani mai zurfi har su gane waɗannan ni'imomi su kuma bauta wa Allah Shi kaɗai.

DARASIN WANNAN AYAR
Allah Shi kaɗai ne Mai amsa addu'ar mai cikin tsananin buƙata.
Ya kamata Musulmi ya koma ga Allah a lokacin farin ciki da lokacin ƙunci.
Allah ne Mai kawar da dukkan wata wahala da bala'i.
Ayar tana ƙarfafa imani da Tauhidi, wato bautar Allah Shi kaɗai ba tare da haɗa Shi da wani ba.Yin tunani a kan ni'imomin Allah yana ƙara imani da godiya.

Allah Ya sanya mu cikin waɗanda idan s**a shiga ƙunci suke komawa gare Shi, Ya kuma karɓi addu'o'inmu. Āmīn. sabo da shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wa Ahlihi wa Sahbihi wa sallam.

18/04/2026

AZIMI RANAR ARAFAT

Address

Nasarawa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The Greatest Man Prophet Muhammad ﷺ posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share