Mustapha Assalafy's fans

Mustapha Assalafy's fans

Share

Darulhadisis Salafiyya

Photos from Mustapha Assalafy's fans's post 15/06/2024

** HUDUBAR BANKWANA DA ANNABI MUHAMMAD (S.W.A) YA YI **

A IRIN WANNAN RANAR TARA GA
WATAN ZUL-HIJJAH,

SHEKARA TA GOMA BAYAN
HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARAFAT
KENAN)

ANNABI (SAW) YA FARA DA CEWA:

🔴🔵 “Ya ku mutane ku ba ni hankalinku, domin mai
yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan
wannan shekarar ba, saboda haka ku saurari
abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar
da abinda zan gaya maku) ga wadanda ba su a
wannan wuri a yau.

🔴🔵 Ya ku mutane kamar yadda ku ka riki wannan
wata, (na Hajji) da wannan rana (ta Arfa) da
kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma
abin tsarewa, to, haka kuma ku riki ran Musulmi
da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma
karewa, ku maida wa mutane kayan da s**a ba
ku amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu
su cuce ku.

🔴🔵 Ku tuna fa, hakika Allah zai yi
sakayya akan ayukakanku. Allah (SWT) ya hana
cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin
da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.

🔵🔴 ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye
addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku
akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka
ku guji binshi akan kanana.
🔴🔵 Ya ku jama'a hakika kuna da hakki bisa
matayenku, amma su ma suna da hakki bisa
kanku, to hakkin su ne akan ku da kuciyar da su,
Kuma ku tufatar da su akan jin kai. ku bi da su
kyakkyawan biyarwa. Ku kuma tausasa musu
domin su majibintan al'amurran ku ne, kuma
mataimakan ku, Hakki ne akan su da kar su yi
abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci
zina.

🔴🔵 Ya ku jama'a, ku yi kyakkyawar bauta ga Allah
(SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, Ku
azumci watan Ramadan, kuma ku bada zakka.
Ku aikata aikin Hajji idan har kun samu damar yi.

🔴🔵 Ku sani fa, kowane musulmi dan'uwan musulmi
ne. Dukkan ku daidai ku ke. Ba wanda yake da
fifiko saman wani sai wajen tsoron Allah da
aikata kyawawan ayyukka
🔴🔵 Ku tuna fa (ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya
gaban Ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku,
saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da
hanya madaidaiciya bayan na kau.
🔴🔵 ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai
zo bayana kuma babu wani addini da zai zo
(bayan addinin musulunci), saboda haka ku yi
tunani sosai akan wannan magana da na gaya
maku, kuma ku fahimce ta (sosai).
Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); (Alkur
ani) ga kuma (Sunnah). Idan kun bi wannan ba
za ku taba bata ba. Duk wanda ya ji wannan
sako to ya jiyar da wadansu, su ma su jiyar da
wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji
magana daga karshe su fi masu ji na yanzu
fahimtar abinda nake fada.
🔴🔵 Ya Allah ka zamo shaida a gare ni, cewa na isar
da aikenka zuwa ga bayinka.”

'Yan uwa ku yada wannan HUDUBAR ga 'yan
uwa musulmi wadda kamar yau aka yi ta!!!

Ya ALLAH Duk wanda ya yada wannan hudubar ka sanya shi a cheton Annabi Muhammad s.a.w

Rubutawar: ✏ Muhammad basheer musa Assalafy

13/01/2024
13/12/2023

** GAISAWA DA MACE **
Annabi s.a.w ya na cewa Kamar yanda aka
rawaito daga ma'akalu dan yasar

ﻋﻦ ﻣﻌﻘﻞ ﺑﻦ ﻳﺴﺎﺭ ﺃﻥ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ
ﻗﺎﻝ : " ﻷﻥ ﻳﻄﻌﻦ ﻓﻲ ﺭﺃﺱ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺑﻤﺨﻴﻂ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺪ
ﺧﻴﺮ ﻟﻪ ﻣﻦ ﺃﻥ ﻳﻤﺲ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻻ ﺗﺤﻞ ﻟﻪ " ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ
ﻭﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ .

Manzo s.a.w yace : A LUMAWA MUTUM KUSA TA BA'KIN QARFE A
KANSA,SHI YA FI MASA ALKHAIRI DA YA SHAFI (GAISAWA) DA
MACEN DA BA MUHARRAMARSA BA

('DABARI DA
BAIHAKI NE S**A RAWAITO.)

ALLAH YA BAMU IKON GYARAWA MU DA SHEHUNNAN MU

Muhammad Basheer Musa Assalafy ✏

06/11/2023

QARSHEN ZINDIQI YAZO !!

" ALLAH YAYIWA DR YUSUF ALI RASUWA

malamin shine wanda yayi ikirari wai yana "rubutawa Allah wasika" Kuma yanada Number wayar Allah
Kuma
"Tun daga Fatiha har zuwa Nasi, Annabi Muhammad (Saw) ne ya karantar dashi ido yana ganin ido, a karkashin wata bishiya.

Bana Mantawa a cikin Kaset din Sheikh Ja'afar Mahmud Adam R-H mai suna ( GWAGARMAYA TSAKANIN QARYA DA GASKIYA ) Yayi Wannan Bayanin

Sannan ya Kira Yusuf Ali da KAFURI , FASIQI , ZINDIQI , sannan yace Yusuf Ali bai Tuba ba daga wannan Kafurcin har bayan Malaman Fadar Masarautar Kano s**a Ayyana shi a Matsayin Kafuri ZINDIQI

******

Muhammad Basheer Musa Assalafy ✏

19/09/2023

Zuwa gaba kadan mutum sai yaji kunyar yace shi dan Darika ne

Ba karamin taimako karantarwar sunnah tayi a Nigeria ba,irin wannan abin da jaki baka jin bugu ya fada al'ummar musulmai s**a yi masa caa! da a shekarun baya ya fadi hakan babu abinda zai fari.

Sai dai jama'a su daga kai su ce "radiyallahu anhu" suna mai cike da da jinjina ga karamar shehu tijjani,da wayan mu za'a tara mu ayi ta mana karairayi da sunan walittaka mu kuwa mu yi ta al"ajabi ga wannan karama ta shehu.

Tsoron ma sa6awa shehu kake yi saboda an ce idan yayi fushi da kai zaka ta6e,😄

Amma yanzu tsoron ma fadar karamomin suke yi saboda yanzu ilimi ya yawaita, kana fadar magana za'a ce kawo hujja, qur'ani ko hadisi, kasuwar mafarki da tatsuniyoyi da karamomin waliyyai ya daina ci yanzu, lokacin yanzu lokaci ne na "qalallahu qala rasulullahi".

Alamu suna nuna zuwa gaba kadan sai mutum ya ji kunyar ma ace shi dan dariqa ne,saboda ko yanzu idan ka duba yadda matasa suke fahimtar karantarwar sunnah abin sai ya baka mamaki.

Dahiru Garba Turawa

19/09/2023

Ga Abin Da Manzon Allah (S.A.W) Ya Fada.

Sahabin Manzon Allah S.A.W Jabir ya rawaito Manzon Allah S.A.W idan zai yi huduba yana cewa : "Hakika mafi alherin zance shi ne maganar Allah. Mafificiyar shiriya ita ce shiriyar [Annabi] Muhammad. Mafi Sharrin al'amura su ne wadanda aka kirkiro [Bidi'o'i] kuma dukkan abin da aka kirkiro bata ne". Imam Muslim ne ya rawaito wannan hadisi.

Don haka babu wani abin da za a kirkiro a addini ya fi na Manzon Allah S.A.W, duk kuwa yadda mai shi yake ganin kyansa.

Dan uwa rike abin da Manzon Allah S.A.W ya zo da shi, ba za ka yi nadama ba ranar alkiyama.

05/09/2023

YAN BID'AH DILLALAN SHARRI, KUNJI KUNYA WLH!

Kunji kunya (inkuna da ita) yan bid'ah wlh, shekaru kusan 50 Maluman sunnah a Nigeria sunjefa muku kalubalen da har yau kunkasa kare kanku ta hanyar baje kolin ilimi na gaskiya ku kare mushrikan cikinku da cuwa cuwar da kuka daura bayin Allaah akai

Tsawon shekarun nan babu wani sako na ilimi da kuka iya karekanku, sai kame kame, da sharri ga maluman sunnah

Wlh kunji kunya!

Maluman dakuka sa agaba da sharri irin naku, su kowa yaga karshensu yayi kyau, domin malamanku dasuke da sauran tunani da sanin gaskiya har saida wasunsu s**ai fatan inama suma suyi irin wannan karshen

Dan sun tabbatar babu mutumin da zai dace da irin wannan karshen sai in shi din nakirkine makusanci Allaah da ManzonSa (Sallallaahu Alayhi Wasallam).

Dan haka kai dan uwana dan bana bakwai irina! Kasani, sharri ba abinyi bane, Ka nisanta kanka daga manyan banza angirma ba'asan angirma ba, angirma ba'adaina karya da sharri ba

Ko bakomi yakamata kusani, daga nagaba ake gane zurfin ruwa, su sunma mutu amma har gobe duniyar muslunci tana amfana dasu, Al'umma na karuwa dasu tafahimci addinin Allaah (Subhanahu Wata Ala)

Kuma kowa yasani basuyi kira da abi wani malaminsu ko shehunsu ba, face kiran A bautawa Allaah (Ta'ala) Shi kadai batare da HadaShi da wani ko wani abu ba, sannan biyayya Ga Annabin Rahma (Sallallaahu Alayhi Wa Sallam ), domin shi Annabi biyayya akemai ba bauta ba

Amma ku baku da aiki dayawuce abi Shehu wane kar'abi Shehu wane!

Allaah ya kyauta yayimana kyakkyawan karshe, yasa muyi mutuwa irinta bayin Allaah nagari (Siddiyqhay da Shaheedai) Yaa Ilaahil Aalameen Yaa Hayyu Yaa Qhayyumu!!!

Allaah Kayimana tsari daga sharrikan kawunanmu da mu nanan aiyukanmu
Yaa Rabbal Aalameen!

👉Engr Abu Humairah Al-Jasawiy
05/09/2023

Want your school to be the top-listed School/college in Minna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address

Minna
Minna
SALAF