13/03/2017
MAHUKUNTA SU DAUKI MATAKI KO FATA DA BURIN MAKIYA SON ZAMAN LAFIYA YA CIKA
Daga Datti Assalafiy
Abinda yarbawa s**ayiwa hausawa a garin Ile Ife jihar Osun ta'addanci ne tsantsan, kuma idan har shugabannin gwamnati s**aki daukan mataki komai zai iya faruwa a cikin kasa
Mu 'yan arewan Nigeria kuma musulmai dole hankalinmu zai tashi da ganin abinda yarbawa s**ayiwa 'yan uwanmu
Anan arewa mata guda dayace tak inyamura aka zarga da laifin ta zagi fiyayyen halitta (saw) sai aka kashe ta nan take, amma ba'a dauki wani lokaci mai tsawo ba sai da ta kai hatta shugaban kasa ya fito ya jajanta akan lamarin
Mai yasa ne idan anyiwa hausawa ta'addanci da sunan addini ko kabilanci shugabannin gwamnati basa nuna damuwarsu akai duk ga dokokin kasa sunce daya ake babu wani banbanci?
A irin wannan yanayi babu laifi idan akace mahukunta suna nuna banbanci da rashin adalci tsakanin 'yan arewa da 'yan kudanci wato musulmai da kiristoci, kumna irin wannan banbanci da wariya da ake nunawa zai iya haifar da kungiyoyin ta'addanci masu fakewa da sunan jihadi
Da 'yan arewane s**ayi ta'addanci irin wannan s**ayiwa 'yan kudanci kofar rago s**a buge s**a konesu da tayu, da yanzu duk wata kafar yada labarai ba wani labarin zasu kawo ba sai wannan ta'addancin
Yana daga cikin dadadden dabi'un mutanen kudanci wato mafi akasari inyamurai da yarbawa shine kona mutane da wuta, dabi'arsu ce hakan tunda jimawa
Misalin gari k**ar Lagos; da zakayi ihu a tsakiyar kasuwa ka nuna wani mutum kace barawo ne iyakacin hukuncin da zasuyi masa batare da wani bincike ba, nan take za'a bugeshi a aza masa tayu a kona da wuta
Ya k**ata mahukunta su hana mutanen kudanci dadadden dabi'arsu na kona mutane da wuta, babu inda wata doka a Nigeria yayi tanadi akan haka, ko 'dan fashi da makami ne dokar Nigeria batace a konashi da wuta ba, amma a gaban jami'an tsaro mutanen kudu suke kona mutane da wuta da sunan wai an k**a barawo
Abinda akayiwa 'yan arewa a garin Ile Ife cewa suke wai fadan kabilanci ne, ba zai taba k**a hankali ba ace mutane sunje wani yanki da ba nasu ba, kuma cikin kabilar da ba nasu ba, watakila cikin addinin da ba nasu ba, sannan ace wai zasu tada fitina ko su takali wani ko wasu daga cikin mutanen da s**aje s**a tarar, haka ba zai taba yiwuwa ba sam!
Da wannan muke zargin cewa an hada wannan husuma ne da zummar a cimma wani boyayyen shiri da manufa irin na makiya son zaman lafiyar kasarmu Nigeria domin a tada hankalin kasa, lura da cewa a halin yanzu akwai kyakkyawan alaka harma a gwamnatance tsakanin 'yan arewa musulmai hausawa da yarbawa wadanda yake suma mafi akasarinsu musulmai ne, a garemu 'yan arewa gwamma yarbawa akan inyamurai
Kuma basu tsananta kunna wutar fitinar ba sai da s**aga shugaban kasa Buhari ya dawo
Mu dai munyi imani da bincike da kuma fayyace gaskiya, muna kira ga mahukunta suyi kwakkwaran bincike tare da daukan matakin gaggawa akan ta'addancin da akayiwa hausawa a garin Ile Ife, sannan a biya diyya, imba haka ba wallahi burin makiya son zaman lafiyar kasarmu Nigeria na dab da cika (Allah Ya sauwake)
Da zaran ance hausawa ko ince musulmin arewa suma sun fusata sun farwa yarbawan arewa domin daukar fansa shikenan kasar ta hargitse, kuma burin wadancan marassa son zaman lafiya ya cika
Muna rokon Allah Ya tona asirin duk wani boyayyen shiri da akeyi don a tada hankalin kasa
Muna rokon Allah Ya bamu zaman lafiya cikin kaasarmu Nigeria