06/04/2025
Allah ya cika maka burin ka !💔
~Idan muna Zaune dasu suna batun Shahada ko akai bana kawo su, sai in riƙa ganin shauƙi ne kawai irin na yarinta, domin a nawa ƙaramin lissafin shine mema s**a sani akan gwagwarmaya
Sannan kuma sune future ɗin da ake kokarin a gina koda Allah yayi..
Amma dayake lissafin bawa ba shine na Allah ba kuma dai na Allah ɗin shine mai tabbata
Mu mun shiga Ramadan Camp so ba tare da su muka rika raya dararen Layalil Qadar ba a makaranta, amma ance daga cikin Addu'ar da yafi yi shine Allah ya bashi SHAHADA..
yayi planning a goman ƙarshe zai tafi Kano, acan zaiyi Salla
Bansan mai yazo ya wargaza shirin ba, Hussainar sa tadamu da kira akan bazai zo bane? Mai yasa, bansan yadda s**a ƙare ba har ya iya gamsar da ita, ashe ƙaddarar sace ke kiran sa
wannan shine karon farko daya halarci Muzahara a Abuja, gashi Allah ya azurtata shi da Shahada.
Lallai Shaheed tafiyar ku a daidai wannan lokaci tai mana bazata! Domin ayyuka mafiya muhimmanci a Makaranta kune kuka tsayu dasu har mu muke samun damar fita muyi wasu abubuwan a waje. Amma Allah shine majiɓin al'amarin bayin sa.
Aroƙa Mana Allah muma ...💔😭🙏🏾🌹
Mai Zahara 💞🌹