18/10/2025
Kashe ƙimar mutaneda zargi ko ɓata masu suna yafi kashesu da takubba.”
Saboda kisa yana kawo ƙarshen rayuwar mutum ta jiki, amma kisan mutunci yana kashe shi a zuciya da al’umma yana hana shi ɗaukar amana, ɗaukaka kalmar gaskiya, da kwanciyar hankali sabida shi Abun zargine a wurin mutane.
A taƙaice, zargi, ɓatanci da ƙarya su ne makaman masu rauni da marasa gaskiya. Su kan kashe mutunci da suna na mai gaskiya suna kiran mutane dasunaye mabanbanta.
A hakikanin gaskiya, duk wata tafiyar addini ko al’umma da ma’abotanta s**a fara rushe ƙimar junansu, s**a mayar da ɗan’uwa wanda yake da ra’ayi ko matsayi daban a matsayin abokin gaba kuma Abun tuhuma, to wannan tafiyar ta fara rushewa daga ciki.
Saboda ba za a sami masu ɗaukar amanar gaskiya da amincin ci gaba ba, idan aka kashe ƙimar masu gaskiya da zargi, s**a zama abin tsoro maimakon abin koyi
Idan mutun yazo da ra'ayi nadaban Ana tsayawane a saurara da kwakwalwar basira Abada Amsa ta hankali ga gareshi cikin ruwan sanyi zata iya yuwuwa rashin fahimtane daga gareshi kokuma shiya fahinci Abinda ba'a fahimtaba hakan yana ƙara bayyana gaskiyar tafiya da irin salon Annabawa wajan shiryarda mutane
Tafiya ba ta rushewa da ƙarfin makiya daga waje kaɗai amma da rashin adalcin ’yan cikinta da kashe juna da harshe da zargi.