10/08/2025
Cikakken sunana Ibrahim Zubairu Baba, dan asalin Arewa amma na tashi a cikin birnin Legas. Na kammala digiri na farko a fannin Kimiyyar Kwamfuta daga Jami’ar Legas, sannan na yi MBA a Dangote Business School. Yanzu haka ina ci gaba da karatun Masters a Management Information Technology.
Tun ina ƙarami, zuciyata na cike da sha’awar fasaha — ina lalubo na’urori, in warware su, in fahimci yadda suke aiki. Wannan sha’awa ce da ta ja hankalina har na gina aikina gaba ɗaya a kai.
Yayin da na ke rayuwa a Legas, na ga yadda fasaha ke bunƙasa. Amma duk lokacin da na dawo Arewa, sai na tarar da tarin matasa da ƙwarewa amma ba tare da damar amfani da ita ba. Abin da ya fi daga min hankali shi ne yadda harshe ya zama babban shamaki: Turanci ya mamaye duniyar ilimi da fasaha, alhali har yanzu akwai miliyoyin mutanenmu da ba sa iya magana da shi sosai.
Wannan ne ya sa na kafa Skill Arewa (wanda aka fi sani da The North Tech Hub) tare da wasu abokaina. Manufarmu ita ce kawo ilimin zamani cikin harshen da mutane s**a fi fahimta — Hausa. Na gano cewa idan aka koyar da fasaha a cikin harshen gida, shingen da ke hana mutane shiga zai karye, ƙwarin gwiwa kuma zai ƙaru.
A karkashin Skill Arewa da Malamiromba Ltd, muna shirya horo, ƙirƙirar ƙunshe-ƙunshe, da gina al’umma inda kowani matashi ko dattijo, mai digiri ko mara shi ,zai iya koyon fasaha, fahimtar AI, ChatGPT, da sauran sabbin kirkire-kirkire. Muna tabbatar da cewa fasaha ta zama ta kowa, ba ta wani rukuni kaɗai ba.
A gare ni, wannan ba kawai buri ba ne — shi ne aikina, shi ne dalilin tashi na kowacce safiya.Ina son ganin matasanmu suna ƙirƙira, suna jagoranci, suna alfahari da harshe da al’adunsu a duniyar fasaha.