28/08/2019
๐บ *ARIKA KAI ZUCIYA NESA {109}* ๐บ
Bayan da Furai'ah ta kammala baiwa Nisreen labari, tare da dalilin da yasa ta dainayin social media gaba daya, sai Nisreen taja kuma ta hadiyi wani irin numfashi tace : _Hmmm, Allah ya kyauta._
Aka iso inda Furai'ah zata sauka, tayi godiya ga Nisreen sosai akan rage mata hanyar da tayi. Nisreen taja motar ta tayi gaba, amma inaa jikinta yayi sanyi tukin ma yana mata nauyi.
Sak**akon mutuwar da jikinta yayi, saboda labarin da Furai'ah taba ta akan Kawarta, Nisreen dai ta paka motar gefe, ta kafa goshinta akan sitiyarin motar tana ta nazari ita kadai tana cewa:
_" Wai yanzu ace komai aka dauko sai akan kawata Ruwaihah zai kare, irin abinda Raihaan tafadamin gashi kuma itama Furai'ah ta fada min haka, amma inajin abayane s**a santa da wannan halin, da kyar ne idan yanzu tana da shi saboda nidai banga wata alama ba."_
*"Nisreen dai kam ta kasayin karatun ta nutsu akan lamarin Ruwaihah, kodai shaidanune s**a zamto kawayenta sakamokon yin watsi da Azkaar da tayi."* _Allah ya kyauta._
_"Idan har mutum ya kauracewa yin Azkaar na safiya da maraice, da sauran mu'amilolinsa na yau da kullu, ya kauracewa sauraron maganar Allah da manzon sa, sai kuga shaidanun Aljanu da na mutane sun zama sune abokansa, kuma surika yin tasiri akanshi"._
Nisreen dai takara jan motar ta tawuce makaranta, ta makara Sosai amma ahakan dai ta tafi, kuma ta kasa amincewa da abinda Ruwaihah akace takeyi, saboda shaidanu sun fitsare mata kunnuwa ba ta jin gaskiya, da zuciyarta tayadda ba ta yarda da gaskiya. Allah ya kyauta.
Bayan ankwana biyu, Sai *Ummu Nisreen* ta hadu da Kawarta *Ummu Waraqa* (wacce ta taba neman agajinta akan ta bata yadda zatayi ta turawa fa NNufail sako) a wani wuri tace da ita:
_"Haba Ummu Waraqa, na turo miki sako akan kibani mafita amma shiru nakejin ki, k**ar na shuka dusa."_
*"Wato Ita Ummu Waraqa, ganin tayi gwamma ta zo su fattauna ido na ganin ido, ta bata shawarwari tare da tsoratar da ita Illar yin hakan, akan ce