Abba Gwani Lawan

Abba Gwani Lawan

Share

A TEACHER ,
FIRST AIDS GROUP OF JIBWIS KONDUGA AND
CEO AGL FORM

02/05/2026
29/04/2026

🎉 SAKON TAYA MURNA 🎉

Muna miƙa saƙon taya murna ga ɗaukacin ’yan Najeriya, bisa wannan babbar nasara da aka samu, inda ɗan ƙasarmu ya samu matsayi na farko (1st position) a gasar.

Wannan nasara abin alfahari ne ga ƙasa baki ɗaya, kuma shaida ce ta ƙoƙari, jajircewa da kuma baiwar da Allah Ya yi.

Muna taya:
Hamid Musa Zakaria murna ta musamman bisa wannan gagarumar nasara.

🤲

Alhamdulillah!
Muna roƙon Allah Ya ƙara ɗaukaka,
Ya sa wannan nasara ta zama alheri a gare shi da ƙasa baki ɗaya.

---

🌟 Allah Ya ci gaba da ɗaukaka Najeriya da ’ya’yanta 🤲✨

23/04/2026

Gwani Anas Salis Kura Ya Kammala Digiri na Uku a Fannin Qira’oin Alƙur’ani a Jami’ar Musulunci ta Madina

Gwani Anas Salis na ɗaya daga cikin fitattun matasa masu haskaka fagen ilimin Alƙur’ani, inda ya gina kansa a kan ƙwazo, himma da natsuwa. Ya samu nasarori masu girma a harkar ilimi, ciki har da kammala karatu a Jami’ar Musulunci ta Madina da sakamakon First Class, wanda ya zama wata alama ta ƙwarewarsa.

Haka kuma, ya mallaki ijaza cikin ƙwarewa, lamarin da ya ƙara tabbatar da matsayinsa a matsayin abin koyi ga masu neman ilimin Alƙur’ani. Salon karatunsa mai sauƙi da santsi ya sa yake da jan hankali ga ɗalibai, tare da haɗa ladabi da mutunci a matsayin ginshiƙai na halayyarsa.

Duk da wannan matsayi, ana kira gare shi da ya ƙara fito da iliminsa fili domin amfanin al’umma, musamman ta amfani da kafafen zamani kamar Facebook da WhatsApp, domin iliminsa ya isa ga jama’a ba tare da tangarda ba.

Allah ya ƙara masa haske, ya kuma sa iliminsa ya zama sanadiyyar amfanin al’umma baki ɗaya. 🤲

22/04/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Itz Ella, Muhammed Baiwa, Mustapha Babanga, Ghaznfar Jujj, Bello Abdullahi, Mohummed Abdul, Aminu Alasan, Hammed Abdurahman

14/04/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Saratu M Rabilu, Aliyu Yankwashi, Halifa Silber Halifa Silber

06/04/2026

MARABA DA ZUWA ZARIA, YA SHEIKHANAH...

A cikin shekarar 2009, Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya taɓa gabatar da wata muhadara a Zaria a lokacin an gabatar da lakcar ne cikin harshen Larabci. In ba na manta ba, matashiyar muhadarar shine (شرط الإمام البخاري في صحيحه). A daidai lokacin muna karatun littafin (تدريب الراوي) tare da malaminmu Sheikh Albaniy Zaria (Rahimahullah), saboda haka sai karatun ya yi mana daɗi.

A yanzu ma in sha Allah, mun sami sahhalewa daga Farfesa Muhammad Sani cewa zai zo Ranar Asabar 11/04/2026 ya gabatar da lakca a Mu'assasatul Ishah dake Anguwar Ɗandutse, Tudun Wada Zaria bayan sallar Magriba sannan in gari ya waye ranar Lahadi 12/04/2026 sai ya zo Daarul Hadeethis Salafiyyah don gabatar da wata lakcar.

Saboda haka, ana gayyatar kowa da kowa don sauraron waɗannan tagwayen lakcoci.

Allah ya ba da ikon halarta

02/04/2026

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
GAGARUMAR LAKCA

Kwamitin Gudanarwa na Jami'u Islahil Ummah na farin cikin gayyatar daukacin al’ummar Musulmi zuwa gagarumar lakca tare da:

Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale

📅 Rana: Friday, 03-04-2026
🕰️ Lokaci: Magriba zuwa Isha
📍 Wuri: Farfajiyar Masallacin dake No. 16, Umar Adamu Kawaji Street, Daura da Ofishin Hisba, Yankaba
🎤 Maudu’i: Idan An Zo A Ji

Allah Ya bada ikon halarta

Sadik Abu Abdallah ✍️
02-04-2026

02/04/2026

I accepted 1 fan badge from Iliyasu Alhaji Akilu.

02/04/2026

MUHADARA MUHADARA MUHADARA

Akwai gagarumin wa'azin addinin Musulunci ranar Asabar mai zuwa (4/4/2026) a Masallacin Juma'a na Usman Bin Affan da ke ƙofar Gadon Ƙaya, Kano.

Tare da babban malamin Sunnah Professor As-Shaikh Abdallah Saleh Pakistan Hafizahullah.

Allah ya ba da ikon halarta

Want your school to be the top-listed School/college in Maiduguri?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address

Sabongari Konduga
Maiduguri