17/03/2026
An gabatar da Hutun jarabawa ga ɗaliban Makarantar Al-akram Islamic Academy Kudan End of 2nd Term Examination 2025/2026 Academic Session.
A wannan rana ta Talata 17/3/2026 an gabatar da Hutun ga ɗaliban Makarantar Ma'ahad Rasulil Akram ( S ) kudan ɓangaren Boko. Al-akram Islamic Academy Kudan, Tare da ba su saka makon jarabawar ga kowanne ɗalibi.
Bayan gabatar da jawabin Director Abdulsalam Husaini inda ya yi jan hankali sosai akan yadda ɗalibai s**a taka rawa a wannan jarabawar wanda kake tunani sai kaga ya zo ya baka mamakin da baka tunani. Inda ya ƙara da cewa lallai Ɗalibai sunbawa malamai haɗin kai sosai wajan gudanar da jarabawa.
Shugaban makarantar Mr. Nuhu Muhammad (Principal) ya yi jan hankali sosai akan wannan ɗalibai tare da jan hankali akan cewa dukkan loƙacin da akace anyi hutu to, abin da ya k**ata ɗalibi ya sani shi ne cewa dukkan loƙacin da ya koma gida abin da yafi da cewa shi ne ya mai da hankali akan karatun da akayi masa a gida ya kasance cewa yana bitarsa sosai bawai ya a jiye littafinsa ba sai loƙacin da za a dawo Makaranta sannan ya ce zai ci gaba da karatu ba haka akeyi ba.
Malama Hannatu Abdullahi (Headmistress) Nursery and Primary Sections. Ta yi jan sosai akan Ɗalibai tare da yabo ga ɗalibai yanda s**a taka rawa sosai, Wanda hakan ya sa lallai tayi farin ciki sosai bisa yadda su kayi ƙoƙari wajan karatu da mai da hankali sosai akan jarabawa.
Sauran Malamai sunyi bayani ta bangaren daban-daban akan jan hankali sosai ga ɗalibai da ƙarfafawa akan Ilimi da mai da hankali akan karatu.
Ga kaɗan daga cikin Hotunan da aka gabatar da taron raba saka makon jarabawa ga ɗalibai.
Al-Akram Islamic Academy Kudan
17/3/2026
17/03/2026
JARABAWAR ƘARSHEN ZANGON KARATU NA BIYU (SECOND TERM)
A ranar Litinin 9 ga watam Maris 2026 ne ɗaliban makarantar Al-Akram Islamic Academy Kudan s**a fara gabatar da jarabawar karshen zangon karatu na biyu (Second Term).
An gabatar da jarabawar ne a dukkan ɓangarorin makarantar k**a daga Nazire da Firamari da Ƙaramar Sakandire da babban sakandire.
An k**ala jarabawar ne a jiya Litinin 16 ga watan Maris 2026.
Yau Talata 17 ga watan Maris 2026 ne akayi hutu tare da mikawa dalibai sak**akon jarabawarsu.
Wannan kaɗan ne daga hotunan da aka dauka a loƙacin jarabawar.
Al-Akram Islamic Academy Kudan
17 March 2026
04/02/2026
Innah Lillahi Wa Innah Ilaihi Raji'un
A madadin Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (Rasool Al-Akram Institute - Nigeria) da dukan bangarorinta (Hauzah) da (Tahfiz) da kuma (Boko) malamai da ɗilibai muna miƙa saƙon ta'aziyyarmu ga Iyalai da Ƴan'uwan da kuma dalibarmu Sahura Auwal wanda mahaifinta Auwal Bakanike (Auwal na Musa) Allah yayi masa rasuwa yau Laraba 16/ Sha'aban/ 1447H daidai da 4/2/2026.
Muna roƙon Allah ya jiƙanshi yayi mashi gafara yasa aljannah ce makomar shi.
Marigayin mutumin kirki ne mai son Addini mafi yawan harkokin wannan makaranta yaƙan halarta, zuwanshi na ƙarshe wannan makaranta shine ranar 22 January 2026 zaman taron Iyayen Ɗalibai na wannan makaranta (PTA) kwana 13 kenanda s**a gabata.
Allah ya bada haƙurin wannan rashi ya albarkaci abinda ya bari.
Hotunan dake ƙasa Marigayin ne ke miƙa kyauta ga wasu daga cikin Ɗalibai.
Al-Akram Islamic Academy Kudan
04 February 2026
23/01/2026
PTA TARE DA KARRAMA ƊALIBAI
Al-Akram Islamic Academy Kudan ta shirya taron Iyayen Ɗalibai tare da karrama dalibanta da s**a nuna kwazo a jarabawar karshen zangon karatu na farko ( First Term).
An gudanar da wannan taron ne a jiya Alhamis 22 January 2026 a dakin taro na Makarantar.
A lokacin taron an tattauna abubuwa da yawa da s**a shafi cigaban makarantar da hanyoyin da za'a inganta harkan koyo da koyarwa a wannan makaranta tare da kawo hanyoyin da zasu taimakawa dalibai domin samun ingantaccen ilimi.
A karshen zaman kuma an rarraba kyautuka ga dalibai sama da 30 waɗanda s**a nuna kwazo a yayin jarabawa a ajujuwansu mabanbanta dake makarantar.
Iyayen daliban da s**a halarci wannan taron sun nuna gamsuwarsu bisa salo da tsarin inganta karatun yayansu wanda Makarantar ke yi tare da nuna wannan makaranta a matsayin wacce babu irinta wajen nuna kwazo da kawo sabbin dabaru don inganta ilimin yara a Makarantar.
A ƙarshe anyi addu'a aka sallami kowa.
A I A KUDAN.
23 January 2026