05/06/2026
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un😭💔
"Hukumar makarantar mu tana cikin babban alhini da jimamin rashin daya daga cikin hazikan dalibanmu..."
kuma jajirtacciyar malama mai koyar da ilimin Hadith da Fiqhu, wadda ta koma ga Allah a yau Juma'a bayan ta shafe tsawon shekaru biyu tana jinya.
Shaidar Alherinta:💯😍
Muna shaida cewa ta kasance malama kuma daliba abar koyi. Ta kasance mai kyakkyawan hali, cike da kirki, da kuma fadin gaban da yake sanya ta kauda kai ga duk wani abin da aka mata. Ko a cikin tsananin jinyarta, ba ta kasance mai yawan korafi ba, sai ma nuna juriya da tawakkali ga Allah.
Addu'ar Mu Gare Ta:🤲🏻😭
Muna rokon Ubangiji Allah ya karbi jinyar da ta yi a matsayin kaffara da kuma silar daukaka darajarta a gidan gaskiya. Ya Allah ka gafarta mata, ka haskaka kabarinta, ka sanya karatuttukan da ta koyar da wadanda ta koya su zama mata sadakatul jariyah. Allah ya hada mu a Aljannar Firdausi.🤲🏻📿
Don Allah ku taya mu yi mata addu'a a wannan rana mai albarka ta Juma'a.
Maintenance... ✍️