03/09/2026
TAWAGAR DARAKTOCIN FMC DAURA TA KAI ZIYARAR GIRMAMAWA ZUWA YUSUF BALA USMAN COLLEGE OF EDUCATION AND LEGAL STUDIES, DAURA
Tawagar Daraktoci da manyan jami’an gudanarwa na Federal Medical Centre (FMC), Daura, a jiya sun kai ziyarar girmamawa zuwa Yusuf Bala Usman College of Education and Legal Studies, Daura, inda s**a gudanar da tattaunawa mai zurfi da mahukuntan Kwalejin kan muhimman batutuwan da s**a shafi ci gaban hukumomin biyu da sauran abubuwan da ke tsakaninsu.
Tawagar wadda ta ƙunshi kusan mutum takwas, Dr. Umar Faruk Abdulmajid, Daraktan Kiwon Lafiya (Medical Director) na FMC Daura, ne ya jagoranta. Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Abdulrahman Abubakar, Ibrahim Abdullahi, Dr. Yusuf Musa Muhd, Bashir Abubakar Gajam, Mrs. Amina Zakari, Rindam Mumir da Attahiru Salisu Mohammed.
Da yake karɓar tawagar, Provost na Kwalejin, Prof. Ibrahim Lawal Kane, ya yi wa baƙin maraba tare da bayyana godiyarsa kan ziyarar girmamawar da s**a kawo.
A jawabin nasa, Provost ɗin ya yi bayani dalla-dalla kan tsarin Dual Mandate na Kwalejin, tare da bayyana shirye-shiryen karatu daban-daban da makomar ci gaban Kwalejin.
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu Kwalejin tana gudanar da darussa daban-daban da s**a haɗa da NCE da kuma nau’o’i biyu na shirye-shiryen Diploma, waɗanda hukumar National Board for Technical Education (NBTE) ta amince da su.
Haka kuma, ya bayyana cewa Kwalejin na shirin fara gudanar da shirye-shiryen bayar da Digiri (Degree Programmes) nan ba da daɗewa ba, daidai da faɗaɗa nauyin ilimi da aka ɗora wa Kwalejin.
Ita ma Registrar ta Kwalejin ta yi wa tawagar baƙi bayani kan darussa daban-daban da Kwalejin ke gudanarwa, tare da ƙarin bayani kan tsarin Dual Mandate da Gwamnatin Tarayya ta bullo da shi. Ta bayyana cewa tsarin zai gudana ne da wani sabon tsarin manhajar karatu wanda ya bambanta da tsarin NCE na yau da kullum.
A yayin ziyarar, an kuma tattauna batutuwa daban-daban da s**a shafi Asibitin Kwalejin, inda bangarorin biyu s**a musayar ra’ayoyi kan ayyukan kiwon lafiya, ci gaban hukumomi da kuma hanyoyin da za su iya yin haɗin gwiwa.
Daga bisani, tawagar tare da wasu jami’an Kwalejin sun ziyarci sabon ginin Sarki Abdulrahman Leko Hospital da ke cikin harabar Kwalejin, inda s**a duba kayayyaki da ci gaban aikin ginin asibitin.
An gudanar da ziyarar cikin yanayi na mutunta juna da kyakkyawar fahimta, inda hukumomin biyu s**a bayyana aniyarsu ta ci gaba da ƙarfafa dangantakarsu tare da binciko hanyoyin haɗin gwiwa domin amfanin al’ummar Kwalejin da sauran jama’a.
Media and Information Unit
Yusuf Bala Usman College of Education and Legal Studies, Daura