28/10/2025
A shekarar 2012 muna Master's Degree, lokacin da wata ƙawar karatuna a jami'ar BUK ta gaya min cewa ba ta taɓa shiga Library ba har ta gama degree na farko, wallahi sai da na girgiza bisa mamaki, mamakin da bai daina ratsa min kai ba sai kusan 2021, lokacin da na samu ɗaliban level 400 da s**a tabbatar min cewa zuwa wannan lokaci da suke level 400 a jami'a, ba su taɓa karanta wani littafi ba, bango zuwa bango, a rayuwarsu.
Na girgiza sosai duba da yanda mu ke rigegeniyar zuwa State Library a wancan lokacin, da kuma British Council Library tun kafin mu shiga jami'a; da yanda mu ke tafiya kasuwar Bata da Church Road don siyo littafin da za mu karanta. Ni da abokina Ibrahim Umar Mustafa (Inyas), mu kan haɗa kuɗi mu sai littafi ɗaya. Ya karanta, sannan in karanta, ko vice versa. Daga baya sai mu ƙara haɗa kuɗi in an samu sai a ƙaro copy ɗaya na wannan littafin don kowa ya mallaki nasa. A BUK kuwa, ni da su Mukhtar Hikima mun abokaci Library da gaske.
A wancan lokacin, na fahimci ƙawar karatuna cewa ita mai baiwar ɗaukar Lecture Note ce da kuma ƙarfin haddace shi. Hakan ya sa ta gama degree na farko da Upper Second Class, kuma, alhamdulillah, tuni yanzu ta kammala PhD ɗinta. Su kuwa waɗancan ɗaliban nawa, babu ɗaukar Lecture Note ballantana su haddace, kuma ba su da lokacin yin karatun ma. Burinsu kawai su karɓi kwalin degree su garzaya Abuja gurin Uncle wane ko abokin dad wane; da Aunt wance ko ƙawar mamansu don su sama musu aiki mai tsoka a can.
A waccan tafiyar kafin bayyanar M***i "AI", Sheikh Google ne bangon jinginar irin waɗancan ɗalibai marasa karatu, shima ta hanyar shehunnai masu typing a café da suke karɓar ƴan kuɗi kaɗan su nemo assignment ko project a Google, a yi copy and paste da canjin suna a wuce wajen. A kan amfani da zaƙaƙuran abokan da ke iya bin dare su yi karatu da haɗa assignment, amma wannan doguwar hanya ce. Shehin Café ya fi sauri.
A yau bayan bayyanar M***i AI, kaso mafi yawa cikin ɗari na ɗalibai sun daina karatu sam. Koda dai a haka ma ina ganin na yanzun sun ɗan ɗara waɗancan rafkanannun da ba sa iya leƙawa Google da kansu sai dai shehun café ya leƙa musu. Waɗannan sun iya tambayar AI da kansu ba shakka. Amma dai maganar Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ta na tabbata cewar za a samu generation na tatattun jahilai a ƙasarnan. Kamar an zo wajen!
Ba za ka gane haka ba sai ka yi hira da masu sayar da littafai irin su Hamza Jalal, Badamasi Book da su Ummi Aliyu Sabon Gida za ka gane cewar mafiya yawan masu sayen littafansu ba yaran wannan zamanin bane, har yanzu abokanmu ne, ƙannenmu kaɗan, da yayyenmu irin su Dr. Shamsuddeen Sani. Ban ce babu yara masu tasowa cikin masu sayen littafi ba, akwai, amma basu da yawa. Social Media Culture ta maye gurbin Reading Culture, musamman a tsakanin ƴan Gen Z.
A yanayin talauci da ƙuncin rayuwa da jama'a ke ciki, na kan yi wa yara uzurin rashin yin karatu in na kalli kuɗin abinci da riga da data da Social Media ta ke ba su. Sannan ita Social Media ta zama ɓangaren rayuwarmu da ba za a ce su daina ba. To me zai hana a ƙarfafa musu guiwa wajen neman ilimi don content da suke samarwa? Tabbas wannan shine abinda ya dace. Maimakon content na shirme da shiririta da su ke samarwa, su canja zuwa amfanarwa mana in sun yi karatu. Ka ga kenan sun yaƙi jahilci, kuma sun samu kuɗi! Allah ya ba mu ikon yin haka!
Mubarak Ibrahim Lawan