Taskar Imam Abubakar Saeed

Taskar Imam Abubakar Saeed

Share

SCIENTIFIC IMAM ABUBAKAR SA'ID CENTRE FOR THE DEVELOPMENT OF SCIENCE AND TECHNOLOGY IN ISLAM (SAISCEDESTI)

27/04/2026

Bayani Akan Internet kashi na Farko tare da Imam Sa'id Abubakar (Digital Imam) Allah ya ƙara lafiya

28/02/2026

Haɗin kai domin yin aiki tare shine ne Mafita

Hausawa Da Fulani: A Ina Matsalar Take?

~ Rubutu na Musamman Daga: Abubakar Isah H.

Hausawa Da Fulani: A Ina Matsalar Take?

Ni Bahaushe ne na asali wajen mahaifi, Bafilatani ta wajen Mahaifiya, kuma ba zan taɓa rufe ido ga abin da nake gani a zahiri ba. Zalunci, cin mutunci da take haƙƙin ɗan Adam da wasu ɓatagari daga cikin Fulani ke aikatawa abu ne da ya fito fili, kuma babu mai musun cewa su ne a gaba a yawancin bidiyoyi da rahotannin neman kuɗin fansa, azabtarwa da tozarta waɗanda s**a k**a. A wasu lokuta ma s**an fito karara suna alfahari da abin da s**a aikata, abin da ke ƙara tada hankali da ƙunci a zukatan jama’a. Wannan gaskiya ce mai ɗaci, amma gaskiya ce. Duk da haka, hikima ba ta yarda mu bar zafin zuciya ya rinjayi adalci ba. Ba zan taɓa amincewa da yin hukunci a kan ƙabila gaba ɗaya ba saboda laifin wasu jahilai. A cikin Fulani akwai malamai, masana, masu ilimin zamani da na addini, da kuma mutanen kirki waɗanda muke zaune tare da su, muna cin moriyar juna, kuma muna gina al’umma tare. Ta yaya zan share wannan gaskiyar in ɗora wa kowa laifi iri ɗaya?

A fahimtata, wannan lokaci ba na zargin juna ba ne, ba na ɗora yatsa ga juna ba ne. Lokaci ne na tsayawa tsayin daka domin kare rayuka da martabar al’umma, musamman idan gwamnati ta kasa sauke cikakken nauyin da ke kanta. Maimakon mu ƙara ruruta wutar gaba tsakanin Hausawa da Fulani, ya k**ata mu mai da hankali kan gano tushen matsalar da magance ta cikin hikima da haɗin kai. Na lura akwai kura-kurai guda biyu masu haɗari: na farko, akwai wasu Fulani da ba sa son a alaƙanta ta’addanci da ‘yan uwansu ko da a fili gaskiya ta bayyana, s**an ba su kariya kai tsaye ko a fakaice. Wannan kuskure ne, domin adalci ba ya son son rai. Idan laifi ya tabbata, dole ne a faɗi gaskiya. Na biyu kuma, akwai wasu Hausawa da s**a rungumi gaba ɗaya ƙiyayya, suna ɗora wa Fulani duka laifin ta’addanci. Wannan ma babbar kuskure ce da take saɓa wa mizani na adalci. Laifi na mutum ne, ba na jini ko asali ba.

Mu tuna cewa Allah Ya ƙaddara mana zaman tare; mun yi aure a tsakaninmu, mun yi kasuwanci tare, mun zauna unguwa ɗaya, har ma mun narke cikin juna. Idan kowane ɓangare ya waiwaya dama da hagu, zai ga makusanci ko aboki daga wancan ɓangaren wanda a lokacin tashin hankali zai iya ba shi kariya. To me ya sa za mu gina katangar gaba a inda tarihi da zamantakewa s**a riga s**a gina gada? Adalci shi ne a ɗora laifi a kan wanda ya aikata shi, ba a shimfiɗa shi kan al’umma baki ɗaya ba. Idan muna son makoma mai kyau ga ‘ya’yanmu, dole ne mu sauya tunani, mu fifita gaskiya da adalci a kan son zuciya, mu kuma haɗa kai wajen kawar da ɓatagarin da ke ɓata mana suna da zaman lafiya. Wannan ita ce matsayata.

Ra'ayin Abubakar Isah Hassan

Allah ya bamu zaman lafiya mai ɗorewa. Baraknmu da Juma'a

31/01/2026

Kimiyyah Da Fasaha

02/09/2025

"Yankin Arewa na Fuskantar barazana” ~ Imam Imam Saeed Abubakar

13/08/2025

Allah yana kishin Musulman Gaza

13/08/2025

Bayani akan Galaxy da Milky way tare da Imam Saeed Abubakar





01/07/2025

Kira zuwa ga Musulman duniya: Sheikh Imam Saeed Abubakar

01/07/2025

Mutuwa tana kan kowa!😭

20/06/2025

Rikicin gabas ta tsakiya: Tsakanin Iran da Isra'el (Part 3)

Gamsashen Sharhi daga Imam Saeed Abubakar

Yana da gayar Muhimmanci mu saurari wannan jawabin

20/06/2025

Rikicin gabas ta tsakiya: Tsakanin Iran da Isra'el (Part 1)

Gamsashen Sharhi daga Imam Saeed Abubakar

10/03/2025

Tafsir 03 (2025) Tare da Imam Abubakar Sa'id

Want your school to be the top-listed School/college in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Katsina