Katsina Focus

Katsina Focus

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Katsina Focus, College & University, Katsina metropolis, Katsina.

15/01/2023
30/12/2022

Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta fitar da Ranakun da zatayi gangamin yakin neman zaben ta, a kananan hukumomin dake jihar.

Photos from Katsina Focus's post 30/12/2022

Adam Musa Bindawa

ASLAM ALAIKUM
Barkanmu da lokaci da fatan alkhairi, munada kaji Broilers na siyarwa yan sati 5, location Bindawa katsina state, muna maraba da siyan daya ko sari.
Allah tabbatar mana da alkhairi Amin.

Photos from Katsina Focus's post 29/12/2022

Dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umaru Radda, ya jaddada kudirinsa na shigewa gaba wajen yaki da rashin tsaro a jihar Katsina.

Dr. Radda ya yi wannan ikirari ne a lokacin da yake ganawa da dimbin jama’ar da s**a tarbe shi a karamar hukumar Safana a ci gaba da gudanar da gangamin yakin neman zaben 2023, a yau Alhamis, 29/12/2022.

Dr. Radda ya jagoranci tawagar yakin neman zaben tun daga Katsina zuwa Zakka domin ziyartar fadar Gatarin Katsina, Hakimin Zakka, daga Zakka zuwa Kukar Samu ta garin Batsari, daga Kukar Samu zuwa Babban Duhu, Daga Babban Duhu, Dr. Radda ya jagoranci tawagar kamfen din zuwa garuruwan Baure, Ummadau, Tsakiya, R***a inda daga karshe kuma ya tsaya a filin taron gangamin kamfen a garin Safana.

A lokacin da ya isa garin Tsaskiya, ya bayyana ma al'umma cewa, sun zo ne domin ganin halin da suke ciki domin kuwa an shaida masu cewa ba zasu iya zuwa ba saboda babu tsaro, amma ya tabbatar da cewa in dai akwai alumma a garin, to babu abun da zai hana su zuwa in dai da gaske yana San shugabancin Katsina.

A duk wuraren da ya ziyarta Dr. Radda ya bayyana cewa duk wani shugaban da zai yi yaki da matsalar rashin tsaro da jihar ke fama da shi, dole ne ya kuduri aniyar shigewa sahun gaba a fagen daga. Ya bayyana yaki da rashin tsaro a matsayin wani nauyi daya rataya a wuyan kowa, don haka akwai bukatar hadin gwiwa tare da yin nuni da cewa dole ne kowa da kowa ya tashi tsaye domin samun nasara a wannan fanni.
Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC ya bada tabbacin inganta harkar noma tare da samar da kananan sana'o'i domin samar da ayyukan yi ga matasa da mata a fadin jihar nan.


Photos from Katsina Focus's post 29/12/2022

Dazu dazun nan.....

Sheik Tijjani Shehul Hadi Murtania, daya daga cikin manyan 'Ya'yan shugaban Darikar Tijjaniyya na Duniya, yana sanyawa H.E. Abba Gida Gida albarka a yammacin yau Alhamis.....

Allah ya amsa adduoin fatan alheri da samun nasarar da Shehi yayi, amin.

Usman Kwankwason Rijiyar Lemo

Photos from Katsina Focus's post 29/12/2022

MANGAL CEMENT

An cigaba da Gina Katafaren Kamfanin Cement na Dan asalin Jihar Katsina Shugaban Rukunin Kamfanin Max air da Afdin Alh Dahiru Bara'u Mangal.

Wanda yanzu haka ya Kai kashi 30%, Wanda ake Saran kammalashi zuwa karshen shekarar 2023.

Photos from Katsina Focus's post 29/12/2022

Samun Dr.Mustapha Muhammad Inuwa a PDP ba karamin alkairi bane ga jam'iyyar a karamar hukumar Danmusa dama jihar katsina baki daya.
Inji.Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na shiyyar katsina Alh.Lawal Mai-Iyali.

Ibrahim Nasir Faskari
Mobile Media Crew

Alh.Lawal Mai-Iyali ya fadi hakane a ranar alhamis 29-12-2022 a garin Yantumaki lokacin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP na karamar hukumar Danmusa.

Yacigaba da cewa"muna da yakinin insha Allah Dr.Mustapha zai zaima alkairi ga al'ummar wannan yanki namu da ma katsina baki daya.Kuma mu a Danmusa yanzu babu abinda zamu ce sai dai Allah ya bamu zaman lafiya.

Sannan mu cigaba da addu'a Allah ya hada kawunan shuwagabannin mu na jam'iyyar PDP domin wannan ita kadai ce matsalar mu wadda yan jam'iyyar Apc suke jima dadi,kuma sa ran zuwan ta karshe insha Allah.

Shima dayake gabatar da jawabinsa dan takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Batsari, Safana, Danmusa Hon.Aliyu Iliyasu Rumah ya bayyana cewa"mu yan jam'iyyar PDP babu abinda ke gabanmu face mu fito mu jefa kuru'a kawai.

Kada kuyi la'akari da jam'iyyar Apc ta gaza ko wani abu mai k**a da haka.Da wannan nike tabbatar maku idan har Allah ya bamu wannan dama zamuyi duk abinda ya k**ata domin kyauta ta maku ta kowane fanni.

Daga karshe inaso in tabbatar yanzu mun kara samun karuwa,wadda wannan ba karamar karuwa bace ta samun Dr.Mustapha Muhammad Inuwa.

Shima a nashi jawabin dan takarar kujerar majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Danmusa Hon.Bishir Atiku Mai-dabino ya bayyana cewa"wannan taro da muka hadu ko ba komai mun kara zumunci a tsakaninmu.

Kiran da zanyi shine halin da ake ciki a Batsari, Safana, Danmusa abune mara dadin ji ke faruwa,wanda idan ba munzo mun karya wannan jam'iyya ta Apc ba bazamu koma cikin hayyacinmu ba.

Mutane da dama ne s**a tofa albarkacin bakinsu a wurin taron daga ciki akwai shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Danmusa Alh.Mustapha Abdullahi,Alh.Aminu Abubakar Yantumaki, shugabar mata Binta

Photos from Katsina Focus's post 29/12/2022

Dr. Dikko Umar Radda Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin tutar Jam'iyyar Apc, a karamar hukumar Safana yakin neman zabe

Photos from Katsina Focus's post 29/12/2022

Yadda bomb yatashi an ajiye mota ne ba,asan Wanda ya ajeta ba jin kadan kafin Buhari ya iso kawai bomb din yatashi an rasa rai na mutum 4 a wajen Allah kiyaye gaba.

Photos from Katsina Focus's post 29/12/2022

Dikko/Jobe Consultative Forum Karkashin Jagorancin Hajiya Hauwa Umar Radda
28/12/2022

Kungiyar ta Dikko/Jobe Consultative Forum ta ziyarci garin yan'daki tare da karamar hukumar Kaita, inda ta gana da mata da s**a amfana da tallafin gwamnatin APC.Matan sun jaddada goyon bayan su ga Dan takarar Gwamnan Jahar Katsina Dr Dikko Umar Radda a Karkashin tutar jam'iyyar APC.

Datake gabatar da jawabi Shugabar Hajiya Hauwa Umar Radda tayi kira ga Al'ummar ta garin Kaita dasu bayar da gudummuwa wajen shiga lungu da Sako dan nema ma jam'iyyar ta APC kuri'u a zaben 2023.

Hajiya Halima Shehu K/dangi ta bayyana matan sun amfana da tallafin gwamnatin tarrayya Wanda aka bude masu asusun banki tare da bayar da tallafin na kudi ga ko wannen su. Haka zalika sun bayar da tallafi daban daban Kuma s**an zo domin yimasu wa'azi duba lafiyar su da sauran abubuwar arziki don inganta rayuwar su

Tafiyar ta samu rakiyar malaman da'awa da sauran magoya bayan jam'iyyar ta APC don ganin samun nasarar jam'iyyar ta APC a zaben 2023 Mai gabatowa

29/12/2022

Kadan daga shirin labarina na gobe jumaa.

Want your school to be the top-listed School/college in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Katsina Metropolis
Katsina