28/12/2024
Wani Ƙaramin Labari Mai Darasi.
Wani yaro ya je wurin tsohon kakansa ya ce,
"Kakalle, za ka iya bani labari mai darasi na rayuwa?"
Tsohon kakansa ya ɗan yi tunani na ɗan lokaci, sannan ya gyara murya ya ce,
"Zo ka zauna ka saurari wannan labarin."
Ya fara da cewa:
"Akwai wata makauniya mai suna Sarah. Lokacin tana ƙarama, iyayenta sun rasu a wani hatsarin mota wanda ya kuma sa ta rasa ganinta. Kakarta ta ɗauke ta daga birni zuwa ƙauye, ta raineta. Sarah ba ta da abokai ko abokan hira. Abokiyar zaman ta kawai ita ce sandanta. Wannan sanda ta taimaka mata sosai. Ta kasance tana amfani da ita wajen yawo a wajen ta, tana zuwa wurare ba tare da ta dogara da wani ba. Sandan ba ta taɓa yi mata hukunci ba. Ba ta taɓa kushe ta ko ɓata mata rai ba. Sandan koyaushe yana sa ta murmushi.
Daga baya, wani hamshakin mai arziki mai kyau ya kamu da kaunar Sarah, ya yanke shawarar aurenta. Ya kai ta wata asibiti mafi kyau a ƙasar don a gyara mata gani. Da sa’a, aikin ya yi nasara, Sarah ta fara gani a karo na farko. Wannan shi ne ƙarshen labarina...”
Yayin da tsohon ya dakata, yaron ya ɗan yi murmushi amma yana jin mamaki ya ce,
"Amma, kakalle, babu wani darasi a wannan labarin. Babu abin da zan koya daga ciki."
Tsohon ya yi dariya sannan ya ce"Bari in gaya maka wani abu. Lokacin da Sarah makauniya ta sake ganin haske, ta yar da wani abu. Ka san me ta yar?"
Yaron ya yi tunani na ɗan lokaci sannan ya girgiza kai, ya ce,
"Ban sani ba... ka gaya min."
Tsohon ya yi murmushi sannan ya ce,
"Ta yar da sandanta. Sandar da ta taimaka mata duk tsawon rayuwarta. Sandar da ta kasance abokiyar zamanta. Saboda kawai ta fara gani, ta manta da abin da ya tsaya mata da ya taimaka mata lokacin da babu wanda ya yi haka. Ta manta komai game da alherin sandar."
A nan ne tsohon kakansa ya dafa kafadar yaron, ya yi ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa,
"Ka saurara, yaro... haka rayuwa take. Gaskiyar rayuwa ita ce, mu kan daina tunawa da mutane lokacin da ba su da amfani a gare mu. Babban kuskuren da muke yi shi ne mantawa da waɗanda s**a tsaya tare da mu lokacin da rayuwarmu take cikin duhu. Ayyukansu da sadaukarwarsu suna da daraja sosai, amma sau da yawa muna rasa damar biya musu. Mun manta sadaukarwar da iyayenmu s**a yi don mu. Har ma da ‘yan’uwanmu, abokanmu, da waɗanda s**a taimake mu a baya, ba mu taɓa tunanin biyan alherinsu ba.
Ga babban darasin: Kada mu taɓa mantawa da waɗanda s**a taimake mu lokacin da muke cikin buƙata. Mu ji alfahari da kasancewa tare da su, mu haɗa su cikin rayuwarmu. Duk wani abu na alheri da muka yi wa wasu, tabbas zai dawo gare mu. Wannan shi ne ƙarfin tunawa da alheri.”
Fatima Abdurrahman Mck