05/12/2025
Assalamu Alaikum.
Barka da zuwa.
TSARE-TSAREN GUDANARWA NA MAKARANTA
*TSARIN TUFAFIN MAKARANTA:*
*Maza:*
- Farar Riga Dunkin Pakistan, ta wuce guiwa.
- Wando Baki.
- Hula Baka mai Ratsin Fari.
*Mata:*
* Farar Riga ta kawo ga guiwa.
* Wando Baki.
* Hijabi fari Rabin Kwauri.
* Safa Baka
*Abin Lura:*
A hannun Makaranta ne kawai ake siya da kuma dunka Tufafin Makaranta, don gujewa samun banbanci.
*MANUFOFIN MAKARANTA:*
◾Samarda Yara Masu Ƙananan Shekaru Mahardata Alqur'ani Mai Girma Tare Da Ingantaccen Ilimin Addini.
◾ Inganta Tarbiyyar Yara Bisa Ga Tsari Na Addinin Musulunci.
◾Koyawa Yara Sana'o'in Dogaro Ga kai.
*HANYOYIN CIMMA WAƊANNAN MANUFOFIN:*
Domin Cimma Wadannan Manufofin Mun:
◾Samarda Malamai Mahardata Alqur'ani Kuma Masana Ilimomin Addinin Musulunci.
◾Mun Ƙulla Alaqa Da Masu Sana'o'i Daban-daban.
*KASHE-KASHEN ƊALIBAI:*
◾Ɗaliban Din-Din-Din (Permanent Students)
◾Ɗaliban Lokutan Hutun Boko (Vocational Students)
*SASHEN KARATU:*
◾ NURSERY (Yadda za a reni yaro ta hanyar lakkana masa Alqur'ani)
◾NAZARI (Karatun Sauka, Ma'ana Yadda Ɗalibi Zai Iya Karatun Alqur'ani Da Tajweedinsa)
◾TAHFEEZ (Haddar Alqur'ani Mai Girma)
*ZANGON KARATU:*
◾First Term (January---April)
◾Second Term (May---August)
◾ Third Term (September---December)
*DARUSSAN DA MUKE KOYARWA:*
◾Qur'an
◾Tajweed
◾Hadith
◾Tauhid
◾Fiqhu
◾Seerah
◾Arabiyyah
◾Huruf
◾Khaddul Araby
*KARANCE-KARANCE NA DABAN*
* Gudanarda Karance-Karance na Nishadi a karshen kowane zangon Karatu.
* Gudanarda Gasar Karatun Alqur'ani a tsakanin Dalibai (Karshen Zango na 2).
* Gudanarda Jarabawar gwaji (C.A) Karshen zangon Karatu na 1 da na 2.
* Gudanarda Babbar Jarabawa a karshen kowace shekara.
* Halartar Musabakar Gwamnati don karfafa karatun yara.
*RANAKU DA LOKUTAN KARATU:*
◾Assabar: 08:00am - 08:00pm (Daliban Hutu Kawai) 2:30PM - 06:30PM (Sauran Dalibai)
◾Lahadi: 08:00am - 08:00pm (Daliban Hutu Kawai) 2:30PM - 06:30PM (Sauran Dalibai)
◾Litinin: 02:30PM Zuwa 06:30PM
◾Talata: 02:30PM Zuwa 06:30PM
◾Laraba: 02:30PM Zuwa 06:30PM
*KUDIN MAKARANTA (SCHOOL FEES):*
KUDIN FORM: N1,000
◾Ɗalibin Din-Din-Din (Permanent Student):
- First Term: N5,000
* Second Term N5,000
* Third Term N5000
*TOTAL: N15000*
◾Ɗalibin Hutun Boko (Vocational Student):
* First Term: N10,000
* Second Term N10,000
* Third Term N10,000
*TOTAL: N30,000*
*DOMIN ƘARIN BAYANI:*
📞 08108115099, 08132534671, 07087106871.
*_Domin Koyon Karatun Alqur'ani Da Haddar Sa, Gare Ka Ko Ga Ƙanen Ka/Ƙanwar Ka, Ko Ɗan ka/Ƴar ka, Muna Maraba Da Dalibai A Kowanne Lokaci!._*