Kabara Community Security, Education & Development Association

Kabara Community Security, Education & Development Association

Share

Manufar Ƙungiyar KCSEDA

Kabara Community Security, Education & Development Association (KCSEDA)

an

10/03/2026

PRESS RELEASE

SANARWA KAN CI GABAN BINCIKE A KAN KISAN HALIFA (CHURI)

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu.

Ƙungiyar Kabara Community Security, Education & Development Association (KCSEDA)

na sanar da dukkan mambobinta da al’ummar gari halin da ake ciki dangane da binciken da ake gudanarwa kan mummunan lamarin kisan Halifa (Churi) tare da jikkatar wasu daga cikin al’ummar unguwarmu.

Bayan ƙungiyar ta miƙa takardar ƙorafi ga hukumar ‘yan sanda domin a buɗe cikakken bincike kan wannan lamari mai tayar da hankali, muna farin cikin sanar da cewa an fara samun gagarumin ci gaba a binciken.

A ranar 07 ga Maris, 2026, jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya rashi jahar Kano sun samu nasarar k**a wani wanda ake zargi da hannu a cikin wannan lamari.

A halin yanzu, ana tsare da wanda ake zargin a Sashen Binciken Kisan Kai (Homicide Section) na Bompai Police Headquarters, inda ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano dukkan waɗanda ke da hannu a cikin wannan laifi.

Ƙungiyar KCSEDA na yaba wa jami’an tsaro bisa gaggawar da s**a nuna wajen ɗaukar mataki da kuma ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da adalci.

Muna kuma tabbatar wa al’umma cewa ƙungiyarmu za ta ci gaba da bibiyar wannan lamari da matuƙar kulawa har sai an tabbatar da cikakken adalci ga marigayi Halifa (Churi) da kuma waɗanda s**a jikkata.

Haka kuma muna kira ga dukkan mambobin ƙungiya da al’ummar yankin da su kasance masu haƙuri, kwanciyar hankali da bin doka, tare da bai wa hukumomin tsaro cikakken haɗin kai domin samun nasarar binciken.

A ƙarshe, muna godewa Allah Maɗaukakin Sarki bisa wannan muhimmin ci gaba, tare da roƙonSa Ya tabbatar da adalci, tsaro da zaman lafiya a cikin al’ummarmu.
Issued by:

Comrade Yahaya Yau Abdullahi

Secretary General
Kabara Community Security, Education & Development Association (KCSEDA)
Date: 08 March 2026

04/03/2026

SANARWAR YABO DA GODIYA

Rana: 4 ga Maris, 2026

Kabara Community Security, Education and Development Association

Kabara Community Security, Education and Development Association na miƙa saƙon yabo da godiya ta musamman ga

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano,

Cp Ibrahim Adamu bakuri

Mataimakinsa, AC CID,

da dukkan jami’an rundunar da s**a bayar da gudummawa wajen buɗe bincike kan kisan gillar da aka yi wa Chure a Unguwar Kabara.

Hakika, wannan mataki abin a yaba ne ƙwarai da gaske, domin ya nuna jajircewa,

kishin aiki, da ƙudurin tabbatar da adalci.

Karɓar ƙorafin da aka shigar hannu bibbiyu tare da ba da damar gudanar da bincike cikin gaskiya da doka ya ƙara tabbatar da aniyar tabbatar da adalci ga al’umma.

Haka kuma, muna miƙa saƙon yabo na musamman ga Global Community for Human Rights Network, wacce a ƙarƙashin kulawarta aka shigar da ƙarar tare da bibiyar lamarin domin tabbatar da adalci.

Gudummawar da ƙungiyar ta bayar wajen kare haƙƙin ɗan Adam da tsayawa kan gaskiya abin a yaba ne matuƙa.

Muna addu’ar Allah Ya ƙara wa jami’an tsaro da dukkan masu ruwa da tsaki basira, ƙarfi, da nasara wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano.
Sa hannu:

Usaman Zunnuraini
Shugaban Ƙungiya

Kabara Community Security, Education and Development Association

Mun gode.

23/02/2026

Kabara community security education development association ta mika kukenta ga kwamashina Yansanda jahar Kano bisa kurafi kisan gillar da aka yiwa daya daga cikin ƴan kwamatin Kabara da jikata mutum uku dan yin bincike da dauka mataki shari'ar kan wanna mumuna lamari da yafaru

21/02/2026

Wanna kungiyar tana taya al umma musulmai murnar shigowar watan Ramadan mubarek da fatan Allah yakarbi ibadun mu yabiya mana bukatu

21/02/2026

🔥🚨 SANARWA MAI MUHIMMANCI GA DUKKAN AL’UMMA 🚨🔥

Ku saurara da kyau!!!
Kabara Community Security, Education & Development Association (KCSEDA)

na sanar da daukacin al’umma cewa gobe Insha’Allah za a yi wata muhimmiyar

tattaunawa kai tsaye da PRO na kungiyar,

Haruna Salisu Sa’ad, a manyan gidajen rediyo — Dala FM, Freedom

Radio da sauran kafafen yada labarai.
⚠️ Za a bankado

muhimman batutuwa kan ayyukan kungiyar, tare da bayani dalla-dalla kan matakin da aka dauka na kai korafi ga Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano dangane da

mummunan kisan gillar da aka yi wa daya daga cikin matasan unguwarmu.

⏰ Kada ku bari a baku labari!

👉 Ku saurara domin jin gaskiya kai tsaye.

Lokaci ya yi da al’umma za su san abin da ke faruwa!!!

Allah Ya kare mu, Ya tabbatar da adalci da zaman lafiya. 🤲

Photos from Kabara Community Security, Education & Development Association 's post 19/02/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI

KABARA COMMUNITY SECURITY, EDUCATION & DEVELOPMENT ASSOCIATION (KCSEDA)

Kungiyar Kabara Community Security, Education & Development Association (KCSEDA)

ta gabatar da korafi a hukumance ga

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano,

Cp Ibrahim bakuri

tana mai kira da a gaggauta gudanar da cikakken bincike kan kisan daya daga cikin ’yan kwamitin Kabara tare da jikkata wasu mutane biyu,

sak**akon rikicin fadan daba da ya barke tsakanin Kabara da Magashi.

Tun bayan faruwar wannan lamari, kungiyar ta dauki alkawarin bibiyar lamarin domin tabbatar da an gano wadanda s**a aikata wannan danyen aiki

tare da gurfanar da su a gaban kuliya domin a yi musu hukunci bisa doka.

A ranar 18 ga Fabrairu, 2026, kungiyar ta shigar da korafi a hukumance ta hannun lauyan kungiyar kuma lauya daga ƙungiyar kare hakkin dan Adam ta

Global Community for Human Rights Network,

tare da shugaban kungiyar, Kabara community da sakataren kungiyar da pro

inda s**a mika takardar karar ga Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano domin neman adalci da kare hakkin wadanda abin ya shafa.

KIRAN GAGGAWA GA HUKUMOMIN TSARO DA GWAMNATIN JIHAR KANO

Kungiyar na kira cikin gaggawa ga

hukumomin tsaro da gwamnatin Jihar Kano da su fito da gaskiya

ba tare da jinkiri ba kan waɗan da ake zargi sun shiga Kabara,

s**a aikata kisan gilla ga yara marasa laifi — yara da ba su aikata wani laifi ba.

Wadanda aka kashe sun hada da:

Halifa Churi — ɗan kwamitin Kabara, mara laifi.

Ɗan Malam — malamin makarantar allo, mai tarbiyyar yara.

Akilu — matashi mai neman halal domin rayuwarsa.

Wadannan ba ’yan daba ba ne, ba masu tada fitina ba ne — ’ya’yan talakawa ne masu neman na kansu da gina makomarsu.

Kungiyar ta jaddada cewa ba za a lamunci amfani da kakin gwamnati wajen cutar da al’umma ba, tare da bayyana wannan lamari a matsayin zalunci da kisan gilla, ba aikin tsaro ba.

BUKATUN KUNGIYAR
Kungiyar na neman:

A fito da cikakkiyar gaskiya kan abin da ya faru

A gano wadanda s**a aikata ake zargi da aikata laifin

A hukunta su bisa tanadin doka

A ba iyalan wadanda aka kashe adalci da diyya

Rayuwar talaka ba abin wulakanci ba ce.

Adalci dole ne ya tabbata.

An fitar da wannan sanarwa ne daga:

Kabara Community Security, Education & Development Association (KCSEDA)

11/02/2026

Liman Malam Yahaya lawan Husaini kabara kenan da kungiyar Kabara community security education ta ziyarta a yau Alhamis

11/02/2026

Malam darja kenan da kungiyar Kabara community security education ta kaiwa ziyara a Yau Alhamis

11/02/2026

Ziyarar da yan kungiyar Kabara community security education kenan da s**a fara kaiwa man yan mutane da malamai na unguwar Kabara a yau Alhamis

08/02/2026

Al ameen Tahir Ahmad pro ll

08/02/2026

Zukirullah Ismail mataimakin ma ajin kungiyar

08/02/2026

Ashiru sani saminu ma ajin kungiyar

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address

Kano
Kano
KABARA