13/04/2026
GOBA Celebrates Patron, Prof. Hafiz Abubakar, on Prestigious Global Fellowship
The Gwale Old Boys Association (GOBA) has congratulated its Patron, Professor Hafiz Abubakar, on his selection as a Fellow of the International Academy of Food Science and Technology.
In a statement issued on Monday, 13th April 2026, the President of GOBA, Mohammed Mukhtar Idris, speaking on behalf of the executives and all class chapters of the Association, described the honour as a well-deserved recognition of Prof. Abubakar’s exceptional contributions to food science, research, and innovation at both national and international levels.
The Association noted that Prof. Abubakar, a former Deputy Governor of Kano State and current Chairman of the Northwest University Governing Council, has consistently demonstrated dedication, hard work, and a strong commitment to advancing scientific knowledge, particularly in the field of food science and technology.
GOBA further expressed pride in his achievement, stating that his recognition would serve as a source of inspiration to young academics and researchers across Kano State to pursue excellence in their respective fields.
Prof. Abubakar was among 27 distinguished scientists from 15 countries selected by the International Union of Food Science and Technology for the 15th class of the Academy. He is expected to be formally inducted in October 2026 during the World Congress of Food Science and Technology in Hong Kong.
By Dr Nura Garba, National Publicity Secretary, GOBA
04/04/2026
*An saka Fitilun Solar Guda 20 a cikin Makarantar Gwale*
A sakamakon korafi da shugabancin GOBA na kasa ya kai ga mai girma Sanatan Kano ta tsakiya abisa rashin haske a cikin makarantar Gwale, a yanzu mai girma Sanata Rufai Sani Hanga ya kawo fitilun titina na solar guda ashirin kuma duk an sakasu a sassa daban na wannan makaranta.
Makaranta a yanzu ta haskaka da dare, kuma hakan zai rage barazanar tsaro a cikin wannan makaranta.
Dr Nura Garba
National Publicity Secretary
08/03/2026
Tsofaffin Daliban GOBA na Shekarar 1984 Sun Bai wa Iyalin Marigayun Abokan Karatu Tallafin Kudi da Kayan Abinci
Mambobin ajin shekarar 1984 na Kungiyar Tsofaffin Daliban Gwale (GOBA) sun bai wa iyalan abokan karatunsu da s**a rasu tallafin kudi da kayan abinci, a wani yunkuri na ci gaba da karfafa dankon zumunci a tsakanin mambobin kungiyar.
An gabatar da tallafin ne a lokacin taron buda baki na shekara-shekara da ajin ke shiryawa, inda mambobin s**a kuma yi amfani da damar wajen tunawa da abokan karatunsu da s**a rasu tare da yi musu addu’a.
Shugaban ajin na shekarar 1984 kuma Shugaban kungiyar GOBA na kasa, Alhaji Muhammad Mukhtar Idris, ya yabawa mambobin ajin kan yadda s**a ci gaba da rike al’adar tallafawa iyalan abokan karatunsu da s**a rasu.
Da yake zantawa da Jegus Online TV a wajen taron, Alhaji Muhammad Mukhtar Idris ya bayyana cewa taron ba wai don karfafa hadin kai tsakanin mambobi kadai aka shirya shi ba, har ma don nuna tausayi da kulawa ga iyalan abokan karatu da s**a rasu.
Ya kara da cewa ajin ya dade yana bai wa irin wadannan iyalai tallafin kudi da kayan abinci, musamman a cikin watan Ramadan mai alfarma.
A cewarsa, wannan shiri yana nuna irin zumunci mai karfi da kuma alhakin da mambobin ajin s**a ci gaba da dauka tun daga lokacin da suke makaranta tare.
Ya ce, “A matsayinmu na ‘yan’uwa da muka yi makaranta tare kuma muka raba abubuwan tunawa iri daya, alhakinmu ba ya karewa bayan mun kammala karatu. Dole ne mu ci gaba da kula da juna tare da tunawa da iyalan wadanda ba sa tare da mu a yau.”
A yayin taron, kungiyar ta mikawa wasu daga cikin iyalan abokan karatu da s**a rasu tallafin kudi da kayan abinci, tare da taimakawa wasu marasa galihu.
Wadanda s**a amfana da tallafin sun bayyana godiyarsu ga kungiyar, suna mai cewa tallafin ya zo a kan lokaci kuma ya karfafa musu gwiwa, musamman a wannan lokaci na watan Ramadan.
Wasu daga cikin mambobin da s**a yi jawabi a wajen taron sun jaddada muhimmancin ci gaba da wannan shiri, tare da kira ga sauran kungiyoyin tsoffin dalibai da kungiyoyin al’umma da su yi koyi da irin wannan aiki domin karfafa tsarin taimakon juna a cikin al’umma.
Taron buda bakin na shekara-shekara ya hada mambobin ajin shekarar 1984, shugabannin al’umma da baki na musamman, inda aka yi addu’o’i, da kuma sabunta kudurin tallafawa juna.
An rufe taron da addu’o’i ga rayukan abokan karatunsu da s**a rasu tare da fatan dorewar hadin kai da ci gaban mambobin kungiyar.
22/02/2026
Yadda daliban makarantar Gwale bangaren Woodwork s**a gyara bencina da kujerun makarantar Gwale Secondary School.
Wannan ya nuna daliban sun samu sana'ar yi tun kafin su gama makarantar.
10/02/2026
In pictures: Government Secondary School Gwale Students during Jamb CBT Orientation ceremony Organized by Corps Members and the management of the school
11/01/2026
Wasu hotunan Taron AGM na GOBA 2025 kenan
06/01/2026
GOBA tana godiya ga Nasir Mikdad Class 1994
Shugabancin GOBA yana mika godiya ga Nasiru Mikdad Dan aji na 1994 abisa tagomashi da yayi na daukar nauyin biryan mai gadi har na tsawon shekara daya.
A baya bayannan a wajen taron AGM na GOBA 2025 Air Commodore Mustapha Suleiman shima Dan class 94 ya ce zai dauki nauyin mai gadi guda daya, inda zai biya kudin albashinsa na shekara daya.
Shi ma yanxu Nasiru Mikdad ya dauki nauyin biyan days mai gadin har tsawon shekara daya.
Shugaban na GOBA, Alhaji Mukhtar Idris Diso yayi murna matuka da gaske, kuma ya godewa Yan class 1994 da irin wannan gudunmawa da suke bawa makarantar Gwale.
29/12/2025
Air Commodore Mustapha Suleiman ya bawa GOBA Gudunmawar Naira Miliyan Daya
Air Commodore Mustapha Sulaiman dan aji na 1994 ya bawa kungiyar tsofaffin dalibai na makarantar Gwale wato Gwale Old Boys Association (GOBA) gudunmawar Naira Miliyan Daya a wajen taron karshen skehara wato Annual General Meeting (AGM) wanda akayi a ranar Lahadi 28 ga watan Disamba 2025.
Air Commodore Suleiman na 455 Airforce Base Kano yace ya bada gudunmawar kudi Naira dubu dari uku 300,000 domin biyan masu gadi, dubu dari biyu domin gyaran motar data lalace ta makarantar Gwale, sai kuma Naira dubu dari biyar ga kungiyar tsofafin dalibai domin gabatar da ayyukanta na yau da gobe.
Air Commodore yaci alwashin cigaba da bawa wannan makaranta gudunmawa ta kowace hanya.
28/12/2025
*GOBA Holds 2025 Annual General Meeting*
The Gwale Old Boys Association (GOBA) on Sunday, 28th December 2025, held its Annual General Meeting (AGM), which also featured the presentation of certificates to deserving members.
The National President, Alhaji Mukhtar Idris, welcomed participants and highlighted the significant achievements recorded by the association since the current leadership assumed office.
In his remarks, Air Commodore Mustapha Sulaiman reaffirmed his continued support and commitment to initiatives aimed at advancing the school.
The Secretary, Muhammad Hamza Daneji, presented a comprehensive report on the activities and progress of the association.
The meeting attracted a wide range of members and stakeholders, including traditional rulers, civil servants, and business leaders, reflecting the unity and growing strength of the association.
28/12/2025
A Yau Lahadi 28 ga watan December 2025 zaayi Taron tsofaffin dalibai na makarantar Gwale wato Annual General Meeting (2025) da misalin karfe 10:30 na safe a babban dakin taro na makarantar Gwale.
Don haka ana gayyatar duk ilahirin tsofaffin dalibai na wannan makaranta domin su halarci wannan taro.