Majigi TV .

Majigi TV .

Share

MAJIGI TV – Muradin Kallo na Hausawa
Tashar nishaɗi da ilimi cikin Hausa. Muna kawo barkwanci, gajerun fina-finai, labarai da shirye-shirye masu amfani.

Ku bi shafin mu domin kada ku rasa sabbin bidiyo.
📞 WhatsApp: 0#########

19/03/2026
13/03/2026
Photos from Majigi TV .'s post 16/02/2026

PRESS STATEMENT
On the Recent U.S. Congress Bill, False Claims of “Christian Genocide” in Nigeria,
and the Targeting of Senator Rabiu Musa Kwankwaso
The Supreme Council for Shari’ah in Nigeria (SCSN) has followed with grave concern the
recent bill and public narratives attributed to elements within the United States Congress,
falsely alleging the existence of a “Christian genocide” in Nigeria and, most astonishingly,
singling out Senator Rabiu Musa Kwankwaso as a supposed enabler of such claims.
1) The Council states, without equivocation, that there is no Christian genocide in
Nigeria. While Nigeria undeniably faces severe security challenges, including
terrorism, banditry, and organized criminal violence, these crimes are not driven by
a state policy or religious agenda of extermination. The reduction of Nigeria’s
complex security crisis to a simplistic and emotive genocide narrative is not only
false but dangerously irresponsible.
2) The Council finds it deeply troubling that such far-reaching legislative and policy
positions appear to be informed by poorly generated, sensational, and unreliable
data, including narratives reportedly referenced by the New York Times, allegedly
sourced from individuals with toxic mindsets and little understanding of Nigeria’s
conflict dynamics. The absurdity of relying on commentary attributed to a trader in
Onitsha, lacking any expertise in security analysis, underscores the unseriousness
of the foundation upon which these grave accusations were based.
3) More disturbing still is the awkward and reckless call by the Nigerian First Lady,
for increased U.S. bombing in Northern Nigeria. The Council condemns such
statements in the strongest terms. Calls for foreign military bombardment of civilian
majority Muslim populated regions betray a shocking insensitivity to human life
and ignore the catastrophic humanitarian consequences such actions would entail.
Nigeria does not need prescriptions that risk turning criminal violence into largescale civilian tragedy. The Council is not opposed to seeking genuine international
assistance, whether technical, intelligence-based, economic, or humanitarian, in
order to decisively end insecurity. But the Council categorically rejects are illinformed, militaristic, and punitive approaches driven by false narratives rather than
facts and local realities.
4) The Council further finds it inexplicable and unjust that, among Nigeria’s vast
political class, many of whom live extravagantly from the plunder of public
resources, only Senator Kwankwaso was singled out in the bogus US legislation.
The real tragedy Nigeria faces is the systematic devastation of its economy, which
has plunged millions into poverty and hopelessness, thereby fuelling crime and violence. To ignore this structural reality while scapegoating one individual reflects
bias, not justice. The Council totally condemns the unfair denigrate of Senator Rabiu
Musa Kwankwaso to further an ethnic or political agenda.
5) Indeed, the Council notes that the only real “crime” of Senator Kwankwaso in the
eyes of his detractors is his principled opposition to the jaundiced designation of
Nigeria as a Country of Particular Concern (CPC), premised on the same false
genocide narrative the Council and all right-minded Nigerians have repeatedly
debunked. His refusal to endorse a label that maligns Nigeria and deepens division
appears to be the true source of his targeting.
6) The Council reiterates its absolute condemnation of terrorism and criminal violence
in all forms in Nigeria, Palestine and anywhere else in the world, in full accordance
with the authentic teachings of Islam, which uphold the sanctity of human life. The
Council acknowledges that criminal killings in Nigeria affect both Muslims and
Christians, but it must be stated clearly that Muslim communities, particularly in the
North, have suffered disproportionately from insurgency and banditry. Any honest
discourse must recognize this shared pain rather than weaponize religion for
political ends.
7) The Council therefore calls on the United States government and its legislature to
exercise restraint, intellectual honesty, and due diligence, engage credible Nigerian
institutions, and abandon narratives that inflame tensions rather than resolve them.
Nigeria requires sincere partnership grounded in mutual respect, not misinformation
that undermines peace and coexistence.

Nafiu Baba Ahmad, mni
Secretary General
Issued this 27th day of Sha‘aban 1447 AH (15th February 2026).

01/11/2025
13/10/2025

Bayanin Shiekh lawan Triumph Bayan Kampala tattaunawa da kwamitin Shura na jihar kano

30/09/2025

Taron Manema Labarai Da Hadakar Kungiyoyin Ahlussunnah Su Ke Gabatarwa Kan Maganganun Da Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Game da Sha'anin Abduljabbar...

22/08/2023

*_MATAR DA BA TA DA AURE, ZA TA IYA SANYA TURARE TA FITA UNGUWA?_*

*Tambaya*

Assalam malam muna san karin bayani akansa turare gamata sufita, wani malami yace wadda ba matar aure ba zata iya sawa?

*Amsa*

Wa'alaikum assalam, To 'yar'uwa ya *HARAMTA* ga mace Baliga ta sanya turare, ta fita unguwaa, saboda fadin Annabi S.A.W : "Duk matar da ta sanya turare, ta wuce ta wani majalisi, to ta zama mazinaciya, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito. A wani hadisin kuma yana cewa: "Duk matar da ta sanya turare, kar ta halarci sallar Isha tare da mu.
Nassoshin da s**a gabata suna haramta sanya turare ga mace balagaggiya idan za ta fita, kuma ba su bambance tsakanin matar aure ba da budurwa ko bazawara, wannan sai ya nuna gamewarsu ga dukkan mata wadanda sharia ta hau kansu, tun da ba'a samu abin da ya kebance wasu nau'i ba, sannan kuma an haramta sanya turaren ne: saboda yana kaiwa zuwa tada sha'awar Maza, wannan kuma baya bambanta tsakanin matar aure da wacce ba ta yi ba

Amma za ta iya sanyawa ta zauna a gida mijinta ya ji kamshi, in ta yi hakan za ta samu lada, haka ma budurwa, za ta iya sanyawa a tsakanin 'yan'uwanta mata, ko gaban muharramanta wadanda ta san ba za su yi sha'awarta ba

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

31/03/2016

Kuyi share A sauran gurare

22/08/2023

*YAUSHE AKE BIYAN WANDA YA YI AIKI LADANSA ?*

*Tambaya*

Assalamu alaiakum Malam idan ka bawa mutum aiki yaushe ya kamata ka biya shi ladan aikinsa ?

*Amsa*

Wa alaikum assalam Ana biyan mutum ladansa daga zarar ya gama aikinsa, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : "Ku bawa dan kwadugo ladansa kafin guminsa ya bushe" kamar yadda Ibnu-majah ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2443, kuma Albani ya inganta shi a Irwa'ul-galil hadisi mai lamba ta : 1498 .
Sannan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana taurin bashi, kamar yadda yake cewa : "Taurin bashin mawadaci zalunci ne, yana halatta mutuncinsa da yi masa ukuba" Bukhari a hadisi mai lamaba ta : 2400.
Don haka ya wajaba mutukar yana da hali, ya biya wanda ya yi masa aiki daga zarar ya gama , kar ya jinkirta .

Allah ne ma fi sani .

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

2/4/2014

Allah kuyi Share A sauran gurare

19/08/2023

HUKUNCI KAYYADE HAIHUWA (FAMILY PLANNING)

Tambaya
Assalamu alaikum.
Shin ko akwai dalilai na shariah da suke halatta mace ta juyar da mahaifarta ko kuma ta samu tazarar haihuwa?

Amsa
Wa alaikumus Salam
To dan uwa amfani da abin da zai kayyade iyali, ya kasu kashi biyu

1. Ya zama zai hana daukar cikin kwata-kwata, a nan bai halatta ba, saboda ya sabawa manufar shari'a na yawaita al’uma, kuma ‘ya’yan da take da su za su iya mutuwa sai ta koma mai wabi.

2. ya zama an tsayar da shi ne na dan wani lokaci, kamar mace ta zama tana yawan haihuwa kuma cikin yana wahalar da ita, sai ta yi nufin ta tsara haihuwarta ta yadda za ta haihu duk bayan shekara biyu ko makamancin haka, to wannan ya halatta in dai miji ya bada izini kuma ba zai cutar da matar ba, dalili akan haka shi ne sahabbai sun kasance suna azalu a zamanin Annabi s.a.w. don kar matansu su dauki ciki, kuma ba’a hana su ba, kamar yadda Bukari ya rawaito daga hadisin Jabir mai lamba ta: 4911.

Abin da ake nufi da azalu shi ne idan namiji yana saduwa da matarsa idan ya ji maniyyi zai fito sai ya fitar da azzakarinsa ya zubar da maniyyin a wajen farji.

Duba Dima'uddabi'iyya na Ibnu Uthaimin shafi na 57.

Duk da cewa na biyun ya halatta, sai dai yarda da cewa kowanne yaro da arzikinsa yake zuwa duniya yana daga cikin Imani, zaton shiga talauci bayan haihuwar 'ya'ya da yawa munanawa Allah zato ne.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
13/7/2014

18/08/2021

INA YA KAMATA NA KALLA A JIKIN BUDURWATA ?

Tambaya:
Assalamu alaikum,
Malam ko ya halatta in kalli gashin macen da nike so in aura? Ko kuma don Allah malam ka taimaka kaman bayanin abunda ya halatta in kalla a jikin macen da zan aura kafin muyi aure. Na gode. Allah ya gafarta maka.

Amsa:
Wa alaikum assalam To dan'uwa ya halatta ka kalli macen da kake so ka aura, kamar yadda ya zo a cikin hadisi, inda Annabi s.a.w. yake cewa : "Idan dayanku yana neman aure, to in ya sami damar kallon abin da zai kira shi zuwa aurenta, to ya aikata hakan" Abu dawud a hadisi mai lamba ta : 2082.

Malamai sun yi sabani akan wurin da ya kamata mutum ya kalla a jikin mace lokacin da ya je neman aure :

*1.* Akwai wadanda s**a ce zai kalli fuska da tafin hannu ne kawai, saboda tafin hannu yana nuna ni'imar jikin mace, kamar yadda fuska take nuna kyau, don haka sai a takaita akan su, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai.

*2.* Zai kalli duk abin yake bayyana a jikin mace, don haka bayan fuska da hannu zai iya kallon duga-dugai da wuya.

*3.* Wasu malaman sun tafi akan cewa : zai kalleta a kayan da take sawa a cikin gida, ta fuskace shi ya kalle ta, sannan ta juya baya ya kalleta.

Wannan ra'ayin shi ne ya fi dacewa, saboda ta haka mutum zai san yanayin matar da zai aura, yadda ya kamata.

Saidai ba'a son yawaita kallon saboda duk abin da aka halatta saboda bukata, to ya wajaba a tsaya a gwargwadonta, wannan yasa yawaita zuwa zance da yawaita yin waya, zai iya zama haramun saboda yana iya tayar da sha'awa, sha'awa tana iya kaiwa zuwa barna.

Allah ne mafi sani

Don neman Karin bayani, duba : Al'insaf 8\15 da Muhallah 9\161.

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
12/04/2013

30/07/2021

AZUMIN NAFILA RANAR ASABAR !

Tambaya :
Dr maganar azumi wani malami yace : indai kamata ne mutum yayi Alhamis da Juma'a, don anyi hani da yin azumi ran sati ?

Amsa :
To 'yar'uwa hadisi ya zo daga Annabi s.a.w cewa : "Kada ku yi azumi ranar asabar sai abin da aka farlanta muku" Abu-dawud hadisi mai lamba ta :2423.
Saidai malamai sun yi sabani akan ingancin wannan hadisin, akwai malaman da s**a tafi akan cewa hadisin karya ne, Abu-dawud ya hakaito hakan daga Imamu Malik.
Akwai wadanda s**a ce hadisin akwai kuskure a ciki, saboda ya sabawa hadisin da ya fi shi inganci, inda Annabi yake cewa : "kada dayanku ya azumci ranar juma'a, sai in ya azumci yinin da yake gabaninta, ko kuma wanda yake bayanta" Bukhari a hadisi mai lamba ta : 1884, wannan hadisin yana nuna halaccin azumtar asabar ga wanda ya azumci juma'a.
Akwai malaman da s**a tafi akan cewa hadisin ya inganta saidai an goge shi da wasu hadisan, saboda yadda aka rawaito cewa annabi yana azumtar mafi yawan Sha'aban, wannan sai ya nuna cewa dole asabar ta fado a cikin azuminsa, ga shi kuma Annabi s.a.w. ya halatta irin azumin Annabi Dawud, wanda za ka yi azumi yau ka sha gobe, babu yadda za'a yi mutum ya yi azumin Annabi Dawud ba tare da Asabar ta fado a cikin azuminsa ba.
Zancen miliyoyin malamai shi ne ya halatta ayi azumi ranar asabar ga wanda ya yi azumi ranar juma'a.
Don neman karin bayani duba: Tahzibu sunani Abidawud 1\469
Allah ne mafi sani

Jamilu Zarewa
23\10\2015

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

101
Kano
700252