12/12/2025
Gwana Hafsah Muhammad Sada kenan wadda zata wakilci Jihar Kano, yau a Musabaqar Kasa dake gudana a Jihar Borno Kuma itace gwarzuwar shekara a musabaqar da aka gudanar anan Jihar Kano
Muna addu'a Allah ya bata nasara ameen summa ameen.
Idan ba'a manta ba Malama Hafsah ta kammala haddarta a shekara ta 2021 a Mu'assasatu Sheikh Muhammad Rabiu, a karkashin tsarin "Tajul Waqar" na haddar Alƙur'ani mai Girma a cikin shekara daya kuma ta kammala karatun Ƙira'at a shekarar da ta gabata a Alfajr College of Education Kano.
Malama Hafsah Sada da ma sauran Gwanaye da wannan tsari ya samar misali dake nuna cewa nan gaba kaɗan wannan tsari zai mamaye ko ina cikin Nigeria.
Signed:
Hashim Idris Ahmad, Secretary General Tajul Waqar Programme.
.