12/09/2025
WASU SUNNONI NA ANNABI (SAW) DA AKA MANTA DA SU
Ya Yan uwana Ilimi da aiki da shi yana kara nisa ga wannan Al-ummar, yana da kyau mu yi waiwaye zuwa Sunnonin Ma'aiki Alaihis Salaam da aka manta da su!!!
1. Salatul Taubah: wannan Sallah ce Nafila Raka'a biyu da ake yi a lokacin da mutum ya sa6awa Allah ko kuma ya ke son ya Tubarwa Allah, da fatan a Kankare masa zunubinsa, wanda Annabi (SAW) babu wani Bawa da zai yi ta face an gafarta masa zunubinsa.
2. Goge fuska ko idanu ya yin da mutum ya tashi daga bacci: Annabi (SAW) ya kasance idan ya tashi daga bacci yana muttsike fuskarSa ko idanunSa domin kawar da alamar bacci.
3. Fara yin Alwala a lokacin da mutum zai yi wanka na musulunci, kamar janaba haila wankan Juma'a da sauransu.
4. Addu'ar sanya kaya, sababbi ko tsofaffi: Annabi (SAW) ya koyar da mu yin addu'a yayin sanya tsofaffin kaya ¹. Alhamdu Lillahil lazi kasani hazal thauba, wa razaqnihi min gairi haulin minni wala wuwwah. ². Sababbin kaya: Allahumma Lakal hamdu, Anta kasautanihi, As'aluka min khairihi, wa Khairi maa suni'a lahu, wa auzubu bika min sharrihi, wa Sharri maa suni'a lahu.
5. Yin Sallah da Takalmi: Annabi (SAW) ya Umarce mu da yin Sallah da Takalmi, inda ya ce mu sa6awa Yahudawa su ne ba sa yin Sallah da Takalmi ko kuma huffi.
6. Yin Sallama ga wanda ka sani da kuma wanda ba ka sani ba.
7. Yi wa kananan yara Sallama, wata rana Annabi (SAW) ya zo wucewa ta wajen wasu kananan yara sai ya yi musu Sallama.
8. Yin Asuwaki a lokacin Sallah, ko kuma Alwala, ko lokacin da aka tashi daga bacci, ko lokacin da mutum zai shiga gida, da kuma bayan gama cin Abinci.
9. Yin addu'a bayan gama kiran Sallah: Annabi (SAW) ya ce:" Ba a mayar da addu'ar da aka yi ta a lokacin kiran Sallah da kuma lokacin yin Ikama.
Ladubban kiran Sallah su ne kamar haka:
¹. Umarni ne idan Ladan yana kiran Sallah a maimaita abinda ya ke fada, sai idan ya ce" hayya alas sallah, sai ku ce Laa haula Wala Quwwata illa billah.
². Yin Sallati ga Fiyayyen Halitta Annabi (SAW) bayan an gama kiran Sallah.
³. Allahumma Rabba hazihud da'awatil tammati, sallatul Qa'ima, Aati Muhammadinil wasilati wal fadhilah, wab'ath'hu maqaman Mahmudanil lazi wa'adtahu.
⁴. Yin addu'a ta musamman da mutum ya ke da ita.
Ya Allah ka tabbatar da mu akan bin Sunnar Annabi Muhammad sallallahu alaihi wassallam.
Dan uwanku ne a Musulunci Muhammad Najib Aliyu Harazimi.